99 MISSED CALL PART 4 like Kundun - TopicsExpress



          

99 MISSED CALL PART 4 like Kundun soyayyah ♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥ Koda naga yarinyar dataimin jagora zuwa cikin gidan ta fito tana turo GIMBIYA FATEEMA a keken guragu bansan lokacin dana mike na doshi gurinsuba zuwana keda wuya nayi mata sallama ta amsamin da wata murya mai dadin sauraro daga bisani na nace da yarinyar dake tare da ita bara na turota bayanda muka zo tsakiyar falon sai nasamu guri na zauna akan katifun kujerun cikin falon yayin data kalleni tace karkasamu damuwa ni basai na sauka daga kan keken ba nasake kallonto sosai farace matsakaiciya wato ita ba doguwaba kuma ba gajeriyaba..... Gashin kanta har gadon baya hancinta madaidata hmmm bara na tsaya haka dayake fuskarta sanye take da wani bakin glass bana ganin idanuwanta.... Na janyo yarinyar dataimin jagora kusa dani daga bisani na kalleta nace mene sunanki kanwata yarinyar bazata haura shekara bakwaiba tace sunana SAUDAT na danyi murmushi nace amma gaskiya sunan akwai dadi sai kace alewar nan wato pop of loli..... GIMBIYA TAFEEMA dake zaune akan keken guragunta tace to nawa zakasai sunan nadanyi murmushi na kalli karamar yarinyara nace SAUDAT nawa zaki sayarmin da sunan naki tace N50 nasa hannu na dakko sabuwar N50 a aljuhuna na mika mata taki karba sannan daga bisani tasa daria tace wasa nake gaba daya muka barke da daria sannu a hankali kallona ya koma zuwa ga GIMBIYA FATEEMA wacce ke zaune akan keken guragunta yayinda karamar yarinyar nan wato SAUDAT ita kuma ta mike tabarmu nida GIMBIYA a zaune cikin falon..... Sannu ahankali naga ta cire glass din dake idanunta hakika sai a lokacin na tabbatar kyakykyawace sannan daga bisani ta fara cewa Shahararran marubucin littafin AHMAD KO SADAUKI tare da........ hmm AHMAD A .... mai abin mamaki taci gaba da cewa tabbas nasan zakayi mamaki bisa yadda kazo kaganni gurguwa kuma duk shirar da mukayi dakai ta waya kafin yanzu mu hadu ban bayyana maka ni gurguwa bace dole abin ya daure maka kai amma da sannu zakaji sirrina.... Na katseta da cewa ai larurace bata wuce kan kuwaba shugabannin kasama yinta suke balle ke yar masu hannu da shuni .... tadanyi murmushi hmm Ta katseni da cewa yanzu kana nufin zaka iya aurata a hakan nace kwarai kuwa duk abinda Allah ya kaddarawa bawa ba doleba...... Da sauri mukaga karamar yarinyar nan wato SAUDAT ta shigo cikin falon da muke ciki ko ince da gudu tazo gaban gimbiya FATEEMA tace Aunty ga daddy can ya dawo daga GERMANY din . Yanzu-yanzu........ Hakan shine yayi sanadiyyar katse mana hirar da muke nida ita kafin kace kwabo zumbur Gimbiya FATEEMA ta mike daga kan keken guragun ta doshi waje cikin sauri domin taro mahaifinta daga kasar Germany.... Hahaha lallai tarkona ya kama kurciya ashe dama ba gurguwabace tayi hakane dan ta gwadani amma dan jin yadda zata kasance mu hadu a kashi na 5 NAKU AKO YAUSHE AHMAD A BABA 07055663578
Posted on: Sat, 02 Nov 2013 20:32:20 +0000

Trending Topics




© 2015