ALAMOMIN TASHIN KIYAMA An samo Hadisi daga Abu Huraira (R.A.) ya - TopicsExpress



          

ALAMOMIN TASHIN KIYAMA An samo Hadisi daga Abu Huraira (R.A.) ya ce: Wata rana Annabi (S.A.W.) yana zaune a majalisa yana bayar da hadisi ga mutane, sai wani bakauye yazo ya ce: Yaushe ne lokacin tashin kiyama? Sai Manzon Allah (S.A.W.) ya ci gaba da bada hadisi. Sai wasu mutane suka ce: Ya ji abin da ya ce, amma ya ki abin da ya ce, wasu sun ce: Bai ji abin da ya ce ba. Har sai lokacin da ya kare hadisinsa, saan nan ya ce: ina wanda nake ji yana tambayar lokacin tashin kiyama? Ya ce: Ga ni ya Manzon Allah, ya ce, duk lokacin da aka wayi gari babu amana, to, ku saurari zuwan tashin kiyama, ya ce: yaya ake salwantar da ita? Ya ce, Idan aka jibintar da alamari ga wanda bai cancanceshi ba, to, ku saurari zuwan tashin kiyama. Al-Bukhari (59, 6496). Jibintawa: Wato dangana abu. Kuma lalle yazo a cikin ruwayar Hadisi na (6496): Idan aka danganta alamari. Saan nan kuma abin nufI da “almari” jinsin lamura: Shi ne danganta alamari ga wanda bai cancanceshi ba, kamar sanya lamuran shugabancin addini ko alkalanci, ko fatawa da makamantansu, zuwa ga wadanda basu san addini ba. Domin lalle, su shugabanni, Allah Ya sanya amanar bayinSa a hannunsu, Ya kuma wajabta musu yin nasiha a gare su, don haka ya kamata su wakilta wadanda suka san addini, idan suka sanya wadanda ba su san addini ba majibinta, to, lalle ne sun salwantar da amanar da Allah Ya danka hannun su. Fadinsa: Na ke jin: Wato: na ke zatonsa. Wannan ba ya kasancewa sai idan jahilci ya yi rinjaye tare da dauke ilimi. Amma matukar dai ilimi na nan, to, akwai tsammanin gyara a cikin lamarin. Idan kuma haka ya faru, to, yana daga cikin alamomin tashin kiyama, kamar yadda nassin Hadisin ya tabbatar. Kuma Hafiz Ibn Hajar (R.A.) ya ce, Hadisin na da amfani mai yawa. Duba: Fathul Bari (1/142, 143, 334)
Posted on: Mon, 02 Dec 2013 18:10:56 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015