TAMBAYA TA 758 ***************** tambayata malam itace - TopicsExpress



          

TAMBAYA TA 758 ***************** tambayata malam itace muna damahaifinmu kuma yanadamata uku mahaifiyarmuce uwargida to kwanakin baya watanni uku zuwa hudu dasuka wuce ta sami matsala wajan haihuwa anyi mata operation to tun bayan ta warke har yanzu ba ya shiga dakinta kuma duk aiyukan wahalar da baaso mace tayi ita tanayi kama daga girki zuwa sauran abubuwa sannan kuma tunda ya auri matarsa ta ukun ya dauketa ya kaita wata unguwar suke zaune bedamu da inda muke ba danhar abincima sai yaga dama yake kawowa, ya barmu da dawainiyar gidan to malam tambayata ita ce: Shin idan munyi wani yunkuri dan nemar wa babarmu yanci shin yin hakan ya haramta? da fatan malam zakayimin kyakkyawan bayani tareda kyakkyawar shawara. wassalam (Daga wani Bawan Allah) AMSA ****** W/salam. Gaskiya irin wadannan matsalolin ana samunsu acikin yawancin Manyan gidaje. Hakika duk mutumin da ba ya adalci atsakanin matansa, yana daga cikin mutanen da zasu tashi acikin mummunan yanayi aranar Alqiyamah. Kuma Manzon Allah (saww) har ya bar duniya bai gushe ba yana yiwa alummarsa wasiyya akan cewa: kuji tsoron Allah kuyi hakuri da mata, ku kyautata musu. Don haka indai wannan abinda kayi bayani haka yake, to tabbas mahaifinka yana cikin babban kuskure. Hanyoyin da zaka bi domin magance wannan matsalar sune kamar haka: 1. Kaci gaba da girmama mahaifinka. Domin kuwa har abada yananan amatsayin mahaifinka. Babu makawa kaci gaba da kulawa da hakkinsa wanda yake kanka. Kada wannan abinda yakeyi ya hanaka girmamashi da kyautata masa. 2. Kaci gaba da kyautatawa Mahaifiyarka. Kana bata hakuri tare da kwantar mata da hankalinta. Da nasihohi. 3. Kuje ku samu wani daga cikin abokan Mahaifin naku ko yan uwansa. Ku gaya musu matsalar da take faruwa. Insha Allahu nasan zasu shigo cikin maganar domin suyi masa nasiha. 4. Kada ku kalubalanceshi gaba-da- gaba. Amatsayinku na yayansa. Domin kuwa hakkin Allah ne kawai yafi hakkin mahaifi nauyi akan mutum. Duk da cewar kuma hakkin mahaifiya yafi girma fiye da na mahaifi. 5. Ka yawaita addua da neman daidaituwar wannan lamarin daga Allah. Allah ya sawwake. Wallahu aalam.
Posted on: Fri, 22 Nov 2013 23:33:05 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015