ABINDA YAFARU DANI DA #DADDARE 44 Muryar ta da naji kamar a dodon - TopicsExpress



          

ABINDA YAFARU DANI DA #DADDARE 44 Muryar ta da naji kamar a dodon kunne na daabin da ta furta min shine yayi matukar jefani cikin wani matsanancin farin ciki mai girma... Harta kai da farin cikin yafito fili karara,,,, kallo na kawai yayana yayi,, sannan ya saki wani tattausan murmushin,,, yayi zaton dawowar da yayi ce ta jefani cikin wannan farin ciki mara misaltuwa... baisan abin ba haka bane,,, ni abin da ya jefani cikin wannan yanayi daban ne,,,, haka na kwana cikin farin ciki da zumudin gari ya waye ,,, washe garin ranar haka na Wuni ina ta Allah Allah dare yayi domin Ta kara ziyarta ta mucigaba daga inda muka tsaya..... Da misalin Karfe 4:00 na yamma na raka yayana Soja tasha ya shiga motar koma wa fagen daga,,, ban dawo ba har saida naga motar su ta tashi... Cike da farin ciki na fito daga cikin tashar motar a dai dai wannan lokaci da agogon hannuna ya buga karfe 6:00.. Bayan na koma gida na yi Sallar magariba da ishai na fita zuwa wani shago dake bakin titin unguwar mu wato (Chicken Republic) ina zuwa ban tsaya wani bata lokaci ba wajen siyan kayan ciye ciye da shaye shaye.. Sai da na cika ledodi biyu da wadan nan kayan sannan na koma gida... Da misalin karfe 9:13 na fara jin kararrawar wayata ta doka koda na dauka na duba sai naga Sakon ta Kamar Haka,,, idan Allah ya kaimu anjima da Daddare ina kan hanya Sai ka shirya karbar abin da zan zo maka dashi,,,,, ina gama wannan karatu wani irin murmushin farin ciki ya subuce min,,, har takai na na rasa inda zan sa kaina saboda tsananin farin ciki,,, tundaga wannan lokacin na fara shirye shiryen zuwanta... Can da misalin karfe 11:30 ina zaune ina duban bakin kofar dakina... Na fara jin sautin takun takalmi ya nufu dakina... Da sauri na nufi kofar dakin ba tare da najira mai wannan tafiyar ya karasa isowa ba... Ina isa na sanya hanu na bude hade da wani irin tattausan murmushi... Abin da idanuna suka gane min ne ya sanya ni bata rai... Nan take fuskata ta murtuke wani irin gumin bakin cikiya ketomin, Dariya kawai naga ya fara yimin... Ba wani bane wannan illah Yayana da Na raka Tasha ya kara dawowa... Cikin bakin ciki na fara tambayarshi da cewar yana ganka kuma ka dawo ince dai lafiya ?? Umm lafiya ba Lafiya ba kaidai mu shiga daga ciki in dan huta tukunna,,,, daga nan bai kara yimin wata magana ba ya kunna kai cikin dakin... Yana shiga yaga wannan kayan abinci iri iri da na baje domin tarbar bakuwata Aisha,, yace kai ashe haka kake cin dadi ai kuwa bai tsaya wata wata ba ya zauna ya fara daukar girki... Nikuwa saboda tsabar bakin ciki kasa cewa komai nayi,,, na nufi makwancina na kwanta wahaye ya cika idanuna... Tambayata naji ya farayi yana cewa kai bazaka ci Abincin bane,,, saboda tsananin haushi cewa nayi dashi yaci ni nakushi,,, wannan daren kuwa har zuwa wayewar gari ban rintsaba,,, haka na tashi washe gari da zazzabi aranar ko kofar gida ban leka ba.... Sai da ya shefa kwana 8 agida batare da ya komaba a wannan kwanaki 8 dayayi agidah jinayi kamar ya dauki Shekaru 40 ne... A rana ta tarane ya koma wajen aikin nashi,,,, ina zaune har bacci ya fara daukata naji karar kunna tv ... Bude idanun da zanyi muka yi ido hudu da ita tana mai yimin wani tattausan murmushi tana cewa,,,,, na baka Tsoro koh??? Girgiza mata kai kawai nayi alamun a,a daga nan na mayar da dubana izu hannunta na hagu.... Abun da iduna ya gane min ne ya jefani cikin tsoro da fargaba na tabbatar da yaukam ba makawa abinda nake tsoro zai afku,,,,, nan take naga ta canza fuska daga yanayin yanda take ta fara da cewaaaa,,, ga duk wanda ta/ya karanta da ya tabbata yayi LIkE dan kada cigaban wannan labari anjima ya wuce ku ana haka jirgi na masoya
Posted on: Thu, 08 Aug 2013 20:46:20 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015