Gaskiya Wasu Mazan Basusan Darajar Ya Mace Ba! Ni kam naga ta - TopicsExpress



          

Gaskiya Wasu Mazan Basusan Darajar Ya Mace Ba! Ni kam naga ta kaina. Da farko sunana Amina, kuma ni macece da ta taba yin aure a baya, amma kafin lokacin Aure na yayi na fuskanci kalubale. Allah ya samin son wani matashi me hakuri da sanin yakamata me suna (Abba), gaskiya Abba yana matukar sona, Abba ya kasance farin-cikin raina. Domin tun ina JSS 2 muka fara soyayya, wanda har na kammala karat... una na Sakandire muna tare kuma ban taba fuskantar bacin rai a tattare dashi ba. A kwana a tashi, Abba ya bude min Facebook, har takai na sami abokai da dama a Facebook, kuma hakan yazo ne bisa yawaita surutu da nakeyi da kuma hababa da nakeyi. Hakan yasa na hadu da wani matashi me yawaita aiko min sako (Message) a Facebook dina, ga kuma yawaita comment a duk Posting da nakeyi, wanda har takai hakan ya jawo bacin ran farin-cikin raina wato Abba. Domin shi Abba, baya so yaga ina yawaita hulda da mutane, ga kuma wancan bawan Allah me yawaita aiko min da sakonni har na bashi lambar wayata, domin gaskiya naga yana matukar daukata da muhimmanci. Shi dai wancan bawan Allah har kirana yakeyi akai-akai, ta kai har ya tambayeni gidan mu, ni kuma na fada masa. Daga karshe dai ya kawo min ziyara ta musamman. Bayan wasu kwanaki, kwatsam sai naga iyayensa sunzo tambayar Aure gidan mu, ganin mahaifina yasan mahaifinsa, sai ya bashi ni ba tareda sanina ba. Agaskiya ni bana sonsa dai-dai da minti daya, amma da yake mahaifina ya riga ya gama komai, sai na baiwa zuciyata kuma hakuri na Aure shi. Bayan wasu watanni da Auren wancan bawan Allah, sai na gane cewa shi mane min mata ne ga kuma shaye-shayen muggan kwayoyi, ga kuma baya kula da mahaifansa ko kadan. Saura yan kwanaki kafin zuwan Azumi, na yanke shawarar yiwa wannan mahaifiya tasa cefanen Azumi, kuma na cika alkwarin da na daukawa kaina na yin wannan cefane. Bayan zuwansa gida sai nace dashi ga wannan ka kaiwa Umma, sai naga bayaso amma na tilasta shi har yakai mata. Bayan dawowarsa da daddare, sai nayi masa sannu da zuwa amma naga babu farin- ciki tare dashi, na tambaye shi lafiya, sai yace dani gashi kinsa naje duk na kashe musu kudina, nace dashi kayi hakuri wataran sai labari. Kashe gari kawai sai naga yace dani ya SAKENI ga kuma takarda ta, yanzu dai na koma gidan mu, kuma Allah ya albarkaci auren mu, domin Allah ya bamu Ya har ta girma tayi wayo. Yanzu ni kuma gashi samari har guda hudu (4) sunzo neman Aurena, har wancan suarayi nawa wato Abba da kuma wani me suna Ahmad amma shi Ahmad yana da mata daya (1) haka zalika akwai wani dan uwanmu shima me mata daya yazo neman aure na kai bari na fada muku akwai me mata uku (3) shima yazo neman aurena. Gashi ni kuma Allah ya samin Son dukkan su a raina. To shi yasa na yanke shawarar ziyartar wanna shafi me farin-jini (Dandalin Mallam B. Kabir Chiroma) domin naji ta bakin ku game da wanda yakamata na Aura. Nagode! Admìn sulaiman Haruna
Posted on: Tue, 15 Oct 2013 08:14:55 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015