2015: ALIYU MAGATAKARDA WAMAKKO DA GWAMNONI 4 NA Kyakkyawan - TopicsExpress



          

2015: ALIYU MAGATAKARDA WAMAKKO DA GWAMNONI 4 NA Kyakkyawan Yunkuri... Da Yake Arewa Na Sake Hadewa Wuri Guda  A wani yunkuri na dinke rarrabuwan kawuna a Arewa da kuma watakila ceto Nijeriya, gwamnoni biyar na jam’iyyar PDP mai mulki suna ci gaba da kai kokarin samun galabar siyasarsu. A jiya ne LEADERSHIP ta bada cikakken rahoton cewa gwamnonin guda biyar da suka hada da Babangida Aliyu (Neja), Rabi’u Kwankwaso (Kano), Aliyu Wamakko (sokoto), Sule Lamido(Jigawa) da kuma Murtala Nyako (Adamawa) za su ziyarci tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida a Minna a jiyan. Wata majiya kwakkwara a jiyan ta shaida cewa “bayan sun ziyarci Janar Babangida, har ila yau gwamnonin sun yi shirin ziyartar tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubukar da kuma tsohon ministan tsaro, Janae TY Danjuma”. Majiyar ta ci gaba da cewa “Gwamnonin sun yi amannar cewa wadannan mutanen su ne ginshikai. A daidai lokacin da wasu suka dukufa wajen ganin ba kawai sun raba kan Arewa ba har ma da kasar nan baki daya ta hanyar kabilanci da addini, su kuwa gwamnonin sun yanke shawarar tunkarar wadannan dattawan ne domin ceto Nijeriya.” Sannan ta kara da cewa dambarwar da ake yi a Jihar Revers da goyon bayan da fadar shugaban kasa ta nuna ga wanda yasha kaye a zaben Majalisar Gwamnoni ta Kasa, alamomi ne na irin guguwar da za ta turnike kasar nan. Haka zalika majiyar ta bayyana cewa “yunkurin ya fi karfin a ce ana yi ne saboda zaben 2015, a’a al’amari ne da ya shafi makomar Nijeriya. Gwamnonin sun fusata da yadda mutanen da aka basu amanar hade kan kasa a yanzu sun zama ummul’aba’isin raba kanta. Yunkurin ya zarta batun jam’iyya kawai. Kuma ku zuba ido ku gani” in ji majiyar
Posted on: Mon, 22 Jul 2013 18:58:01 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015