Burina guda daya ne. Abarni da kaunarka Rasulallah. Dik - TopicsExpress



          

Burina guda daya ne. Abarni da kaunarka Rasulallah. Dik Rintsi kuma duk wuya Kaina Rike Shafiullah. Yarda dani kamun Lamuni Agefenka kace dani Zau zona. Dan kaine Muradin Zuciyata. Ya Ilahina Rabbi mai Girma Nai Roko ka Haskaka kirjina. Kaban basira fasaha kada dan Domin na baige Farin cikina. Zababbe Shugaba dan Shugaba baban Shugaba Muhammad Rasulallah Wallahi Kaina Rike Abin Kauna. Rabbi kasa hikima A Harshena dan na Ladabtar da Bakina Da Baigen sa. Tsarkake zuciyata Khalikina Kabar mun sansa Kadai yamamaye duk Sashen dake ajikina. Nazamto Adare Rana Yabansa shine aikina. Nada de ina fama da cuta ajikina ganinka Rasulu shine Samun Lafiyata. Allahu Arrahimu Yarje mun ganinsa koda acikin bacci nane inna gansa nasan Hakika na yantu. Rabbi kasa Aduk.lokacin da ka bukaci Ruhina yazamana Ina bisa Tafarki maikyau Na bauta agareka Ya Ubangijina. Allah kare dukkan gabobina daga fadawa sharri nasa Shaidan Bani kariya Ilahi daga Afkawa Rudu Nasa Zamani. Dogaro agareka nayi Allah Karfafa Imani na Yawuce duk hasashen insi wal-jinni dama hasashena nida kaina. Assmaul Husnah Ya ga Harun Nake begen Rasulu Shine aikina. Rabbi kasheni ina mai Rero Baitika agaresa Sayyadis-Sadati Masha Yabo Ahmadu Aminullahi Sirrin Zuciyata Muradina. Anan zan tsagaita da Yabon bawai dan nagajiba sai dan karancin Ilimi agareni Rabbi kaimun agaji. Akan hanyar dana kama tazarce kar makiya Su sassare ni. Allahumma Salli wa sallim Ala Sayyadina Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam Allah kajikan. Umar Abdulazeez Fadar Begen Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam. Dama duk wadanda suka rigamu gidan gaskiya Ameen. Allah kasa intamu tazo mucika da Imani tare da Kalmar. Shahada Ameen Thumma Ameen. #Husnet
Posted on: Sat, 19 Oct 2013 00:15:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015