ABUBUWA HUDU SUNA JAWO ARZIKI IBN QAYYIMUL - TopicsExpress



          

ABUBUWA HUDU SUNA JAWO ARZIKI IBN QAYYIMUL JAUZIYYAH. (Rahimahullahu)yana cewa: *Abubuwa hud‘u suna jawo arziki: 1) Yawan Tsayuwar Dare 2) Istigfari Lokacin Sahur 3) Yawan Sadaka 4) Yawan Anbaton Allah a farkon dare da Qarshensa. *Ya cigaba da cewa: Abubuwa hud‘u suna hana arziki: 1) Bacci Bayan Sallar Asubahi 2) Qaranta Sallolin Nafila 3) Yawan Kasala 4) Yin Ha‘inci. *Ya Qara da cewa: *Abubuwa hud‘u suna Qara hasken fuska: 1) Tsoron Allah 2) Cika AlQawari 3) Mutunci 4) Karamci. *Yace: Abubuwa hud‘u suna busar da fuska: 1) Qarya 2) Rashin Kunya 3) Tambaya ba don neman Ilmi ba (Tambayar Qure) 4) Aikata Fajirci. Allah ya tabbatar damu akan tafarkin shiriya, mu rayu mu mutu akai.
Posted on: Fri, 20 Sep 2013 15:23:29 +0000

Trending Topics



re you willing to get
MINISTRO DA SAÚDE FEZ BEM EM RECUAR DA DESASTRADA DA CAMPANHA DO

Recently Viewed Topics




© 2015