MU KEWAYA JIHOHI: SOKOTO: Gwamnati Ta Kashe Milyan 610 Kan - TopicsExpress



          

MU KEWAYA JIHOHI: SOKOTO: Gwamnati Ta Kashe Milyan 610 Kan Masauki Na Musamman Gwamnatin jihar Sokoto ta kashe kudi har Naira milyan 610 wajen mallaka tare da yin kwaskwarima ga masaukin baki na musanmman wanda tsohon shugaban Kasa, Janar Ibrahim Babangida ya kaddamar a garin Sokoto. Gwamnan jihar, Aliyu Wammako ya ce, an samar da masaukin na zamani ne don sauke manyan baki da ke ziyarar jihar akai akai inda ya kara da cewa, an tanadi kayayyaki alatu a cikin katafaren gini kuma za a ci gaba da kulawa da masaukin don ganin bai lalace ba. A nasa bangaren, tsohon shugaban kasar ya nuna farin cikinsa game da samar da wannan masaukin inda ya yaba wa gwamnan jihar bisa wannan namijin kokarin da ya yi. Haka ma, tsohon shugaban ya kaddamar da wasu hanyoyi da aka gina a cikin jihar.
Posted on: Sat, 21 Sep 2013 21:05:58 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015