ABINDA NA GANI: Na jima da jin cewar ana koyar da yaranmu adduoin - TopicsExpress



          

ABINDA NA GANI: Na jima da jin cewar ana koyar da yaranmu adduoin kirista a makarantunsu musamman na kudi da kabilu ke koyarwa. Ina yiwa wasu yara karatu sai daya daga cikin yaran ya shigo ya zauna, zamansa ke da wuya a lokacin da kaina yake duke ina duba takarda, sai naga ya sa hannunsa ya tsokali goshinsa da gefen kirjinsa na dama da na hagu! Kamar dai yadda muke ganin kiristoci yan Ball ko a Fim suna irin wannan adduar. Abin ya daure min kai ainun, na tambayi yaron kai Muhammad me ka yi? ya ce ba komai, na ce masa abinda kayi na duddungura hannu a goshinka. Sai yace da ni, a Makaranta aka ce musu su dinga yin adduah haka, ammafa sai da na matsa shi sosai sannan ya fada, na lura cewa an sanyasu yin adduar ne a boye. Wannan alamarin ya tayar min da hankali matuka, dan abinda nake jin labari ne na ganshi da idona. Lallai ne iyaye su sanya ido sosai akan yaransu.
Posted on: Wed, 06 Nov 2013 20:32:52 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015