BAYANI A KAN ILIMIN ALKUR’ANI (Mu’ujizarsa, Saukarsa, Yadda - TopicsExpress



          

BAYANI A KAN ILIMIN ALKUR’ANI (Mu’ujizarsa, Saukarsa, Yadda Aka Tattara Shi Da Falalar Karatunsa) Wallafar: Shaikh Aliyu Said Gamawa *** Darasi Na Sha Tara (19) *** ================================== HIKIMAR LISSAFI A CIKIN ALKUR’ANI (Daga Dr. Ahmad Deedaat) Akwai hikimomi masu yawa a cikin Alkur’ani mai girma. Shi Alkur’ani gagara badau ne, babu wani abu da ya yi kusa da shi wajen hikima da fayyacewa. Allah (S.W.T) Ya fada a cikin Alkur’ani mai girma cewa : «Ka ce, lallai ne idan mutane da aljanu suka taru domin su zo da misalin Alkur’ani, ba za su zo da misalinsa ba. Kuma ko da sashinsu ya kasance mataimaki ga sashi.» (Suratul Isra’i 17:88). Don haka na kawo misalai da za su tabbatar da dukkan masu imani, da ma wadanda ke tantamar cewa littafin Alkur’ani ba saukakken littafi ne daga Allah ba, ko suke cewa wani ne ya kirkiro shi. Misalai da za su nuna mu’ujizar Alkur’ani wadanda Sheikh Ahmad Deedat a cikin littafinsa: ‘ALKUR’AN THE ULTIMATE MIRACLE’ ya kawo misalai a kan zamowar littafin Alkur’ani gagara gasa. Sai dai wadannan misalai ya kawo su ne a bisa ijtihadinsa, kuma mai ijtihad yana dacewa kuma yana iya yin kuskure. Ya kawo misalai kamar haka: 1. Farkon lambar lissafi a kirge ita ce daya (1), ta karshen kuwa ita ce tara (9), to idan aka jera su (a rubuce) za a sami goma sha tara (19). Wanann lambar goma sha tara (19) ita ce mai kunshe da hikima (irin ta lissafi) a cikin Alkur’ani. An ambaci wannan lamba ta 19 a cikin Alkur’ani wajen bayani a kan matsayin wutar Sakar, amma wannan adadi ya yi daidai da hikimar lissafin da ke kunshe a cikin littafin Allah mai girma: عليها تسعة عشر “A kanta akwai matsara goma sha tara.” (Suratul Muddathir: 30). To wannan adadi ya shiga lissafin bakake, kalmomi, ayoyi da kuma surorin Alkur’ani. 2. Bakaken da ke cikin ayar: بسم الله الرحمن الرحيم “BISILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM” da rubutun larabci haruffa goma sha tara ne. 3. Adadin kalmomin da ke cikin «Basmala» su hudu ne watau Ismi, Allahu, Arrahmanu da Arrahimu. Kowane kalma yawanta a cikin Alkur’ani zai iya rabuwa daidai da goma sha tara. Watau: (i) Ismi : Guda goma sha tara 19 ne a cikin Alkur’ani, watau daidai lissafin adadin goma sha tara. (ii) Allahu : Guda 2,698 ne cikin Alkur’ani wanda ya yi daidai da adadin goma sha tara har sau dari da arba’in da biyu (2698 ÷ 9 = 142) (iii) Arrahmanu : Guda 59 ne cikin Alkur’ani wanda ya yi daidai da adadin goma sha tara har sau shida cif-cif (114 ÷ 19 = 6). 4. Adadin ayoyin Sura ta farko wadda aka saukar daga cikin Alkur’ani (watau Suratul Alaq) ayoyi goma sha tara ne daidai. 5. Daga kan Suratul Alaq (Iqra’a) wadda ita ce Sura ta farko da aka saukar, zuwa Suratun Nasi, watau Sura ta karshe a jerin Surorin da ke cikin Alkur’ani, akwai adadin Surori goma sha tara ne daidai. 6. Sannan daga Suratul Fatiha (Sura ta farko a jerin Suraron cikin Alkur’ani), zuwa Suratul Alaq (watau Sura ta farko da aka saukar wa Manzon Allah (S.A.W); akwai Surori casa’in da biyar. Wannan adadi na Surori 95 ya yi daidai da goma sha tara har sau biyar (95 ÷ 19 = 5). 7. Akwai Surorin da suke farawa da wasu haruffa, (watau kuramen bakake) wadanda ba wanda ya san hakikanin ma’anarsu, sai Allah. Wadannan Surori su ashirin da takwas (28) ne, kuma adadin dukkan haruffa da surorin suka fara da su (a cikin wadanann surori) ana iya raba su daidai da goma sha tara ba tare da wani gibi ba. Misali : (a) Surorin da suka fara da Alif, Lam, Mim, الم (A.L.M) sun kasance kamar haka : A M L * Bakara 2,195 3,204 4,592 * Ali’Imrana 251 1,888 2578 * A’rafi 1,165 1,523 2,572 * Ra’ad 260 479 625 * Ankabut 347 554 784 * Rum 318 396 545 * Lukman 177 298 348 * Sajda 158 754 268 JIMLA 5,871 8,493 12,312 i) Adadin harafin Alifun, 12,312 ya yi daidai da goma sha tara har sau dari shida da arba’in da takwas cif, babu wani gibi (12,312 ÷ 19 =648). ii) Adadin harafin Lamum 8,493 ya yi daidai da goma sha tara sau dari hudu da arba’in da bakwai (8,493 ÷ 447). iii) Adadin harafin Mimum 5,817 ya yi daidai da goma sha tara har sau dari uku da tara, (5817 ÷ 19 = 309) (b) Suratul Maryam ta fara da haruffan ‘Kaf-Ha-Ya-Ain-Sad’. A nan yawan wadannan haruffan cikin wannan Sura kai 798 wanda ya yi daidai da goma sha tara har sau arba’in da biyu. Kaf – 137, Ha – 168, Ya – 345, Ain – 122, Sad – 26 (137+168+345+122+26) wanda ya yi daidai da dari bakwai da casa’in da takwas (798 ÷ 19 = 42). (c) A Suratul Nun kuma an maimaita wannan harafi (na Nun) har sau 133, wanda ya yi daidai da goma sha tara sau bakwai cif. (133 ÷ 19 = 7). 8. Adadin Surorin Alkur’ani guda 114 ya yi daidai da goma sha tara sau shida. (144 ÷ 19 = 6). 9. Yawan ayar ‘Basmala’ wadda aka bude dukkan Surori da ke Alkur’ani banda Suratul Tauba (Bara’atun Minallahi), 133 ne, an kawo cikon na 114 a wata Sura, don inganta lissafin hikimar goma sha tara cikin Alkur’ani. Wannan ciko ya zo cikin Suratul Namli, hakan kuma ya sa adadin ayar cikin Alkur’ani ya yi daidai da goma sha tara sau shida. Wannan kadan ke nan daga cikin hikimar lissafi da aka tsara Alkur’ani da shi. Wallahu A’alamu
Posted on: Tue, 29 Oct 2013 10:21:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015