ABUBUWAN QI GA MAI AZUMI (MAKARUHAI) Bismillahir-Rah - TopicsExpress



          

ABUBUWAN QI GA MAI AZUMI (MAKARUHAI) Bismillahir-Rah manir-Rahim.... . Abubuwan Qi ga mai Azumi: 1. KAIWA MATUQA WURIN SHAQA RUWA: Ya yin da mai alwala ya zo kan shaqar ruwa, Manzon Allah (S.A.W.) ya kwad‘aitar game da shaqa sosai, amma sai ya togace banda yayin da mutum yake Azumi. Kamar yadda ya tabbata a Hadithin da As‘habus-Sunan da Ibn Kuzaimah suka fitar: Manzon Allah (S.A.W.) yace: ((Ku shaqa ruwa sosai (yayin alwala), sai dai yayin da kuke Azumi)). Malamai suka ce: Annabi (S.A.W.) ya karhanta Mubalaga wurin shaqa ruwa ne tsoron kar ruwan ya wuce zuwa maqogoro ya zama sanadiyyar lalacewar Azumin. 2. SUNBANTA (KISS): Sunbantar mace ma makaruhi ne yayin da mutum yake Azumi, domin yana iya taso da sha‘awar mutum har ya kai ga lalacewar Azumi ta sanadiyyar fitar Maziyyi, ko kuma ya kai ga Saduwa (Jima‘i) wanda yake wajabta kaffara. [Minhajil Muslim: shafi na 239] Allah ya kaimu Ramadana muna masu Imani. (Ameen)
Posted on: Sat, 06 Jul 2013 07:42:15 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015