Daga: Al-Ameen Abdullahi Idris - TopicsExpress



          

Daga: Al-Ameen Abdullahi Idris U/Mu’azu (08027451174, 08035814046) TAMBAYA TA 29: Wannan takarda ce da wata baiwar Allah budurwa `yar jami’a (University) ta aiko dashi, ta ce Assalamu alaikum Malam! Mahaifina ya hana masoyina ya aure ni don shi talaka ne, ni kuma wannan bai dame ni ba, saboda yana bin Musulunci sau da qafa, kuma yana xan kasuwancinsa, na tabbata zai iya samun xan abin da zai iya riqe ni dashi, nikan ko kusa kasancewarsa talaka bai dame ni ba, koda a cikin runfar zana zai zauna dani ni na yarda ya aure ni ya zauna dani, arziqi nufin Allah ne. Kuma mahaifin nawa ya ce dani sai kin yi Digiri, kin qara tsada kan in aurar dake. In kinyi karatu ba zaki sha wahala ba, koda bayan mutuwata ko mutuwar mijinki a rayuwarki, rayuwa fa akwai wahala. Ni kan bana son kowa sai shi wannan saurayin, kuma wallahi na matsu ayi mana aure ba tare da vata lokaci ba. Amma dole na bi ra’ayin babana don ina jin tsoro da kuma kunyarsa. A dole ya saka ni a jami’a, amma abin haushi da takaici akwai wata (Club) a cikin jami’a, ta munafukan malamai da `yan iskan xalibai maza da mata, da lalatattun manyan gari. Manufarsu abu guda xaya ne tak! Shi ne: Sai sun yi (kawar da budurcin) disvirgining din duk wata budurwa a jami’a, ko `yar wace ce, kuma ko ta halin qaqa, ta hanyar:- qawaye, kudi, yaudara, dabara, tsoratarwa da sauransu. Ma’ana duk wata `ya data je jami’a, sai an kama ta an kawar da budurcinta koda qarfin tsiya. Akwai wannan qungiyiyar ta tirniqe yanzu a ciin jami’a. ta qunshi waxanda daga cikin malaman jami’a, da waxansu daga cikin dalibai maza da mata. Kuma ana amfani da kowanne irin abu. Malam don Allah ka yi bayani gamsassu askan wadannan tambayoyi ta gidan talabijin da radiyo a cikin Ramadan an fi saurare da kuma daukan nasiha a cikin wannan wata. Ko Allah (Ta’ala) zai sa mahaifina yaji, ya wa’aztu. Tambayoyin nawa sune:- 1. Na daya: Malam yanzu idan na fada hannun waxannan fasiqai (Allah ya kiyaye) shin zunubin nawa ne ko na mahaifina? 2. Na biyu: Labarin Raping (wato fyade) a jami’a boye su ake yi domin gudun jin kunya da tsoron vacin suna, koda anyi musu fyade basa fada don sunansu zai vaci, kuma za ki yi ta jin kunya ana ganin ki da abin, amma kusan (96%) na budurwayen jami’ar nan (wato Jami’ar Maiduguri) an lalata su. Ta ce da rana tsaka ma akan kama yarinya budurwa cikin mota ayi nesa da ita daga inda idon mutane suke a cikin jami’a ayi lalata da ita. Sannan a bata qwayoyin hana xaukar ciki. Kuma ace da ita ko yaushe idan ki ka buqaci wadannan qwayoyin akwai su, a kyauta. Kya iya holewarki yadda ki ke so. Wasu matan daga nan fa shi kenan sai su zarce a cikin tafarkin lalaci. Ta hanyar shan waxannan qwayoyi. Tambayar anan ita ce! Shin amfani da irin wannan magani shin ba kisan jariri bane? 3. Na uku: Malam mai yasa bakwa yawaita nasiha akan ire-iren waxannan matsaloli? Ina tsoron Alllah (Subhanahu Wa Ta’ala) zai tambaye ku ku malamai. Wallahi yawancin iyaye gafalallu ne bisa ababen dake faruwa game da ya’yansu mata a jami’a, ko yaya mutum ya yarda da yarsa! Akwai hadari a cikin al’amarin, tunda akan lalatasu rana tsaka da qarfi da yaji badon suna so ba, bawai don su yan iska bane, malam don Allah ku yi kasa-kasai na musamman akan haxarin karatun ya mace a jami’a. Misali: Munafuqan malamai suna kayar da yan mata daga jarabawa, idan sun qi miqa wuya a yi lalata dasu. Amma wadanda suka miqa wuya kuwa! Tunda farkon fari ba zasu fadi a jarabawa ba. Don Allah ci ko faduwar ya mace a jarabawa ta jami’a ba ya zama abin tayar da hankali?. Idan ance yarka ta ci jarabawa! Koda ko daqoqarinta ta ci jarabawar? Ai wannan zai kawo zargi ga iyayen arziqi ba za su natsu ba. Lalle sai ya mace ta yi karatu a irin wadannan wurare ne? dole ne sai ta yi hakan? 4. Na hudu: Yanzu idan na yiwa mahaifina tawaye na qi karatu kotu ta aurar dani ga wanda nake so! Ina da laifi a wurin Allah? Malam don Allah ka yiwa iyaye nasiha su aurar da ya’yansu ga masoyansu akan lokaci, don wallahi kusan dari bisa dari na yan mata bamu da haquri. Kunya ce take hana mu mu bayyanawa iyayen haka, shin ba zasu tuna yadda suke ji ba, yadda idan su sha’awa ta sa su suka matsu da junansu! Ai mu ma yan Adam ne kamar su, muna matsuwa. Iyayenmu mata su ya kamata su taimaka mana su aurar damu da wuri kafin a saka mu a jami’a. Kuma yawancin yan matan da suke sha’awar karatu a jami’a suna yin hakan ne don neman duniya ne kawai, badon saboda neman lahira ba. Haka nan iyayen da suka matsa ‘ya’yansu sai sun yi karatu a jami’a su ma don menan duniya ne kawai ba don neman lahira ba. A qarshe Malam don girman Allah a karanta wannan wasiqa gaba dayan ta ga iyaye a talabijin da rediyo domin su san halin da ya’yansu mata suke ciki a jami’a. Don nasan akwai iri na da yawa kunya da tsoro ne suka sa mu ka yi shiru. Ni kam na gamsar, saura ku malamai ku shaidawa sauran jama’a. Allah ka zama shaida. Malam don Allah ka yi mini Addu’ar Allah ya kare ni daga sharrin fasiqai da shaidanu, kuma Allah yasa mahaifina ya aurar dani da wuri ga wanda nake so. Allah ya saka da alkhairi. AMSA: Wannan shine abinda ya faru, kaga wannan ta wakilci daruruwan ya’yan Musulmai da suke karatu a Jami’a ko a wadansu manyan makarantu na Gwamnati. Shi ne abin da ake ciki. Ko shakka babu iyaye sune abin tambaya na farko ranar tashin Qiyama. Tunda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce “Kullukum ra’in wa kullukum mas’ulun an ra’iyyatihi” (dukkanku ma su kiwo ne, kuma kowanne za a tambayeshi game da kiwon da aka bashi). Ban tsammanin wannan takardar tana buqatar wani dogon ta’aliqi. Abin da nake so ince a nan wurin. Zaku zama shaida (Masu sauraro na cikin Masallaci) akwai kamar shekaru uku ko hudu da suka wuce ‘Muslim Brotherhood Forum’ sun shirya wata Lecture (Lacca) a Masallacin Sheikh Abba Aji wanda muka gabatar ni da Professor Abubakar Musxafa. Na yi wannan maganar na illar lalata yan mata a University, ma’ana tun shekaru hudu ko biyar da suka wuce, kuma a cikin kowanne karatu a shekara in na samu dangantakar Magana sai na shigar, sai dai dambu in ya yi yawa baya jin mai (kamar yadda Hausawa suka ce). To, a nan wurin akwai hanyoyin da za’a warware waxannan matsaloln ko a rage su. Kar matsala don ta yi girma ta gagaremu ta kowanne hanya…. Admin: *Al-Ameen Abdullahi Idris* Allah ya sa iyaye su gane, mu kuma ya kare mu. (Ameen)
Posted on: Sat, 28 Sep 2013 09:44:00 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015