Baban Manar Alqasim ALLAH YA ISA BAN YAFE BA // 32 Tambayar - TopicsExpress



          

Baban Manar Alqasim ALLAH YA ISA BAN YAFE BA // 32 Tambayar da Sule ya yi wa Sani ta dan jefa shi cikin tunanin yadda zai ba da amsar, domin kuwa kullum yana tare da ita, wani lokaci ma a dakinsa take wuni ba tare da wani muharrami ko qawa ba, ba dai wanda zai iya fadin abin da yake gudana a tsakaninsu, sai irin maganganun da shi Sanin yake fada wa Sule, ita ko Mari tana da cikakkiyar amincewa da shi, kuma ko kanta ya juye ba za ta iya gaya wa wani abin da yake faruwa a tsakaninta da shi ba, illa dai saurayinta ne da kuma yake mata alkawarin zai aure ta, a ganinta tun da ta yarda da shi, kuma nan gaba matarsa za ta zama kamar yadda ya yi mata alkawari, shi kenan yana iya samun duk abin da yake nema tare da ita, shi ma ya tabbatar ma ta da cewa komai na ta na sa ne lokaci kawai ake jira da sanarwa, bai dai ta6a zuwa gidansu ba a matsayin manemi, bare ya tura wani daga cikin magabatansa, hasali ma ba wanda ya san shi daga cikin iyayen na ta, sai maganar ta yi daidai da ta Ado Ahmad a wani tsohon littafinsa na Masoyan Zamani in da yake nuna cewa kaza in ka zuba mata tsaba ko a wuya sai ka cafke ta, Fatu dai tana samun alhairai daga Sale don haka bari a gama tatse shi sannan daga qarshe a yi maganar auren, ta manta da cewa namiji sunansa kenan. Irin wannan sakacin na iyaye ya yi kama da wanda malama Kawthar take magana a wata lakca da ta yi kwanaki, in da wani uba ya cewa yarsa ya gaji da biya mata kudin makaranta, sai ta san yadda za ta yi ta ci gaba da daukan nauyin kanta, tare da sanin cewa ba ta da wasu hanyoyin samun kudi, kuma ba ta da wata kama sayar in ba abu guda daya kacal ba, wato matantakarta, iyayen Mari sun gajiya wajen ba ta kariya ta masamman a daidai wannan shekara mai matuqar hatsarin gaske, wace kowace mace take ta fafutukar neman mazauni mai kyau da za ta rufa wa kanta asiri, mahaifiyar Mari din na sane da cewa wani abu yana faruwa ko ba ta sane, akwai dai kudi da yarta take yawan kawo mata daga wani saurayi, wanda har lokacin ba ta ta6a saka shi a idonta ba, ta dai tambayi Marin in aurenta zai yi, shi kuma ya tabbatar mata da haka, shikenan abin da ake son bincikawa ya gama cika, matuqar yana miqa abubuwan da ake buqata a wurinsa. A 6angaren Sani kuwa akwai sa6anin hakan, don shi bai ta6a kawo wa zuciyarsa cewa zai yi aure nan kusa ba, koma ya yi niyyar yi, ya bayyana wa babban amininsa Sule cewa ba zai iya auren Mari ba, don kuwa yar iska ce, wannan kalmar a wurinsu tana nufin macen da maza suke lalata da ita, ba tare da mai da ita sanaa ba, Sani ya fallasa cewa hakan takan faru tsakaninsa da Mari, mafi yawan abokansa kallon da suke mata kenan ita ba ta sani ba, galibin samarin da suke lalata da yammata ba sa 6oye wa abokansu abubuwan da suka yi da su, yammatan ne dai abin tausayi, don kowa yana ganinsu tsirara su ba su sani ba, su suna qoqarin rufa wa saurayin asiri, shi kuma yana fallasa su a koina, da haka ake cewa wance ta shahara, sai kowa ya yi qoqarin zuwa diban rabonsa, ita kuwa sai ta yi tsammanin tsabar qauna ce da daukaka da Allah SW ya yi mata, a daidai wannan lokacin ko sadaka za a yi da ita, duk cikinsu ba mai yarda ya dauka, duk da tsabar kudin da yake miqa mata don ganin ya kai ga biyan buqata. I to in ka lura akwai bambanci, duk abin da yake faruwa a tsakaninmu da yardarta ake yi, ni ban ta6a saka ta dole ba, ita take zuwa dakina da kanta ba sakawa nake yi a dauko ta ba, sannan in da ba bisa yardarta ake yi ba to da in ya faru sau daya ban sake ganinta, amma ka ga kullum sai ta zo ai, wallahi wata rana ita take matsa min sai na jira ta in ji Sani, ga alama Sule ya dan tausaya game da lamarin, har da kasancewar duk dai tafiyarsu guda ce Ina ganin kamar za ka cuci rayuwarta matuqar ba ka aure ta ba, duba fa, ta ba ka amanar kanta, ta nuna maka iya qaunar da take maka sabo da Allah, duk qawayenta sun san cewa kai kake nemanta kuma tana alfahari da kai a wajen duk wata qawarta, har ma ta kori wasu samarin a dalilinka wadan da dukanmu mun tabbata aurenta suke ninyar yi, sannan a qarshe kuma ka ce ba da kai ba gaskiya in ka yi haka ba wani mai iya saka ma ta sai Allah, kuma alhakinta yana iya kama ka, don kuwa za ta bar ka da Allah. Sani ya saurari maganar Sule sosai,to amma bai gusa daga kan bakansa ba, sai ma dada tabbatarwa ya yi ba zai iya aurenta ba Jinan Sule! ya dan jawo hankalinsa Ba wani namiji mai kishin iyalinsa da zai auri wata yar iska... Ya za ka yanke irin wannan hukuncin bayan kuwa da kai take yi? Sule kenan ya katse shi, amma sai ya ba shi amsa da cewa Na farko dai ba ta da kamun kai, tun da ka ga tana yin wannan kafin aure, in da take tsoron fitan wani abu da zai iya hana ta samun miji, ya kake gani idan ta riga ta yi aure yadda ba wani zancen tonon asiri? Harka da kowace iriyar mace wannan abu ne mai matuqar sauqi amma aure da yar iska, wannan kuma wani abu ne na daban, ni in ba sakarai ba ai ba zan iya ba, ita ma ka lura mana, in da tana da hankali ai ya isa ta fahimci abin da ake ciki, ba fa wani abu da na ta6a yi wanda zai nuna cewa ina da niyyar aurenta hirar Sani da Sule ba wata aba ba ce da za a ce wane ke da gaskiya ko wane bai da ita, amma wani irin darasi ya kamata kowace budurwa ta dauka a ciki? Irin wannan alaqar da take tsakanin Sani da Mari, da miqa wuya ta gaskiya wace Mari ta yi wa Sani, sam shi ko a zuciyarsa kudinsa kawai yake morewa, amma ba shi da wata manufa ko qalilan ta yin rayuwa da Mari, haka ire-iren aurarrakin wucin gadi suke, namijin zai ciro maqudan kudi ya ba macen, don dai kawai ya biya wa kansa buqata na wani lokaci, amma ba shi da wata manufa ta rayuwa da ita, ya dai biya buqatarsa a lokacin da ta taso masa, a nan ba a wata maganar qauna da soyayya don kuwa, shaawa ce zalla ya rage wa kansa, ita kuma macen ita ta san yadda za ta tafiyar da rayuwarta nan gaba, shi dai ya ba ta haqqinta na kudi bai rage mata komai ba, don haka yake ganin bai zalunce ta ba, wani ma zai ba da abin da ya bayar ya kuma sami abin da ya samu, amma duk haqqoqin da matansa suke da su, ba ta da su, ko da kuwa an kira ta da suna matarsa, Sule ya ce To ina ganin ka daure ka bayyana ma ta abin da ake ciki tun yanzu kafin lamari ya yi nisa Sani ya girgiza kai Baba ba yanzu ba ka ji, ka bari mutum ya gama more kudinsa, wallahi in na shaida mata wani abu ban sake ganinta ka ga ai na yi asara ko?!
Posted on: Thu, 31 Oct 2013 15:47:32 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015