#CIGAN_KISSAR_SARKI_MALIKUSSAIFI. In baxa ku manta ba - TopicsExpress



          

#CIGAN_KISSAR_SARKI_MALIKUSSAIFI. In baxa ku manta ba abaya muntsaya a inda waziri baharu ya aika bawansa da takarda wacce ya fayyace wa sarki #ziyazan lbrn abin da ke faruwa. Bawan nan nasa yakama hanya yana ta tafiya, bayan kwana uku ya isa #Hamraul_Yemen yariga mutanen sarki SAIFU AL ARDU yana xuwa ya fada yanemi iso akamar ixini yashiga yafadi gaban sarki #Ziyaxan yayi gaisuwa , ya mika takarda , da sarki ziyaxan yakaranta yayi matukar mamaki, sai bawan yace wa sarki ayi maxa a sallamesa sbd yana tsoron kar jama,ar saifu al ardu suxo su riske sa. sarki #ziyazan yayi mar kyauta ya sallemesa. Bayan saa uku da tafiyar bawan nan saiga jama,ar sarki saifu al ardu sun shigo suma suna xuwa sukayi mar gaisuwa sannan suka mika wannan kuyangar wato #Kamriyya ga sarki #Ziyyaxan lita, sarki ya karba ya nuna kmr ma baisan nakircin d suka kulla masaba, sannan ya basu masauki suka kwana washe gari suka juya. Wata rana sai Sarki #Zayyazan ya kadai ce da wannan kuyangar da aka kawo masa , ya xare takobi yace ta fiddo guban nan da aka bata ko kuma ya hallakata, da taga dagaske yake sai taciro akanta ta mika masa, awannan daren ya tara da ita kuma tasamu ciki. da Sarki yaga tasamu ciki sai sarki #Ziyyaxan ya kira wani malaminsa akan yabuga mar kasa akan wannan cikin, da malamin ya biga kasa sai yacewa sarki ai wannan namiji ne, kuma shine akansa adduar nan ta kakanku Annabi Nuhu xata fadawa akan shi xai mulki duniya. da jin haka sarki yadinga nunawa #Kamriyya kauna da tattalinta, da cikinta yakai wata hudu sai sarki #Ziyazanun ya kwanta ciwon ajali in da yayi wasiyya d cewa idan ya mu2 #kamriyya tahau gadon sarauta taci gaba da mulki har ta haihu, idan dan da tahaifa yagirma tasauka tabashi mulkinsa ya hau, bayan yan kwanaki sarki #ziyazan ya cika aka nada kamriyya taci gaba da mulkin HAMRA UL YEMEN. Da aka samu yan watanni sai #Kamriyya ta ringa debo mutanen Habasha tana korar mutenen Hamra ul yemen a majalisa. cikin dan kan kanin lokaci duk ta kori mutanen Ziyazan mai mu2wa a majalisa.bayan da cikin ta yacika wata tarasai Kamriyya ta haihu ta haifi dana miji kyakyawa fari balarabe kmr ubansa, bayan haihuwar da kwana daya Kamriyya ta shirya jariri tafitoa dashi xuwa fada ta ajiye agefe kan shinfida irinta yayan sarakuna, jama,ah sukaita xuwa suna kwasar gaisuwa ,kan suje gun kamriyya sai sutafi gun yaro suyi gaisuwa suna cewa sarkin mu na gobe, sannan sudawo gunta suyi gaisuwa. nan kamriyya taga yanda 2n yanxu anfara mantawa da ita kuma tasan nan gabama kila tubeta xa ai anada yaro kan mulki, sai kishi yakamata sbd ta dana giyar mulki, amma saita boye rashin damuwarta sai tadauki jariri tayi gida dashi bayan da dare yayi sai tafara 2nanin yadda xatayi dashi jaririn, cen ta dauko wuka tasamar a wuyansa zata yanka sai tafasa, sai takara sawa xata yankai sai tafasa, da takara kaiwa a karo na uku sai wata tsohuwa kuyanga taganta tace haba yarinya mai wannan yaro yamiki kike neman hallakashi........ SHIN KAMRIYYA TANA YANKA YARON NE KO TANA FASAWA? YA LBRN SARKI SAIFU AR ARDU? ZANCI GABA NAN DA BADA JIMAWABA NAKU AKULUM TUKUR IBN ABUBAKAR
Posted on: Mon, 25 Nov 2013 05:32:40 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015