BACIN TAFARKIN ‘YAN SHI’A DA AKIDOJINSU! Wallafar: Shaikh - TopicsExpress



          

BACIN TAFARKIN ‘YAN SHI’A DA AKIDOJINSU! Wallafar: Shaikh Dr Umar Muhammad Labdo *** Darasi Na (22) *** ================================== Babi Na Uku MATSAYIN SHI’A A CIKIN AL’UMMA (1) Ko ba’a fadi ba, wanda duk ya dubi akidojin Shi’a kamar yadda muka yi bayanin su a babin da ya gabata, zai iya sanin matsayin ‘yan Shi’a a idanun sauran al’umma. Ahlus Sunnah Wal Jama’a, wadanda – Alhmadulillah – su ne agalabiyar Musulmin duniya, suna duban kungiyar Rafilawa a matsayin ‘yan bidi’a, batattu wadanda suka kudure miyagun akidoji da suka sabawa Alkur’ani da Sunnah da hankali lafiyayye. Haka kuma suna ganin cewa, alal akalli, wasu daga cikinsu sun fice daga Musulunci dungurum. A daya bangaren kuma, su ma ‘yan Shi’a, saboda akidojin nan da suka kudure, dole ne ya zama suna da wani matsayi wanda suka tsaya a kansa dangane da alakarsu da sauran al’umma da wata mahanga wacce da ita ne suke hangen sauran Musulmi. Wadan nan abubuwa guda biyu, watau matsayin Rafilawa a wajen al’umma da akasi, su ne abinda za mu duba a cikin wannan babi. SHI’A DA AHLUL BAITI Da yake Rafilawa suna da’awar son Ahlul Baiti, watau iyalin gidan Manzon Allah (SAW), da jibintar su wanda a kan haka suka gina shika-shikan tafarkinsu, to bari mu fara da duba dangantaka tsakaninsu da wannan babban gida da kuma zababbun mutane da Allah ya yiwa baiwa da zama ‘yan wannan gida. ‘Yan Shi’a suna da’awar son iyalin gidan Annabi (SAW) da zuri’arsu, amma sun kasa su kashi uku. • Na farko Ali wanda yake kani ne ga Annabi (SAW) watau dan baffansa ne, mahaifinsa da mahaifin Annabi Ubansu daya, da Fatima wacce ita ce karama a cikin diyan Annabi mata guda: Zainab, Rukkaya, Ummu Kulthum da kuma ita Fadima din. Wannan kashi, Ali da Fatima da ‘ya’yansu, in banda guda Ummu Khulthum (watau ta biyu), da jikokinsu da zuri’arsu su ne ‘yan gaban goshin Rafilawa wadanda suke kauna, suke jibinta suna matukar girmamawa har ya zuwa haddin bauta. • Kashi na biyu su ne matan Manzon Allah (SAW) uwayen muminai, musamman wadanda suka fi shahara a cikinsu kamar Aisha diyar Abubakar da Hafsa diyar Umar, Allah Ya yarda da su baki daya. Wadannan ‘yan Shi’a na kin su matukar ki, suna la’antar su, suna kudure kafircinsu kuma suna da yakini, a ganinsu, cewa su ‘yan wuta ne, masu dauwama a cikin ta. • Kashi na uku su ne sauran diyan Annabi mata wadanda muka ambata a sama, Zainab, Rukayya da Ummu Kulthum da zuri’o’insu. Wadannan koda yake suma ‘ya’yan Annabi (SAW) ne na tsatsonsa, amma ‘yan Shi’a suna yin burus da su, ba sa ko ambaton su, babu Imamai a cikin zuri’arsu kuma ba su da wata daraja ko matsayi na musamman. Kuma a cikin wannan kashi suka sanya diyar Ali da Fatima wacce muka toge a sama, watau Ummul Khulthum (ta biyu). Koda yake Ummu Kulthum Ali da Fatima ne suka haife ta, kuma Hussaini binu Ali ne ya saki nono ya ba ta, amma Rafilawa ba su sa ta a jerin zuri’ar Annabi (SAW) masu daraja ba. Laifinta shi ne wata kaddara da ta fada mata ta auri Sarki Musulmi Umar binul Khaddabi (RA) kuma ta haife masa diya biyu don haka ‘yan Shi’a suka kore ta daga jerin zuri’ar Ali da Fatima. Daga nan mai karatu zai fahimci cewa da’awar Shi’a ta son Ahlul Baiti da jibintar su da’awar karya ce wacce aka gina ta a kan jahilci da munafunci da son zuciya. Idan da ace wannan da’awar gaskiya ce, ta ya ya za su bambance tsakanin Aisha matar Annabi da Fadima diyarsa? Ko ta ya za su bambance tsakanin diyan Annabi mata wadanda dukkananinsu uwarsu daya ubansu daya? Kuma ta ya za su bambance tsakanin Hassan da Hussain da kuma kanuwarsu Ummu Kulthum wadanda uwa daya, uba daya suka haife su? Abinda muka ambata a nan na soyayya da jibintar da ‘yan Shi’a suke da’awa ga Ahlul Baiti, mun kawo shi a dunkule ne amma bayaninsa filla-filla ya gabata. Dangane da kashi na farko, Ali da Fadima da zuri’arsu, mun ga matsayin da Rafilawa suka ba su a inda muka yi magana a kan akidar Imama. Mun ga yadda suka girmama su, suka kambama su, suka ajiye su a wani matsayi, wanda yake sama da matsayin Annabawa da Manzanni, sa’annan daga bisani suka ba su sifofin allantaka. Dangane da kashi na biyu kuwa, watau matan Annabi (SAW) uwayen muminai, musamman Aisha da Hafsa, mun gabatar da bayani, a cikin babin akidar Shi’a da Sahabbai, yadda Rafilawa suke la’antar su tare da mahaifinsu, Abubakar da Umar, a cikin addu’arsu da suke cewa “Du’a’u Sanamai Kuraish”, watau Addu’ar Gumakan Kuraishawa Biyu. Sai dai muna son mu kara wani abu a nan wanda yake nuna cewa har Manzon Allah (SAW) bai tsira ba daga ta’annuti da jafa’in Rafilawa. Wannan shi ne abinda suka ruwaito cewa: “A LAHIRA ZA’A KONA AL’AURAR ANNABI (SAW), WATAU ZAKARINSA, SABODA AUREN AISHA DA YA YI.” Ibn Taimiya ne ya hakaito wannan danyar magana tasu a cikin Fatawa nasa. Kuma tabbacin wannan ya zo a littafin Kashful Asrari wa Tabri’atil Al’immatil Adhari na Sayyid Hussain Almusawi, wanda a da dan Shi’a ne kuma ya tuba. Ya rubuta cewa, daya daga manyan Malaman hauza (hauza a wurin ‘yan Shi’a kamar zawiya ne a wurin ‘yan Darika) mai suna Sayyid Ali Garawi ya ce, “LALLAI ANNABI (SAW) BABU MAKAWA SAI AL’URARSA TA SHIGA WUTA SABODA YA AURI WASU MATA MUSHIRIKAI.” Yana nufin A’isha da Hafsa. (Duba Kashful Asrari na Musawi, 21-22). Wannan magana wacce ‘yan Shi’a na wannan zamanin suke yin ta, kamar yadda Musawi ya hakaito, ba wani Musulmi da zai shakkun kafircin wanda yake yin ta. Ubangiji muna neman tsarinka daga kafirci da munafunci da bata. Su kuwa kashi na uku, watau sauran diyan Annabi mata, Zainab da Rukayya da Ummu Kulthum, ‘yan Shi’a suna yin burus da su, kamar yadda muka bayyana a sama, ba sa ko ambaton su. Amma da yake mun sanya Ummu Kulthum, diyar Fatima kuma kanuwar Hassan da Hussaini, a cikin wannan kashi, bari mu tunawa mai karatu da abinda Ni’imatullahi Aljaza’iri, wani babban Malamin Shi’a, yake fadi, “ABIN DAURE KAI SHI NE YADDA ALI (A.S) YA AURAWA UMAR BINUL KHADDABI DIYARSA UMMU KULTHUM TARE DA CEWA MIYAGUN AYYUKA SUN BAYYANA DAGA GARE SHI (SHI UMAR) KUMA YA YI RIDDA DAGA MUSULUNCI FIYE DA RIDDAR KO WANE MAI RIDDA.” (Al’anwarul Nu’umaniya 1/18). Watau auren Umar shi ne laifin Ummu Kulthum kuma shi ya sa ta rasa daraja koda yake ita ma diyar Ali da Fadima ce, kamar Hassan da Hussain. Insha Allah za mu ji ‘AHLUL BAITI DA SHI’A’, duk a cikin Babin MATSAYIN SHI’A A CIKIN AL’UMMA! Admin: Ummu Abdillah Zaria.
Posted on: Thu, 28 Nov 2013 20:25:04 +0000

Trending Topics




© 2015