Allah sarki, akwai abu mai dadi kamar ka sami mace ta qwarai wace - TopicsExpress



          

Allah sarki, akwai abu mai dadi kamar ka sami mace ta qwarai wace zuciyarta gaba daya tana hannunka? Haka Allah ya dora mana, kwanciyar hankalinmu tana hannunsu. Dan uwa daure ka nemi macen da kake so take sonka, mai mutunci da sanin ya kamata, mace mai kunya da kawaici da nuna qauna a aikace ba a baki ba, wace kullum tana bayanka don share maka hawaye. Dan uwa dena hange-hange tsaya ka tanaji kwanciyar hankalinka, yi tunani kafin ka tura kanka: Shin wannan ta dace dani? Anya za ta iya barin komai na ta domin yi min hidima? Shin qaunata take yi ko abin hannuna take so? Wai kuwa za ta mutunta yan uwana kuwa da sauran jamaata? Akwai kyawawan mata a duniya, a kuma duk inda ka jefa qafa, amma ka sani, in fa ka aure ta don kyaunta kawai da zarar ka fara biyan bukatunka shikenan. Yi qoqari ka auro wace za ta riqa tunanin rayuwarka kamar yadda take tunanin na ta. Wacce in kana gida ba ta da wani sukuni sai abin da ranka yake so. In salla zaka yi tana bayanka amma adduarta Allah ya azurtaka ya kare mata kai. In ka fita hankalinta yana kanka har sai ka dawo. In ka ga ta yi murmushi to ta ga kwanciyar hankalinka. In kana waje sai ta yi nafila tana roqon Allah ya dawo da kai lafiya. In ka ga ta yi ado to kana gida, qoqarinta ta janyo hankalinka. Wacce jin dadinka shi ne na ta. Allah ka hada mu da masoya na gaskiya, masu taimaka mana neman aljanna.
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 23:05:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015