ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta - TopicsExpress



          

ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Marubuci Dr Mansur Sokoto Fitowa ta 12 Shekarar Giwaye Shekarar haifuwar fiyayyen halitta ita ake ce ma shekarar giwaye. Abinda ya faru a wannan shekarar kuwa (shekara ta 571M) shi ne, an yi wani sarki a garin Sanaa ta kasar Yemen wanda ake kiran sa Abrahatal Ashram. Ya mulki wannan garin ne a bayan da ya rinjayi Aryat wani nadadden sarki daga fadar Najashi na kasar Habasha. Wannan juyin mulki da ya yi kuwa ya fusata Najashi ainun, alamarin da ya rikita Abrahata ya sa shi yan kame-kame don neman kubuta daga sharrinsa. A kan haka ne ya aike masa da sakon cewa, zai gina wani babban dakin ibada a bisa tafarkin addininsa mai kuros (Coci) wanda ba a taba jin labarin irin sa ba. Ya dauki alkawarin idan ya kammala wannan Coci zai juya hankalin larabawa da suke yin tururuwa suna bi ta kasarsa don ziyartar dakin Allah da ke Makka. Abrahata ya gina wannan Cocin ya kuma kawata ta matuka bayan ya kashe makudan kudade. A zatonsa idan larabawa suka gan ta hankalinsu zai rajaa gare ta su bar Kaaba. Da wannan shi kuma sai ya samu daukaka ma kansa da birninsa na Sanaa. Ya janyo karin kasuwanci da ciniki ta hanyar yan ziyara sai ya bunkasa tattalin arzikin kasarsa. Ga shi kuma idan haka ta samu ya kubuta daga sharrin Najjashi tun da ya juya hankalin larabawa zuwa bautar Almasihu. Da haka sai ya yi fatar ya jefi tsuntsu hudu kenan da dutse guda. (Mausuat At-Tarikh Al-Islami, na Dr. Ahmad Shalabi, 1/119-120). To, amma ga alama ko tsuntsu guda bai samu ba. Domin kuwa ko da suka ahamo wannan Coci tayi kaca-kaca da najasa! To wa zai yi ibada a daki maras tsarki, wanda ba shi da alfarma da za ta kare shi daga wulakanci?! Ai kuwa gogan sai ya shaci fushi, ya yi rantsuwa sai ya rusa Kaabar da ke Makka tun da yake larabawa ake tuhuma da wannan taadi da aka yi wa Coci. Ya shirya runduna wacce larabawa ba su taba jin irin ta ba. A cikin ta har da giwaye. Ya kuma jagoranci rundunar da kansa. Kafin isowar sa birnin Makka labari ya game sassa. Kuma duk wani yunkuri da larabawa suka yi domin yin arangama da shi da hana shi isa Makka sai da ya ci tura. Amma fa sun yi amanna cewa, Allah shi ne mai wannan dakin kuma ba zai kyale shi ba. Misali, a kan hanyarsa ta zuwa Makka, kabilun larabawa da dama sun tare Abrahata kuma suka yake shi amma ya tarwatsa su. Tun daga kasar Yemen wani sadauki da ake kira Zu-Nafar ya ci karo da shi tare da rundunarsa amma tuni giwaye suka tattaka su. Kabilun Khasam; Shahran da Nahis su ma sun tura na su jarumawa aka fatattake su. Da rundunar Abrahata ta iso Taif sai suka bace hanya. Kuma duk wanda suka tambaya sai ya ki dora su a kan hanya. Sai da suka samu wani shakiyyin mutum ana ce da shi Abu Rigal shi ya yi ma su jagora amma Allah bai yi masa jinkiri ba, domin ba su yi nisa ba malaikan mutuwa ya sharbe shi. Shi ne wanda larabawa ke jifar kabarinsa har in da yau ke magana a wani kauye da ake kira Mugammas a hanyar Taifa zuwa Makka. (As-Sirah An-Nabawiyyah, na Ibn Hisham 1/58-60). Allah sarkin sarauta! Ashe dai ko ina akwai marasa arziki a cikin duniya. Lokaci da Abrahata ya isa Makka sai mutanen garin duk suka taru wurin dakin Allah suka makalkale gare shi suna kai kara ga maabocinsa. Saannan suka fice daga garin suna jiran faruwar ikon Allah gwanin sarki. A lokacin da ayarin Abrahata ya sauka wajen gari, Abdulmuttalib ya samu ganawa da shi in da ya nemi a mayar ma sa da rakumansa guda 200 da wannan runduna ta mamaye. A cikin taajjubi Abrahata ya tambaye shi, rakumanka ne suka fi maka muhimmanci ko wannan daki da ka gaji ibada a cikin sa daga kaka da kakanni?! Sai Abdulmuttalibi ya kada baki ya ce ma sa: Ba haka ba ne. Rakuma mallakina ne, shi ya sa nake neman abina. Shi kuma wannan daki yana da mai shi kuma zai kare shi. Ba zai bari kome ya same shi ba. Kangara irin ta kafirci ta sa Abrahata duk da jin wannan magana bai karaya ba balle ya fasa abinda ya yi niyya. Amma ya mayar ma da Abdulmuttalibi duk dukiyarsa da aka riga aka kwace can da farko. An ba da labarin cewa, su wadannan giwaye sun turje a bayan garin Makka duk lokacin da aka fuskantar da su zuwa garin. Amma idan aka karkata su zuwa hanyar komawa sai su zura da gudu. Kaico! In da akwai basira da kafirai sun gane wannan ishara. Amma ina! Da suka ci gaba da nacewa a kan shiga garin ne sai Allah ya aiko ma su wasu irin tsuntsaye masu manyan kawuna wadanda ba a taba ganin irin su ba, suna dauke da duwatsun wuta suna jifar su da su. Duk wanda suka samu kuwa ba shi kai labari. Da haka suka tarwatse rundunar kowa ya san inda dare ya yi ma sa. Shi kam uban tafiyar; Abrahata faduwa ya yi a tagayyare duk jikinsa ya lalace. Suka dauke shi suka koma da shi gida yatsunsa suna sancewa guda guda, ya cika a nakkashe, Allah ya wulakanta shi. (As-Sirah An-Nabawiyyah, Ibn Hisham 1/58-60 da Fathul Bari 12/210-216).
Posted on: Tue, 19 Nov 2013 21:11:05 +0000

© 2015