Daya daga cikin tambayoyin da Jaridar Leadership tayiwa Jagorar - TopicsExpress



          

Daya daga cikin tambayoyin da Jaridar Leadership tayiwa Jagorar Kungiyar Izala game da Taron Hadin Kan Ahlussunah wanda ake yin shi a jahar Lagos. Akwai wadanda suke yi wa wannan taron naku fassarar gangamin siyasa. A na muku kallon magoya baya Shugaba Jonathan ne, kun fito da karfinku, domin ku share masa fagen yakin neman zabe a siyasar 2015, me Malam zai ce kan hakan? To, mu dai ba mu da wata alaka da shi shugaban kasa a siyasance. Ba mu taba zama muka tattauna da shi ba, duk babu wannan. Sai dai kawai mun gayyace shi ne a matsayin shugaban Nijeriya kasancewar a Nijeriya za a yi taron. Kuma wane ne shugaban Nijeriya na yanzu? Idan akwai wani shugaban Nijeriya mai ci da ba shi ba, to wannan din muka gayyata. Ba Goodluck Jonathan (tsuransa) muka gayyata ba, Shugaban Nijeriya ne dake rike da ragamar shugabanci. Bakinmu za su shigo, idan shugaban ya ce ba za a yi taron ba, ta zauna ba zai yiwu ba. Saboda haka duk wanda ya ke kan kujera shi ne muke gayyata don ya dace da lokacin da za a yi taron. Idan da ba shi ne shugaban Nijeriya ba, ba mu da wata alaka da shi. Idan muddin shi ne shugaban Nijeriya kuma ina da alaka da shi kai ma (mai tambaya) kana da alaka da shi, haka nan kowa ma. Har ila yau, hakki ne na shugaban Nijeriya ya kare wa Musulmi da wanda ba Musulmi ba hakkokinsu da tabbatar da zaman lafiya. Ka ga kuma wannan taron ya shafi zaman lafiya. Idan zan gayyato baki daga waje su shigo, sai Nijeriya ta ce ba za su shigo ba, a matsayina na shugaban Izala ba zan iya fada ba in ce dole sai an bar su sun shigo. Ashe kenan ina da bukatar shugaban Nijeriya a matsayinsa na shugaba domin ya ba ni hakkina na shugabanci da yake wuyansa. Saboda haka ni shugaban Nijeriya na gayyata, idan kuma ba shi ne shugaban Nijeriya ba a kawo mun wani. Ko Malam zai yi mana karin bayani, shin taron nan na Afirka ne kadai ko an gayyato malaman duniya? Taro ne na al’ummar Musulmin Nijeriya tare da sauran ‘yan’uwansu na kasahen Yammacin Afirka kuma mun gayyaci ofisoshin jakadanci masu alaka da addinin Musulunci saboda haka taro ne na al’ummar Musulmi. Yanzu misali, idan al’ummar musulmi na Kamaru suka kira taro, wane ne shugabansu? Wanda ya ke shi ne shugaban kasansu dole ne ya je walau Musulmi ne ko ba Musulmi ba. Haka nan a Togo. Lokacin da za mu je taron Nijar, shugaban kasan ya ce a bude kan iyaka domin wanda ya ke kan kujerar Musulmi ne. Saboa haka, ko Musulmi ne ko ba Musulmi ba shugaba yana da hakki kuma dole ka ba shi. A matsayinmu na jagororin Musulmi ba mu jahilci hakkin kasa ba, ba mu jahilci duk abin da aka shimfida na ka’ida ba. Don haka, duk mai cewa taron na siyasa ne to wannan lissafinsa ne kawai. Taronmu na al’ummar Musulmi ne, kuma ba shi ne na farko ba akwai wanda muka yi na programme dinmu ‘family in difficult circumstances support scheme 2011’ a nan National Moskue. Mun gayyaci kowa da kowa a Nijeriya, mun gayyaci shugaban kasa shi kuma ya aiko mana da mataimakinsa a matsayin wakili. Haka nan ma watakila zai faru a wannan karon, ko shugaban kasa ya turo mana mataimakinsa ko wani minister, mu dai Nijeriya muka gayyata.
Posted on: Sat, 15 Feb 2014 06:16:27 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015