Al-Qurani na cewa INNA LLAHA WA MALAIKATAHU YUSALLUNA ALA NABIYY - TopicsExpress



          

Al-Qurani na cewa INNA LLAHA WA MALAIKATAHU YUSALLUNA ALA NABIYY YAAYYU ALLADHINA AMANU SALLU ALAIHI WA SALLI MUTASLIMA YUSALLUNA da ace yadda kalmar take a Sallah haka take a nan ma in an dauka ance salati. Shin da wannan salati da wannan kalma ta sallah babu wani bambanci a ciki, sai aka ce Allah da Malaiku suna yiwa Manzo SAWWW salati, to wani irin salati. . ?? Wani zai ce Allahumma Salli Alaa Muhammad... Allah ka yiwa Manzo SAWWW salati kuma Yusalluna Ala Nabiyy aka ce, ku duba fa ku gani. Duk tunanin ka yadda duk ya kai ya kawo a girman Allah din, tunanin ka da yadda kayi wai kana ganin girmar Allah domin WAMA QADARALLAHU HAKKA KADRIHI ne. Saboda haka masu daawah da WAI Qitab wa Sunnah basu girmama Allah girmama wa ba. Domin duk abinda suke fada suce Allah kaza da kaza ai duk bai wuce yadda Mushrikan makkah suke fada ba. Duk yadda yayi wanda yake daawah ya san Allah madamar bai yiwa hanyar wulaya ba, to bai san Allah ba. Kuma duk wanda yake daawah yasan Allah idan ka bishi kawai zaka ga sanin Allahn nasa baida bambanci da na mushrikai, babu bambanci da na yahudawa, baida bambanci da na christians. To ina sanin Allahn a nan kenan. . . . ??? Saboda haka duk wanda ya san Allah dole sai biyo ta wannan Mujaddadin da Annabi SAWWW yake fada: FI KULLI LIATIN MUJADDADAN amma sai ya kara da cewa MAN MATA WALAM YAARIF LIMAMA JAMALIHIN FAQAD MATA MAUTIL JAHILIN maana duk wanda ya mutu bai san Imamun zamaninsa ba to yayi mutuwar jahiliyyah. Duk wanda yasan addini yasan abinda ake nufi da mutuwar jahiliyyah (wanda ya mutu bai san zuwar Manzon Allah SAW ba) DA FATAN ALKHAIRI!!! Amin summa Amin
Posted on: Fri, 29 Nov 2013 08:47:17 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015