BIYAYYA GA IYAYE //1 ﻪﻴﻠﻋ ﻪﻠﻟﺍ ﻰﻠﺻ - TopicsExpress



          

BIYAYYA GA IYAYE //1 ﻪﻴﻠﻋ ﻪﻠﻟﺍ ﻰﻠﺻ ﻲﺒﻨﻟﺍ ﺖﻟﺄﺳ :ﻝﺎﻗ ﻪﻨﻋ ﻪﻠﻟﺍ ﻲﺿﺭ ﻪﻠﻟﺍ ﺪﺒﻋ ﻦﻋ ﻰﻠﻋ ﺓﻼﺼﻟﺍ :ﻝﺎﻗ ؟ﻞﺟﻭ ﺰﻋ ﻪﻠﻟﺍ ﻰﻟﺇ ﺐﺣﺃ ﻞﻤﻌﻟﺍ ﻱﺃ :ﻢﻠﺳﻭ ﻢﺛ :ﻝﺎﻗ ؟ﻱﺃ ﻢﺛ :ﺖﻠﻗ ،ﻦﻳﺪﻟﺍﻮﻟﺍ ﺮﺑ ﻢﺛ :ﻝﺎﻗ ؟ﻱﺃ ﻢﺛ :ﺖﻠﻗ ،ﺎﻬﺘﻗﻭ ﻲﻧﺩﺍﺰﻟ ﻪﺗﺩﺰﺘﺳﺍ ﻮﻟﻭ ،ﻦﻬﺑ ﻲﻨﺛﺪﺣ: ﻝﺎﻗ ﻪﻠﻟﺍ ﻞﻴﺒﺳ ﻲﻓ ﺩﺎﻬﺠﻟﺍ Abdullahi (RA) yace: Na tambayi Manzon Allah (SAW) cewa wane aikine Allah mai girma da daukaka yafi so sai yace: "Sallah akan lokacinta, sai nace sannan me? Sai yace: Bin Iyaye, sai nace sannan me? Sai yace: Sannan Jihadi don daukaka kalmar Allah. Sannan yace ya fada mun wainnan abubuwan kuma da naso ya karamun da ya karamin". ﺎﺿﺭ ﻲﻓ ﺏﺮﻟﺍ ﺎﺿﺭ :ﻝﺎﻗ ،ﻪﻨﻋ ﻪﻠﻟﺍ ﻲﺿﺭ ﺮﻤﻋ ﻦﺑ ﻪﻠﻟﺍ ﺪﺒﻋ ﻦﻋ ﻂﺨﺳ ﻲﻓ ﺏﺮﻟﺍ ﻂﺨﺳﻭ ،ﺪﻟﺍﻮﻟﺍ Abdullahi bin Umar (RA) yace: Yardan Allah yana cikin yardan iyaye, kuma fushin Allah yana cikin fushin iyaye. Wato wanda iyayensa suka yarda dashi to Allah zai yarda shi, haka ma idan iyayensa suna fushi dashi to Allah ma yana fushi dashi. A wani hadisin kuma Abdullahi dan Abbas yace: Lallai ni ban san wani aiki wanda yafi kusanci zuwa ga Allah ba fiye da biyayya ga Mahaifiya. [Duka hadisan suna cikin Al-Adabul Mufrad]. Allah kasa mu kasance masu farantama Iyayen mu.... (Allahumma-Ameeeeen)....
Posted on: Wed, 02 Oct 2013 07:22:00 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015