{{{{{{{{CIGABAN TARIHIN SHARIF SHEIKH AHMAD ALI ABUL FATHI - TopicsExpress



          

{{{{{{{{CIGABAN TARIHIN SHARIF SHEIKH AHMAD ALI ABUL FATHI YERWA}}}}}} }}Al hamdulillahi kamar yadda muka tsaya a bayanin wasu daga littattafansa mun sami bayanin cewar sheikh Abubakar atiku sanka yana cikin malamansa hasalima shi ya hadashi da sahibul faidha. Cikin nasarorin da shehi yasamu sun hada da gina zawiyyarsa a maiduguri a shekarar 1949 don yada addinin Allah sai sabuwar madinatul maiduguri a shekarar 1990 Shehi yagina makarantar tahfizul kur an sannan ayanzu haka akwai makarantar primary da secondary duk na shehi a karkashin gidauniyar sheikh Abulfathi wadda bata gwamnati bace wannan gidauniya ta shehi a yanzu tanada wajen sayarda litattafan addini da madaba a .MOULANA Sharif Qutbi Ahmad Ali Abul fathi ya koma rahama a shekarar 2003 yabar iyali da dama maza da mata . Babban khalifansa shine sheikh Ali Abul fathi sai wasu daga yayansa irinsu sheikh Arabi Abul fathi limamin masallacin madinatul maiduguri kuma shugaban fityanul islam ta kasa akwai su sheikh Murtala Abul fathi dasu sheikh sukairaj Abul fathi da sauransu da dama sannan wannan bawan Allah nada dubban almajirai da dama a kasashe dabam dabam irinsu nigeria niger chad sudan cameroon central africa da sauransu wasu daga cikin Aminansa sune sheikh sharif Ibrahim saleh maiduguri sheikh Abubakar Almiskin sheikh Abdurrazak kusa sheikh Abubakar cota sheikh sharif tijjani alhasaniy da sheikh salisu bappa (katibinsa) da sauransu Allah ya jaddada masa rahama da yarda ...lallai yan uwana matasa akwai jan aiki a gabanmu domin yadda duniya bata auren raggo haka itama lahira bata auren raggo da nagaba ake gane zurfin ruwa daga almajirinku murtala ibrahim imam katsina
Posted on: Sat, 10 Aug 2013 18:01:18 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015