'RARIYA'TSOKACI: Sirrin ‘A Cuci Maza’ Daga Aliyu - TopicsExpress



          

'RARIYA'TSOKACI: Sirrin ‘A Cuci Maza’ Daga Aliyu Ahmed Duniya mai yayi! A kullum al’amuran mata wajen yin shigar da zai ja hankalin maza zuwa gare su ya kan canza sabon salo. Idan yau ka ga wani irin shigar, ba da jimawa ba kuma za ka sake ganin wani sabon yayin ya fito. Mata ko kuma na kira su da ‘yan mata, sun fito da salon abubuwa da dama, walau na abubuwan da suka shafi dinki, kwalliya a fuska, daurin dan kwali da sauransu. Wani sabon yayin da ‘’yan mata suka bullo da shi, shine sabon salon daurin dan kwalin nan da ake kira da ‘a cuci maza’. Shi dai wannan sabon daurin dan kwali a duk inda ka zaga a fadin kasar nan musamman yankunan Arewa, irin sa za ka ga ’yan mata suna daurawa. Inda a wasu yankunan ma idan mace ba ta yin irin wannan daurin dan kwalin, ana yi mata kallon wadda ba ta waye ba. Babban abin da ya fi jan hankali na ga yin wannan sharhi duk da cewa na jima ina ganin irin wannan daurin dan kwali a kan ‘yan mata shine, a safiyar Talatar makon da ya gabata ne ina daga cikin daki a kwance sai na ji wata ‘yar makwabtanmu tana cewa “mama yi min a cuci maza”. Ina daga cikin daki ban san lokacin da na fashe da dariya ba kasancewar yarinya ce karama, domin ba ta wuce shekara biyar ba. Duk da cewa na sha dariya a lokacin da na ji wannan yarinya tana wannnan furucin, ban yi kasa a gwuiwa ba, sai da na fito domin na ga yadda aka yi mata daurin. Fitowar da zan yi kawai sai na ci karo da yarinyar ta zo wucewa ta kofar gidanmu da wannan daurin dan kwali mai taken a cuci maza da mahaifiyarta ta yi mata. A nan ne na sake fashewa da dariya gannin cewa kofin silba na ga an maka mata a keya. Sai nake tambayar mahaifiyar na ce dama haka ake daurin a cuci maza? Sai ta ce min ai lokacin da abin ya bullo sabo kofin ‘yan mata ke makawa a kan su, daga bisani su dauki mayafi ko dan kwali su rufe. Bincike ya nuna cewa kananan kofin shan shayyi ‘yan mata suka fi amfani da shi wajen yin daurin, kafin daga bisani aka kirkiro da wani abu da masu sayar da kayan koli suka fito da shi domin taimaka musu wajen yin daurin. Amma sai dai idan ka ga kofin da wannan yarinya ta yi amfani da shi wajen yin irin daurin, dole ya baka dariya, saboda kamar yadda mahaifiyarta ta ce tana gama shan shayi ne kawai sai ta ji sha’awar a yi mata daurin. Bincike ya nuna cewa salon daurin dan kwalin ya samo asali ne daga wajen matan Fulani, kasancewar suna da doguwar suma, sai suke yi mata irin wannan tattara. Daga bisani kuma sauran ‘yan matan da ba su da wadatacciyar suma, suka bullo da hikimar yin amfani da kofi domin koyi da’yan matan Fulani masu yin irin wannnan daurin. Saboda yawan suma yana daga cikin suffar kyakkyawar mace. Masu magana dai na cewa ‘idan ba ki da gashin wance, kada ki yi kitson wance’. Saboda tsantsar karbuwar da wannnan daurin ya yi a gari, har fim aka yi masa mai taken “A Cuci Maza. Rabilu Musa Ibro shine ya fito a fim din. Sannan kuma har wakoki an yi mata masu yin irin wannan daurin. An kira daurin da ‘a cuci maza’ ne saboda wai samarin yanzu sun fi mayar da hankalin su wajen ‘’yan mata masu yin irin wannan daurin. Saboda su kan su ‘yan matan sun tabbatar da hakan. Kuma duk munin mace idan ta yi irin wannan daurin ta hau kan hanya, zai yi wuya baka samu wani na mijin ya tare ba. Haka ya sa a bikin sallar karama da ta gabata, kashi tamanin cikin dari na ‘yan mata irin wannan daurin suka yi. A yayin jin ta bakin wasu daga cikin ‘yan matan da suke yin irin wannan daurin dan kwali, sun bayyana ra’ayoyi daban-daban. Da farko na soma jin ta bakin wata budurwa wadda ta nemi a sakaye sunanta, inda ta bayyana min cewa a baya kafin ta fara yin irin wannan daurin idan ta fi kasuwa ko unguwa, zai yi wuya ka ga wani ya tare ta da sunan yana so, amma tun daga lokacin da ta soma yin daurin a cuci maza, samari da dama suka soma tare ta a hanya, walau za ta je unguwa ko kuma ta dawo daga kasuwa. “Ni dama ina so na ga ina ja wa samari aji, sai gashi kuma dama ta samu. A baya fa samari ba su cika kula ni ba duk da cewa ina da kyau daidai na rufin asiri, amma yanzu kuwa ba a magana, domin ina fama da su a yanzu”, inji budurwar. Sai dai a yayin da na tambaye ta abin da take amfani da shi wajen yin daurin a cuci mazan? Ta bayyana min cewa abin sirri ne domin ba ta so kowa ya san abin da take amfani da shi wajen yin daurin. Duk da cewa ta san ba da asalin sumar kan ta take wannan daurin ba. Ita kuma Hafsat kamar yadda ta bayyana min sunanta cewa ta yi “ai akasarin mazan yanzu sai da irin wadannan salo za ka ja hankalinsu, domin hankalin su ya fi karkata kan ‘yan matan da suke yin irin wannan daurin. Ni yanzu idan ba daurin a cuci maza na yi a kai na ba, ba na jin dadi, saboda na riga na saba. Ko saurayin da zan aura ma ya ba ni goyon bayan da na cigaba da yin daurin saboda yana burge shi, duk da cewa ya san ba suma ta ba ce”. Sai dai ra’ayin Zainab ya sha bamban da na sauran matan da na zanta da su game da lamarin, domin a cewa ta yi “ ni wannan daurin a cuci mazan kwata-kwata bai taba burge ni ba, saboda ba shi da wani alfanu. Ina amfanin ki yi kitson wance, alhali ba ki da gashin wance? Don haka ni iina kira ga mata masu yin irin wannan dauri da su daina, su tsaya a matsayin da Allah ya ajiye su. Haka kuma rashin sa ko yin sa bas hi zai sa ki samu saurayi ba”. Haka a bangaren samarin da na gana da su game da lamarin, ra’ayoyinsu ya sha bamban, inda wani mai suna Sulai¬man da soma zantawa da shi ya bayyana min cewa ba karamar yankar su ‘yan mata suke yi ba da irin wannan daurin. Domin a cewar sa yana son ya ga budurwa da irin wannna daurin dan kwali. A cewarsa shi ya cusa budurwarsa ra’ayin daurin a cuci maza domin da farko ba ta da ra’ayin yin daurin. Shi kuma Abubakar tonon silili ya yi wa ‘yan matan inda ya bayyana kamar haka “ai yanzu idan ka nemi kofunan gidanku ka rasa, to ka binciki ‘yan matan gidanku, ko kila sun dauka sun yi daurin a cuci maza da shi. Saboda ban a mancewa akwai labarin da ya zo kunne na cewa wata budurwa tana cikin tafiya ta sha kwalliya tana takun kasaita da daurin a cuci maza, kwatsam sai dan kwalin da ta yi daurin da shi ya fita, kawai sai ga kofi irin na masu sayar da shayi ya fado”. Abubakar ya kara da cewa don haka a yanzu babu wata burga da ‘yan mata za su yi masa da daurin a cuci maza, saboda an yi walkiya ya ga sirrin daurin. Sai dai kuma a cewar wata mata daurin yana tattare da illoli, inda ta kawo misali da yadda wata budurwa da ta yi irin daurin ta fado daga kan babur, ta buga kanta da gurin da ta yi daurin da kasa, wanda hakan ya yi sanadiyar samun mummunan raunii da ta yi da kofin da ta yi amfani da shi wajen yin daurin. Sannan kuma duk macen da ka ta yi irin wannan daurin dan kwalin, za ka ga hankalinta ya rabu gida biyu don gudun kada abin da ta yi daurin da shi ya fado asirin ta ya tonu. Da yawa daga cikin maza dai sun bayyana cewa tuni aka yi walkiya suka ga abin da duhu ya rufe, domin sun gano cewa akasarin ‘yan mata kofi suke amfani da shi wajen yin wannan sabon salon daurin dankwali da ya zama ruwan dare gama gari ga ‘yan mata. Wasu ma cewa suka yi, ban da kofi, har karamar robar cin abinci ‘yan matan na amfani da shi wajen yin daurin. Saidai kuma wani bangare na samarin sun yaba da irin salon daurin dan kwalin domin yana matukar burge su. Saboda su a nasu ra’ayin sun fi son mace mai son kawata kanta da ado. To mata adon gari, ni dai ban yi wannan makala don na tona muku asiri ba, sai dai na yi ne don yadda na ga wannan yarinyar da ta yi silar yin wannan rubutun ta fito da irin na ta sabon salon daurin dan kwalin a cuci maza, saboda ba da irin wannan kofin ‘yan matan ke yi ba.
Posted on: Mon, 23 Sep 2013 08:12:39 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015