IDAN KUN KARANTA KO SHAKKA BABU SAI KUNYI FARIN CIKI. . .inSHA - TopicsExpress



          

IDAN KUN KARANTA KO SHAKKA BABU SAI KUNYI FARIN CIKI. . .inSHA ALLAHU .Via#Mahmoud_nagudu . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . Yau daya ga watan sabuwar shekarar Muslunci (1/1/1435). Ya-Allah muna tawassali da kyawawan sunayenka, da ka sanya wannan sabuwar shekara ta zama hanyar arziki ga duk wanda ya yarda kai kadai ne baka da abokin tarayya. Ya-Allah, ka sa wannan sabuwar shekara ta zama waraka ga duk wani me dauke da cuta komai girmanta da karfinta. Ya-Allah ka kawo mana karshen duk wani tashin hankali da alummar musulmai suke ciki a arewacin Najeriya dama duniya baki daya, bisa wannan sabuwar shekara da muka shiga. Ya-Allah ka yaye mana duk wani bakin-ciki dake damun mu, ka maye mana shi da farin-ciki a wannan sabuwar shekara da muka shiga. Duk wata wanda takai munzalin aure, Ya-Allah ka aurar da ita ga miji nagari, me tausayinta kuma kaunarta. Samarin mu marasa aure, Ya-Allah ka basu damar yi, kuma ka hada su da mata nagari. Matasan mu marasa aikin-yi, Ya-Allah kasa wannan sabuwar shekara ta zama karshen zaman banza da sukeyi. Ya-Allah ka bamu shugabannin nagari masu kishin talakawa, ba wai masu kishin aljihinsu ba. Ya-Allah ka bamu yaya nagari, kangararrun cikin su Allah ka shiryar mana dasu. Ya-Allah kai kace mu roke ka zaka amsa mana, mun roke ka kuma ka amsa mana, dan haka muke kara rokon ka da ka amsa mana, domin kai kadai zamu roka ka amsa, domin kai kadai ne (Mabuwayi Gagara Misali). Ya-Allah duk wanda ya karanta wannan duai kuma ya amsa da AMEEN, ka biya mishi duk wata bukata tashi ta alkhairi a dai-dai lokacin da yake da bukatar hakan. Wanda kuma bai samu damar amsawa da AMEEN ba, Ya-Allah shima ka biya masa bukatunsa na alkahiri. Ni kam nace AMEEN SUMMA AMEEN.
Posted on: Tue, 05 Nov 2013 10:14:09 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015