Ya kai Dan uwa musulmi!! ************************* Abin zai baka - TopicsExpress



          

Ya kai Dan uwa musulmi!! ************************* Abin zai baka mamaki idan ka leka cikin pages na wani Pastor ko Bishop, ko father.. Zaka iya gani LIKES kamar sama da guda dubu dari biyar (more than 500,000 LIKES). Sannan idan kaga yadda Jamaar Kiristoci suke girmama Bishop dinsu da Pastor dinsu abin zai baka mamaki. Yanzu duk wanda yake zaune a Birni yasan cewar agari daya ma kadai zaka iya samun sama da Chochi 20 kala kala. Ko wadanne kungiyarsu daban. Amma ba zaka taba jin wani yana zagi ko kushewa wani ba. Ba zaka taba jin wani ya fito yana zagin PAPA ROMA ko kuma wani Shugaba acikinsu ba.. Idan ka ziyarci pages dinsu ba zaka ga wani abu na rashin mutunci atsakaninsu ba.. (Sai dai gurbataccen abinsu shi suke yi). To amma me yasa mu musulmi wadanda karantarwar addininmu yafi nasu, sannan muna kan manhaji mai haske wanda babu duhu acikinsa ba zamu fisu tafiya akan halaye managarta ba!! Ba wai inaso in fifitasu bane, amma shi hadin kai da mutunta juna abin so ne. Kuma abin koyi ne.. Ya Allah ka Qara mana hadin kai da girmama juna da mutunta juna. Ameeen.
Posted on: Sat, 19 Oct 2013 08:26:07 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015