Daga cikin darussan da za mu iya dauka a cikin azumin watan - TopicsExpress



          

Daga cikin darussan da za mu iya dauka a cikin azumin watan Ramadan akwai cewa: 1.Ramadan watan hakuri ne: Assabru, wanda ke nufin hakuri da Hausa, shi ne kamewa. Arragib ya ce: “Hakuri shi ne kamewa a lokacin tsanani.” Kuma ya ce: “Ana kiran azumi da hakuri saboda kasancewarsa kamar nau’insa ne.” (Almufradat, shafi na 474). Dalili Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku nemi taimako da yin hakuri, da Sallah:…” (k:2:45). Ibn Jarir ya ce: “An ce ma’anar hakuri a nan na nufin azumi ne. Domin azumi wata ma’ana ce daga cikin ma’anonin hakuri a wurinmu.” (Tafsirin dabari, Mujalladi na 1 shafi na 259). Ramadan da hakuri: An karbko daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Watan hakuri da kwanaki uku a kowane wata azumin shekara ne.” Nisa’i ya ruwaito. Suyudi ya ce: “Watan hakuri shi ne watan Ramadan. Asalin hakuri kamewa ne, sai aka kira azumi da hakuri saboda abin da ke cikinsa na kame rai daga ci da sha da aure. (jima’i) . (Sarhin Sunnani Nisa’i). Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce ga wanda ya zo yana neman ya rika azumi kullum cewa: “Ka azumci watan hakuri da akalla rana daya a kowane wata….” Abu Dawuda da Ibn Majah suka ruwaito. Ramadan makarantar koyon hakuri ne: Don haka Ramadan makarantar koyon hakuri ne kamar yadda Ibn Rajab Alhambaliyyu ya ce: “Mafi falalar nau’o’in hakuri shi ne azumi. Domin ya tara hakuri kan abubuwa uku; shi hakuri ne wajen yin da’a ga Allah Madaukaki da hakuri wajen barin sabkon Allah. Saboda bawa yakan bar sha’awoyinsa saboda Allah alhali ransa yana jayayya da shi kan haka. Don haka ne Hadisi ingantacce ya zo cewa lallai Allah Madaukaki Yana cewa: “Kowane aiki na dan Adam nasa ne ban da azumi. Shi kan nawa ne, Ni zan saka a kai. Domin ya bar sha’awarsa da abincinsa da abin shansa saboda Ni.” Buhari da Muslim suka ruwaito. Kuma a cikinsa har wa yau akwai hakuri kan kaddara mai wahala da za su iya shafar mai azumi na daga yunwa da kishin ruwa. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana kiran watan azumi watan hakuri. (Jami’ul Ulumi wal Hikami, Mujalladi na 1 shafi na 26). Nau’o’in hakuri: Ibn kayyim ya ce: “Hakuri bisa lura da abin da yake da alaka da shi ya kasu kashi uku: hakuri a kan bin umarce- umarcen Allah da ayyukan da’a har sai an aikata su. Da hakuri daga abubuwan da aka hana da sabko har a tabbatar ba a auka musu ba. Da hakuri kan kaddarori da abin da aka hukunta wa mutum har ya zamo bai fusata Allah a kansu ba.” (Mudarijus Salikina, Mujalladi na 2 shafi na 165).
Posted on: Sat, 13 Jul 2013 06:02:58 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015