(Dr1) TARIHIN ILMINBOKO A NAJERIYA TA AREWA Assalamu alaykum mai - TopicsExpress



          

(Dr1) TARIHIN ILMINBOKO A NAJERIYA TA AREWA Assalamu alaykum mai karatu, yau kuma dai na kara dauko Kano ba gammo, na kara dauko al’amari mai nauyi wanda ya fi karfina, amma in fatar ba za ka kira ni kiyashi mai daukar abin da ya fi karfinsa ba. Hakika na yi wannan karambani ne don masanan sun noke sun ki sauke nauyin da Allah ya aza masu, sun bar mu, mu ‘yan dagaji mu yi ta dumuiniya wai shiga turakar kuturwa in ji Hausawa. Wannan jagwalgwalon da zan rubuta kamar na kullum ne, ina matukar bukatar gyara da kuma suka mai ma’ana ga dukkan ma’abucin hankali ko ilmi da zai kara mani zamma ko kuma sanya ni bisa Siratal mustaqima. Kuma ina rokon Allah ya kare ni daga sharrin magabta da wadanda rabonsu kadan ne ga hankali da ilmi ma’abuta tsukakken tunani. SHIMFIDA Tun kafin Turawan Ingila su kafa wata kasa wai ita Najeriya, al’ummomin da suke wannan yanki musammanmusulmi suna da ilmi na addinin musulunci wanda suka samu tun kafin jihadin Mujaddi Shehu Usman Dan fodio. Tun kafin haihuwar Mujaddadi musulunci ya riga ya shigo nan arewacin Nejeriya ta hanyar kasuwanci da mutanen kasashen Afrika ta arewa watau wanda ake kira ‘The Trans Saharan Trade’ a turance. Wadannan Larabawa sun kawo musulunci kuma ya samu gindin zama har an yi sarakunan da suka mayar da Shari’ar musulunci ta zama tsarin rayuwar daulolinsu kamar Askiya Mohammed Turi wanda daularsa ta kawo har cikin jihar Kebbin yanzu ina ma jin har ta shigo jihar Sakkwato ta yanzu. Ana ciki wannan zama ne sai kuma abubuwa suka cakude aka yi ta gama al’adu da addini gami da zaluncin Sarakunan gargajiya ya sanya Shehu ya fara samun matsala da sarakunan. Daga karshe dai har ya yi hijira da mabiyansa daga Degel zuwa Gudu. Duk da hijirar da ya yi bai tsira ba, Sarki Yunfa ya bi shi aka gwabza yaki wanda Allah ya ba Shehu Dan Fodiyo nasara. Daganan kuma aka ci gaba da wannan jihadi har aka samu nasara akan Yunfa da kasar Gobir baki daya. Bayan cin nasarar Shehu Dan Fodiyo ne kuma almajiransa da ke wasu yankunan da suke yanzu ko dai cikin Najeriya ko kasar Kamaru su ka taho Sakkwato suka amshi tuta suka fara jihadi a wurarensu. Kafin a jima sai ga daular Usmaniyya ta tashi mai cibiya a Sakkwato.Wannan daula ta yi tsawon shekara dari, amma abubuwa suka fara sakwarkwacewadon shugabanni sun fara barin karantarwar Shehu sun fara komawa bin son ransu. ZUWAN TURAWA AREWACIN NAJERIYA Ana cikin wannan ne Turawa suka fara zowa arewacin Najeriya, amma kada mai karatu ya dauka sune na farko. Bature na farko mai suna Clapperton wanda kabarinsa na nan a Sakkwato ya zo ne tun lokacin Sarkin musulmi Muhammadu Bello da shigar burtu kamar Balarabe amma Muhammadu Bello ya dago shi. Anan ya mutu aka kuma rufe shi. A lokacin ya zo ne don binciken kogin kwara. Bayansa wadannan da ni ke magana suka zo sun zo ne da niyyar kasuwanci kamar yadda suka yi bayani, har suka zowa da Sarkin Musulmi na wancan lokacin da tsaraba suka kuma roki iznin yin kasuwanci a cikin kasarsa. Sarki musulmi ya yi murna da su, ya kuma ba su iznin yin kamfani a lokoja wanda ake kiraRoyal Niger Company da turanci. A nan suka rika yin sabulu da Greecemaganin fasho da sauran kayayyaki, suna shiga cikin kasa suna sayarwa. Ashe ba a sani ba, ba kasuwancin kawai ya kawo su ba akwai tsiyar da suke shukawa. Nan suka shiga koyar da leburorinsu yadda za su samo masu bayanin halin da kasa ke ciki suna kuma koya masu fada da makamai.Kafin tafiya ta yi nisa sarkin musulmi Attahiru na farko ya gane inda suka sa gaba ya yi kokarin hanawa amma abin ya faskara. Daga karshe abin ya koma yaki daganan suka tumbuke wannan daula ta Usmaniyya. Bayan da suka rushe daular Usmaniyya ne kuma suka kawo na su tsari, suka hana wasu sashe na shari’a amma sun bar rabon gado da dokokin aure da saki da wasu kananan abubuwan na game da zamantakewa, amma fa duk shari’ar haddi suka soke ta. Bayan wannan in an yi wa mutum shari’ar musulunci ya ji bai yarda da ita ba, sun ba shi ikon daukaka kara don a sake shari’ar a tsari irin na su. Wannan shi ne appeal da turanci. A fannin tattalin arziki kuma suka rusa tsarin zakka da jizya su ka maye su da haraji wanda ya hau kan kowa musulmi da wanda ba musulmi ba. TURAWAN MISHAN Bayan da mulkin Turawa ya kafu shine kuma ‘yan mishan suka fara zowa don samun mabiya addinin kirista. Wadannan ‘yan mishan su su ka sanya kakanninmu suka fara kyamarkaratun boko tun farkon zuwansa. Don makarantar da mishan suka bude ba su karantar da kome illa yadda mutum zai karanta Baibul, saboda haka makarantar ta zama wurin da Arne ko Bamaguje zai shiga ya fito a matsayin kirista, don kafin ka iya karatun sun cusa maka ra’ayiun kiristanci kuma har ya yi tasiri a zuciyarka. Wannan dalili ne ya sa kakaninmu suka ki yarda da shigar da iyayenmu wadannan makarantu, saboda haka sai mishan suka maida hankalinsu a wuraren da arna suke fi yawa kamar yankin Filato da sashen Borno da Adamawa da Bauchi da Binuwai. Dama can kudu duk wannan ilmi ya riga ya samu karbuwa musamman a Abeokuta da yankin Calabar. Da ace ba su zo da wannan manufa ba, da hakika yanzu ‘yan kudancin Najeriya ba su fi mu ilmin boko ba. Dama Kalmar boko a Hausa ana nufin duk abin da ya ke dankare da coge ko kuma yaudara. Daga baya kuma suka so su canja, amma an riga an fara dunki da mugun zare, mutanenmu suka ki yarda. Bayan karatun bokon kuma Turawa suka shiga bata al’adunmu suna cewa kauyanci ne da rashin wayewa. Saboda haka aka wanke kwanyar duk wanda ya yi karatun bokon ya zamana ba ya ganin al’adarsa da wani abin da ke da alaka da ita da kima. Babu wani abu mai daraja sai abin da Turawa suka kawo ko kuma dabi’un da suka kawo shine wayewa. Zan iya tunawa da tarihin Sir Abubakar Tafawa Balewa inda ya ke fadar a wani lokacin can baya a Ikko dole duk malamin asibiti ya yi shigar Turawa in har yana son ya yi kima a wurin abokan aikinsa da kuma marasa lafiya. Don a lokacin in mutun ya sanya kayanmu na gargajiya ya tafi ofis ko magani ya rubutawa maras lafiya ba zai sha ba, don yana ganin bai san abin da ya ke yi ba, a nan mai karatu zai gane cewar wannan wanke kwakwalwada kuma abin da mishan suka kawo ba ya da wata alaka da ilmi, sai dai mu ce dibgewar mutanenmu ta sa haka ya faru. KARATUN ‘BOKO’ Shin wannan karatu wanda ake yi a ‘karatun boko’ ina ya samo asali? Turawa ne suka kirkiro shi da kansu suka watsa shi a duniya koko dai ba su ba ne, su ma sun same shi ne a wani wuri? Amsar wannan tambaya na cikin rubutu na da na sanya wa taken “Shin Akwai Maita a Kasar Hausa�. Amma saboda amfanin wadanda ba su samu karanta waccan jarida ba zan kara maimaita kaina. Mai karatu ya sani dukkan wadannan fannonin ilmi wadanda ake kira boko sun samo asali ne daga Kur’ani mai girma har da karatun da ake kira da boko a wannan zamani. Kuma wannan fannonin ilmin na da kuma wasu bayin Allah managarta da musulunci ya yaye. Ka dauka tun daga Chemistry har zuwa Lissafi da Physics da Biology da Geography da Falsafa da ilmin zamantakewar Jama’a mai suna Sociology da Tarihi da sauransu, duk musuilmi sun taka gaggarumar rawa a gina su, in da babu musulunci hakika da wadannan fannoni sun samu wani gabjejen gibi ko kuma ma kila da babu su dungurugum. Idan ka shiga ilmin Falsafa muna da Sheikh El Gazzali wanda ya ciri tuta a zamanin kuma da kowane zamani in dai ilmin Falsafa ne, kuma tarihin ilmin falsafa ba zai taba cika ba matukar ba a ambaci sunan wannan bawan Allah managarci ba. A fannin kimiyya,shi kansa Chemistry ya samo sunan ne daga kamar Kimiyya wadda ta ke larabci ce, bayan shi kuma, musulmi ne suka fara harhada sinadaran da ake amfani da su ga magunguna da kamfanoni a halin yanzu. Musulmai ne suka harhada sinadarin Sulphuric Acid da Alkane da Furan da Aldehyde da Alkanol da Benzene da sauran derivatives na Organic chemistry. A fannin lissafi, musulmi ne suka fara kawo sifiri watau ‘zero’ a cikin lissafi, kafin musulunci babu wannan lamba, musulmi ne suka kawosix trigonometrical functions watau Sine da Cosine da Tangent da Cotangent da Secant da Cosecant da ake amfani da su a lissafin Triangle. A cikin littafin musulunci mai suna ‘The Endless Bliss’ na yadda ake amfani da wadannan function an fitar da lokutan salloli biyar na musulunci. Aljabra wanda Turawa suka canjawa suna zuwa Algebra, musulmi ne suka kawo shi. Ma’anar wannan kalma da larabci shine harhadawa. Allama Mohammad Alkhwarizmi kuma ya harhada Logarithm ya kuma kawo Arithmeticda kuma Zero a cikin lissafi. Wadannan lambobin ma da ake amfani da su a lissafi yanzu musulmi ne suka fara shi kuma har yanzu sunansu Arabic numbers. A fannin magani kuma akwai mutane kamar su Ibn Rushdi wanda Turawa ke kira Averroes da Ibn Sina wanda suke kira Avecenna wanda ya yi littafin da ake kira Kanun wanda Turawa suke kira a halin yanzu da suna The Canon wanda har yanzu masana ilmin magunguna sun tabbatar da cewar maganar da ke cikinsa dahir ce babu tantama. Bayan wannan kuma Salahuddin Ayyubi wanda Turawa ke kiraSaladin mai yin tiyata ne tun wancan zamani. In ma an ce yana daga cikin likitocin da suka fara tiyata a duniya ba gardama. A fannin Geography kuma har wayau musulmai ne suka raba dare da yini suka maida su awa ashirin da hudu, suka kuma mayar da awa minti sittin, shi kuma minti suka mayar da shi sakan sittin, bayan wannan Sheikh Abu Rayhan Al Biruni ne ya gano The Circumference na duniya tun kusan shekaru dubu da suka wuce. A fannin Tarihi, musulunci ya yaye Ibn Batuta wanda ya yi yawo na kusan mil dubu dari da hamsin a bisa motar kare watau kafarsa. Ya kuma kawo bayanai wanda har zuwa da gobe da jibi suke dahir don shi ganau ne ba jiyau ba. Ba ya karya ba ya tsegumi sai ya ji ya ga, ba zai kage ba! Duk mafi yawan wadannan abubuwa sun faru lokacin mulkin Banu Abbas musamman lokacin mulkin Khalifa Harunar Rashida da dansa Mamun. A lokacin babu garin da ya kai birnin Badgada a duk duniya, kamar dai Birnin New York a yau, a lokacin ne Khaliafa Haruna Rashid ya ba Sarkin Rum mai suna Chalmagne agogon da musulmi suka kirkira, a lokacin musulmi ne ke fada aji a duniya kaf. Su ne suka je Turai suka fitar da Turawa cikin kogo suka sanya masu sutura suka koya masu ilmi. Daga baya musulmi suka lalace sai neman matan banza da shan giya har Allah ya sallada su ga kafirai suka yi Crusading na shekara dari da tasa’in da uku suka karkashe musulmi suka koma manyan duniya. Mai doki ya koma kuturi. Akwai ranar da na karanta wani Littafai mai suna ‘Discover the Wonders’ bayan na gama ganin al’ajaban sararin samaniya sai kuma na kranta kur’ani duk a rana daya na kama karatu har na kawo wata aya a cikin ciki suratun An’am wadda ta ce, Famaan yuridul lahu an yahdi yahu yashrah sadarahu lil islami, waman yurid an yudil lahu yaj’al sadrahu dayyiqan harajan ka’annamaa yas’adu fis sama’i…….. (6:125) da yake larabcin bai yi yawa ba sai na duba tafsirin Sheikh Abubakar Mahmoud Gummi na ga fassarar na kara gane fassararsa. Sai ma na ga Shaihi ya ce wannan na daya daga cikin mu’ujizojin kur’ani mai girma. Mai karatu kai ma ka duba ka ga ma’anarta, kuma ka tambayi wani ‘dan boko’ ya ba ka bayaninta a cikin ilmin Geography. Allahu Akbar Kabiran, Allah na gode maka da ka halicce ni musulmi, Allah kuma ka karbi raina ina cikinsa. Mai karatu ka ji, ka kuma hada da wancan hadisi da ya ce, ‘Hikima bataccen kayan mumini ce. duk inda ya ganta ya dauki abinsa’, to ina ga kayan da kai ka yi sakaci ka kyale wani ya dauka? Kuma ina son mai karatu ka sani cewar Bashir Othman Tofa ya wallafa littafai gida Biyu masu suna ‘Kimiyya da Al’ajaban Kurani’ da ‘kimyyar Sararin Samaniya’. Wallahi in ba ka karanta su ba ban yafe maka ba. ILMIN‘BOKO DA SAURAN ADDINAI Wani abin mamaki shine wannan ilmin na ‘boko ba ya da wani hurumi ga sauran addinai in ban da addinin musulunci kuma har da addinin kirista. Lokacin da addinin kiristanci na mulkin dukkan kasashen Turai aka yi wani masanin ilmin ‘boko’ mai suna Galileo Galili. Wannan masani bayan da yayi karatun littafan da musulmi suka rubuta sai ya harhada madubin-duba-rudu (Telescope) wanda ya rika duban taurari har ya gano ilmomi masu yawa amma kuma kash, ilmin ya sabawa karantarwa addinin kirista. Nan da nan shugabannin coci suka yi taron gaggawa inda aka yanke shawara cewa yayi ridda aka kuma nemi tubarsa ammaGalileo ya ce atafan. Wannan ya sa aka kamo shi aka daure shi a tanteni aka kone da ransa. Bayansa kuma wasu sun kara gano abubuwa daga baya. Suma suka sanya kafar wando guda da malaman coci, daganan kuma malaman coci suka ce a hana mutanen irin wannan karatu sai rigima ta tashi. Bayan da aka yi rigimar ne kuma ka fi karfin malaman cocin sai aka yanke shawarar cewar matukar za a ci gaba da bin dokokin addinin kirista to ba za a ci gaba ba. Saboda haka suka watsar da karantarwar addinin suka rungumi kimiyya su ka ci gaba. Daganan suka bullo da wani tsari mai suna Secularism da turanci watau addini daban in kana so ka tafi coci ka yi, in kuma ka fito ka bar addini can sai lokacin da ka koma. Bayan addinin kirista mutanenChina suna da addinin Budhdha da na Tao da na Confusianism, suka yi ta bin wadannan addinai suka ko yi ta wahala da shiga bala’I har zuwa shekarar 1948 akasamu wani shugaban da ya jagorance su, suka yi tawaye aka kafa gwamnati da ba ruwanta da wadannan addinai, kai ba ma ruwanta da addini, suka rungumi wannan ilmi na ‘boko’. Yau ko bakauyen da kauye ya san China don kere-kere. Bayan wannan kuma Japan sun dade cikin addinin Shinto suna wahala ba su kome sai kamun kifi do noman shinkafa. Da suka gaji da zaman banza suka rungumi ‘boko’ yanzu kun ga Japan. Na taba karanta wani littafi da wani Bature ke fadar addini musuluncin gaskiya ne,don shi kadai ne addinin da in mabiyansa suka rike shi da kyau za su daukaka su yi daraja amma in suka yi watsi da shi sai su lalace, Allahu Akbar kabiran mai karatu ka ji shaida daga wanda ba musulmi ba. Ka kuma dubi tun ranar da Kasar Iran suka koma ma addini sun kama yin sama. Suna yin motoci da jiragen sama, suna da fasahar nukuliya. Ga tauraron Dan adam sun jefa bana a sararin samaniya ba tare da taimakon wata kasa ba. Kuma wallahi mai karatu da za ka yi karatun addini ka fahimce shi sosai, sa’annan ka sami littafan Biology ko Geography ka yi ta karatu, in ka kai wani bayani sai ka fadi ka yi sujada ga Allah don za ka san cewa lallai ayoyin Kur’anin nan da ke cewa, ‘Wa kaanal Laha Aliiman Hakiiman gaskiya ne don zaka gani karara. In kuma ka yi gardama ga fili ga mai doki. Wannan dalili ya sa su ke cewar kimiyya da addini sun yi hannun riga. Wannan ko karya ne don sun tafi kafada-da-kafada da na musulunci. kuma duk binciken kimiyya da kaga ya sha bambam da kur’ani ka tabbatar da cewa ilmin su ne bai kai can ba. In Allah ya yi maka tsawon rai kana nan za ka ji wani ya kawo abin ya yi daidai da kur’ani. Don shi ilmin kimiyyaabu ne wanda ke bukatar bincike, babu wata magana ta take tabbatatta tana iya canzawa duk lokacin da aka samu wani binciken da ya canza ta. Misali mutun na iya daukar Dalton Atomic Theory, shi wannan mutun John Dalton shi ne ya fara gano atom wadda zan iya kwatantawa da zarra a Hausa. Kuma ya yi wadannan maganganu: 1. Kowace halitta ta samu ne da wani dan kankanan abubuwa da ba su rabuwa gida biyu da ake kiraatom. 2. Ba a iya kara ko rage atomda suke cikin halitta. 3. Duk sidarin da ka dauka, to atomdinsa kala daya ne ba su da wani banbanci, amma kuma sun banbanta da sauran atom din wasu sinadarai. 4. Duk lokacin da sidarai za su hadu, suka hadu ne da atomwadanda ba su da yawa. Karin Bayani Watau ka dauki kowace halitta za ka iske wasu sinadari ne suka taru suka yi ta. ko dai sinadari guda ko kuma da yawa. To da zaka dauki suinadari guda ka raba shi , rabin kuma ka kara rabawa, in kaci gaba da rabawa za ka kai lokacin da wani balli ba zai rabu ba don ya cika kankanta. Shi wannan abin da baya rabuwa din shi ne Dalton ya kiraatomkuma ya ba su siffofin da na zana guda hudu a sama. Amma bayan wannan mutun ya mutu an gano cewar ashe atomba shi ne mafi kankatar abu ba, shi kansa yana da wasu kananan abubuwa da ake kira electron,Proton da neutron. Kuma an gano cewar ana iya rasa atomko kuma kara shi. Abin nufi anan Dalton yana nufin cewar in da mutun zai fara aiki da atom goma in ya gama zai samu atom goma daidai ba dadi ba kari. Misali da za ka dauki wani guntun itace ka auna nauyinsa sa’annan ka kone shi, to daga karshe in da zaka tara hayakin da tururin da gawayin da tokar zaka samu nauyin yana nan cas ba ragi ba kari. A zamaninsa an yi ittifakin maganarsa gaskiya ce, amma yanzu daga samuwar ilmin nukiliya an gano wannan magana ba gaskiya ba ne. kuma da ya ce dukatomdin sinadari komi nasu daya ne an gano ya yi kuskure akwai Isotope ga wasu sinadarai kamar na Chlorine yana da mai nauyin awo talatin da biyar da kuma mai talatin da bakwai. Maganar karshe kuma an gano akwai complex compound. Mai karatu ba Hausa na iya ba sosai saboda haka ka samu wani ‘dan boko’ isasshe zai yi maka wannan bayani filla-filla yadda za ka gane. Daga wannan da sauran abubuwan za ka iske cewar ilmin kimiyya ba haka ake yinsa shaci-fadi ba, sai an shiga Laboratory an tabbatar da gaskiyar abu kafin a yarda da shi. Saboda haka duk abin da ba a iya gwada shi a Dakin kimiyyawatau laboratory to ba Kimiyya ba ne. EVOLUTION Akwai wani fannin ilmin halitta watau Biology da aka fito da shi don a kore samuwar Allah daga cikin al’umma. Wannan sashen ne ake kiraEvolution. don wadanda suka kirkire shi sun yi da’awar cewar in har gaskiya ne akwai Allah ta yaya ake samun yakukuwa da cuce-cuce da bala’o’I suna ta fada wa al’ummuamma kuma shi Allahn bai hana ba. Suka yi da’awar cewar duk mutumin kirki ba zai bar bala’I ya shiga gidansa ba alhali ko yana da karfin hanawa? Wasu kuma suka ce akwai na’urorin da satellite da aka kakkafawaa sararin samaniya ga kuma jirage kumbo Apollo da taurarin dan adam amma har yanzu ba a samu wandda ya dauko hoton shi ko kuma ya tunkudo shi kasa ba (wa iya zu billahi) bayan wannan sai kawai suka yanke shawarar cewar sam babu Allah. Kuma suka kawo hujjoji da basu gwaduwa a cikin dakin kimiyya,illa dai da sun sha barasarsu ta kai masu geji sai suka kama sambatu. Kadan daga cikin wadannan akwai Mendel da Hugo de Urieda Sigmund Frued da Lamark da sauransu. Mai karatu ya san cewar dirkaniya ce kawai, kuma bari in baka wasu daga cikin wadannan dirkaninoyin don kai ma kada kasuwa ta watse ba ka samu komi ba. Daga cikin wadannan rudaddun akwai wani mai suna Lamark.Shi wannan ya ce wai duk abin da halitta ke bukata in ta cika amfani da shi sai ya girma ya makasura amma in ta bar amfani da shi sai ya bace. Ya kawo misali da rakumin dawa ya ce wai a da can-can-can wuyansa gajere ne kamar na rago ko bunsuru amma saboda yawan mike wuyan shi yasa ya kara tsawo ya kai yadda ya ke yanzu. Ganin wannan magana sai wani ya kama kiwon beraye amma yana datse masu wutsiya har aka yi shekaru amma ba a taba haihuwar beran da ba wutsiya ba. Daganan ya tambayi Lamarkto ta yaya haka ga bera ba ya amfani da wutsiya shekaru da yawa amma abin da ya ce bai faru ba. Daganan ya kama kame-kame. Na biyu a cikin shekarar 1953 wani mahaukacin mai suna Stanley Miller ya ce wai farkon halitta ta faru a cikin ruwa kuma zafi ne ya yi yawa har ya sa wasu sinadaran amino acid da na Nueleitide suka cure sai wata fata ta baibaye su, shi ke nan sai kananan halittu suka fara tashi. Su wadananan kananan halittu ne suka yi ta canzawa har wasu suka zama kifi daga kifi suka koma kwado daganan kuma sai tsuntsaye sai kuma dabbobi masu ba yayansu nono har aka kai ga birai daga cikin birai kuma wasu suka koma Chimpanzee da Gorrilla daganan kuma sai suka koma mutane. Da gama wannan bayani masana suka tambaye shi hujjar da zai tabbatar da haka sai ya samu sinadaran Hydrogen da na Methane da na Ammonia da tururin ruwa ya hade su wuri guda. Dama ya ce sune suka taru suka yi amino acid da Nucleotide din da suka yi halitta da suka ji zafi ya yi yawa. Daya hada sai kuma ya turo zafi daga wani injinin lantarki. A cewarsa za a samu amino acid ashirin daganan ko sai halitta ta tashi. Aka ce ga fili ga mai doki. Da ya hada wuta sai Allah ya ba da amino acid biyar kacal daganan kuma babu abin da ya faru. Shi ke nan ‘malamin’ ya koma gefe guda ya kama kakari. Akwai abubuwa da yawa amma mai son bayani ya samu littafan Biology ko kuma wani littafi mai suna LIFE- HOW DID IT GET HERE? BY EVOLUTION OR BY CREATION. NEMAN ILMIGA MUSULMI Wannan wani abu ne da ya kamaci musulmi mace da namiji, don jahilci ba hujja ba ce ga kotunan duniya ko kuma gobe kiyama. Ba ya yiwuwa ka je lahira gobe kiyamaka ce wa Allah ba ka sani ba. A tarihin duniya ba a taba al’ummar da ta mai da hankali ga neman ilmi ba kamar musulmi kuma kowa ya shaida haka tun daga makiyan musulunci har zuwa masoya. Kuma ya kamata duk wanda zai nemi ilmi ya neme shi don kawar wa kansa jahilci, ba don neman abin duniya ko mukabala ko kuma neman girma da isa ga masu iko ba. Allah ya kawo mu wani lokacin da ilmi ya rasa kimarsa, ana nemansa ne don neman daukakar duniya da kuma samun abin yin gardama da jayayya. Wannan ba ina nufin munazara da mudaraha da muzakara ba wadanda ake kirasymposium da seminar da debate. Duk wadannan hanyoyi ne ke karawa mai neman ilmi daraja ga ilmi amma almajiri ya kiyayi gardama da jayayya. SABANIN RA’AYI Yanzu kuma ina son shiga ciki wani sashen da ni ke son dunkewa da wannan rubutu nawa, watau sabanin ra’ayi. Sabanin ra’ayi da fahimta yana tasowa ne daga banbancin fahimta ko kuma bayyanar zahirin abu da kuma yadda ya zo wa mutun ko al’umma. Ga wani misali. Wata rana ne aka kawo wasu makafi guda uku aka ce masu ga Giwa nan, kowanensu ya taba ta amma za a yi masa tambayoyi daga baya. Da aka jawo makaho na farko sai aka sa shi ya taba hancin ko kuma abin da ake kira hannunta, da ya laluba aka ce ya je ya zauna. Na biyu kuma aka kawo shi sai ya shiga karkashinta ya rungumi cikinta shi ma aka ce ya koma ya zauna, sa’annan aka kira na uku aka kai shi wajen kafar Giwa ya runguma. Bayan wannan aka tambayi makaho na farko ya ya Giwa ta ke, sai ya ce haka take kamarbututu, na biyu ya ce karya ka ke haka ta ke kamar rumfa na uku kuma ya ce duk kun yi karya haka ta ke kamar ice. To wa yayi gaskiya wa kuma ya yi karya a cikincu. Sai da aka yi masu bayani aka kuma kai kowa ya taba sauran wuraren da bai taba ba ya gane ashe yadda ya dauki abin ba haka ya ke ba. SABANIN RA’AYI A MUSULUNCI Wannan sabani ra’ayi an fara samunsa tun zamanin da manzon Allah SAW yana da rai. Don akwai wasu sahabbansa da ya aika wani garin da na mance. Kafin tafiyarsu ya fada masu cewar kada su sake su yi sallar la’asar sai sun isa wannan wurin. Daganan suka kama hanya, ba su kai wurin kuma la’asar ta yi. Wasu suka ce a tsaya a yi sallah amma wasu suka ce ai manzon Allah SAW ya ba mu umurnin cewa kada mu yi sallah sai mun isa garin. Su wadancan suka ce ba umurni ba ne ya fada mana haka ne don mu yi sauri, su kuma wadannan suka ce umurni ne. Daga karshe dai aka samu fahimta biyu, daya suka yi sallarsu, daya kuma suka bari sai da suka shiga garin sa’annan suka yi ta su. Da suka dawo suka tambayi manzon Allah SAW ya ce kowannensu ya yi daidai. Saboda me? Kowa yayi don Allah. Sabanin Ra’ayi ne ya kawo musulunci ya rabu zuwa Sunni da Shia kuma sabanin ra’ayin ne ya sa aka samu mazhabobin Imam Maliki da Shafi’i da Abu Hanifa da ta Hambali a cikin mabiya sunna. Kuma ko cikin mazhabar Mlikiya akwai sabanin ra’ayi tsakanin shi kansa Imam Maliki da almajiransa. Duk mai son wannan ya duba zai fara haduwa da shit un daga Izziya har zuwa Muhtasar. A cikin almajiran ma akwai ra’ayin Suhnunu da Ibn Kasim da Majisuna da sauransu amma kuma sabaninsu alheri ne ga al’umma. Idan mutun ya dubi addini kirista sai ya ga banbancin ra’ayin da ke cikinsa ya fi na musulunci yawa, amma duk da haka sun zauna lami lafiya da junansu. Da farko littafin na su ba daya ba ne, darikar Katolika tana da na ta baibul dabam, su kuma Protestant suna da na su. Akwai littafan da ake kira apocrypha wadanda suke a cikin baibul din Katolika amma na Protestant sun ki yarda da su kuma sun cire su. In kuma ka dawo cikin Protestant ‘yan Jehovah Witness su ma sun cire wasu ayoyi a cikin littafin Markus surah ta sha shidda da wani sashe na Littafin Matta. Bayan wanan ka dubi cocinsu, wasu na kalon gabas wasu arewa wasu yamma wasu kuma kudu kai har da kusurwa, bayan wannan kuma mafi yawan kiristoci na zuwa coci ranar lahadi amma ‘yan Seven Day Sabath sukan yi ta su bautar ranar asabar.Bugu da kari ‘yan Jehovah Witness ba su kida da waka, sukan zauna ne suyi abinsu cikin tsanaki babu kwaranniya amma sauran da kade-kade da raye-raye su ke yin nasu. Kuma har yau dai Jehovah Witness ba su yarda da Trinity ba watau Allah uba, Allah uwa kuma Allah ruhi mai tsarki. Amma duk da wannan abubuwa sun zauna lafiya. Amma kalura mu musulmi kur’aninmu daya ne tun daga Sunni har zuwa Shi’a, bayan wannnan alkiblarmu guda duk duniya, sallar mu biyar kuma lokacin yinsu duk daya ne a dukkanmu, mu yi azumin a watan Ramalan, mu ba da zakka. Kuma duk shekara mu taru a Makka don hajji kuma lokacin daya. Duk wanda bai yi wadannan ba, to ya kafirta kuma dukkan musulmi ya yarda da haka, amma kumamun kasa zama lafiya tsakaninmu mene ne dalili? Akwai wani labari da na taba ji mai ban dariya. Wai wani Inyamiri ne zai musulunci sai ya musulunta a hannun wasu bangare musulmi, da wasu bangaren ma su adawa da wancan bangaren suka ji sai suka fada masa musuluncin bai yi ba, saboda haka suka kira shi a masallacinsu su sake musuluntar da shi. Amm abin mamaki sai suka sake fada masa Kalmar Shahada. Da jin haka sai ya fada ma su cewar ai ko wadancan ma abin da suka ce ya fada ke nan. Tandam. SON RAI DA KWADAYI Babbban abin bakin ciki ne yadda malamai suka maida kansu don neman abin sanyawa a abakin salati. Wannan abu ba bako ba ne, ya dade watau mayar da karatun addini ya zama sana’a. A da can malaman zaure ke ta banna suna ta tsibbace-tsibbace daganan kuma su koma har da amfani da Rauhanai da shaidanun aljannu. Yanzu kuma abin ya koma kungiyoyi kowa ya duntsi na sa jama’ar da zai rika juyawa kamar waina. Mabiyansa na iya yin kome matukar dai shi ya fada masu yin hakanan daidai ne. A cikin haka kuma zai tara mukarrabai da za su rika kambama shi. In kuma ana cikin haka daga cikin mukarraban suka ga bukatarsu ta ki biya sai kuma su kama sharri, kafin ka san abin da ake ciki sun balle sun kafa sabuwar kungiya. Daganan sai kuma gama mabiya fada. Su kuma malaman kasa-kasa sun kakkafa masallatai an sanya ‘yan kwamiti. ‘Yan kwamitin nan su za su fara hada fiina a masallacin har husuma ta tashi. Misali akwai masallacin da na lizimta ina sallah amma sai na’ibi liman da wasu ‘yan kwamiti suka shirya juyin mulki amma kumababu hujja, don babu dalilin fitar da limamin a shari’ance. Saboda haka aka ce sallama uku ya ke yi mai makon biyu. Shi na’ibin ya kawo hadisan da suka ce manzon Allah SAW sallama biyu ya ke yi, shi kuma ya kawo tasa hujjar a littafan Fiqh amma ina. Kafin ka ankara masallaci ya koma filin dambe sai Shago da Dandunawa ke ta kikif. Ni kaina nan sai da na samu wani katon naushi wajen rabon damben. Ana ko ba ni wannan naushi na yiwo waje na barsu suna yi. Ganin wannan na bar zuwa wannan masallaci na koma wani. Shi kuma watan azumi ya kama, sai wasu suka kawo cewar sallar tarawihi za a yi raka’a takwas saboda wani hadisin Nana A’isha. Shi kuma liman ya kawo hadisin Abdullahi bin Abbas watau lokacin da ya kwana wurin goggonsa matar manzon Allah SAW da kuma wasu hujjojinsa a cikin Risala. Amma ina! Kafin aje ko ina sai na ga wani kato na takwaikawaye wando, nan da nan na tashi na koma bakin masallaci don gudun ko-ta-kwana. Kafar farko da katon nan ya kai ni ko na yi waje don ba ni kara yarda da daukar dawainiyar ko yin waigi ga naushin da ya yayi makuwa ko batan kai har sauka a bias bigiren da ba can aka nufa da shi ba. Ka ji yadda na bar wannan masallaci har yau ban sake komawa ba. KIRA GA MABIYA KUNGIYOYI Akwai miyagun malamai da su ke cikin kungiyoyi da kuma darikun sufaye wadanda suka shiga don cimma wata manufa tasu ta dabam. Irin wadannan mutane za ka ga sun fi kowa azarbabi a cikin kungiyar ko darika da son a san da su. Da an ce maka ba su samu yadda suke so ba to fitna ta tashi. Nan da nan za su hada rudami. Ka sani kai mabiyi mai tafiya cikin irin wannan harka in dai don Allah ka ke yi ga wadansu shawarwari da zan baka don kada wani ya kwashe maka kumaji a aikin banza, ka rasa ranka a banza ba ji dadin duniya ba kuma ka je lahira babu dadi. 1. Ka nemi ilmi, don tsoron Allah da gudun duniya ba shi yiwuwa da jahilci. In babu ilmi sai malaman zamani su mayar da kai kamar kwallo. 2. Ka yi amfanin da hankalinka sosai ka fahimci shugabanka, shin makwadaici ne ko kuwa. Yana da amana in harkar kudi ta hada shi da sauran mutane? 3. Shin shugaban yana da sana’ar da ya ke daukar nauyin iyalinsa ko ko da addini ya ke ci yana kuma fadanci ga mahunkunta da masu kudi. 4. Shin yana da hali irin na manzon Allah SAW na daukar abin duniya ba komai ba, kuma yana iya fidda dukiyarsa da kome nasa a kan abin da ya ke kiranka akai, koko dai nauyin abin ku ya ke dorawa shi ko ya yi likimo. 5. Malaminka shi ke karantar da ‘ya’yansa ko ko dai wani ya ya karantar da su? Don akwai mamakiga mutumin da ke kokarin karantar da jama’a amma kuma bay a samun lokacin karantar da iyalinsa. don Allah y ace, Ya ayyuhal lazina amanu, quu amfisikum wa ahliikum naaram wa quudu han nasu wai hijaara….. Abin da yasa na ce haka in ka lura da manzon Allah zaka iske ko da ya zama shugaba a duk duniyar Larabawa amma shi ke dunke rigarsa da takalmansa in sun tsunke, bayan wannan kuma har Manzon Allah ya bar duniya ba a taba hada kwana uku ana abinci a gidansa ba, don babu abin,lokacin wafatinsa ya bar alfadari da takobi da rawani da kuma rigar da take wajen jingina. Shi ke nan. Ko nawa kuma manzon Allah SAW samu rabawa sahabbansa ya ke yi ba boyewa ya ke ba. Shi kuma sayyidina Abubakar mai dukiya ne kafin musulunci, amma da ya musulunta ya dauki dukiyar duk yayi aikin addini da ita. Daga ciki akwai sayen bayin da aka matsawa da tsada kamar su Bilal da Zinnira don su samu sakat, su kuma bautawa Allah ba tsamgwama. Sayyida Umar shi kuma rigarsa da wandonsa guda kuma suna da faci saba’in. Sayyidina Usman shi ma mai arziki ne ka dubi irin hidimar da ya yi ta yi wa musulunci musamman lokacin yakukuwa. Sayyidna Ali da ma shi mai tsanani zuhdu ne, bai tara kome ba sai tsoron Allah. Idan ka koma nan kusa Shehu Usman Danfodio ya yi rayuwa mai sauki kuma bai taba hada riga ko wando ko rawani biyu ba kuma tufka igiya ya ke yi yana sayarwa don ciyar da iyalinsa kamar yadda Annabi Dauda ke yin kira. Don akwai hadisi a cikin Mukhtarul hadisi da ya ce, mafi kyawon abinci shine na annabi Dauda wanda ba ya cin kome sai abin da ya samu da guminsa. Nan kusa kuma ka dubi Sheikh Abubakar Mahmoud Gummi. Kamar yadda wani abokina ya bani labari da kudin royalty din littafan da ya wallafa ya sayi gidan da yake a Kaduna kuma alkalin alkalai ne. Ka kuma dube za ka ganshi kamar wani mayunwaci da gajiya kila don tsabar sallar dare, suturarsa kuwa kamar tatalakka kamar ka. Har ya koma ga Allah ba shi da mota mai tsada. Kuma bai bar komi ba sunan alheri. Saboda haka duk malamin da ya tsaya ba shi sana’ar kome, kuma ka ga yana ta holewa da sharholiya da sunan addini ka kiyaye shi, in ko ba haka ba sai ya kai ka ya baro. Bari in kawo maka wasu abubuwa da suka faru a kasar Guyana da kuma Uganda. A cikin kasar Guyana ta can cikin kudancin Amerika aka yi wani fasto mai suna Jim Jones. Asalinsa mutumin Amerika ne, ya yiwo kaura ya komo Guyana tare da wasu mabiyansa mafi yawancinsu bakar fata. Da zuwa nan kuma ya kara samun wasu suka debi daji su ka yi ta yi masa noma. To amma fa yana da matsala da gwamnatin Amerika don suna tuhumar cewar yana da akidar markisanci. Lokacin da aka sa kungiyar leken asiri Ameriaca ta CIA suka kama nemansa, da ya ga za an kusa kama shi ya samu lemu ya sanya masa guba ya ba mabiyansa su 910 duk suka mutu. Da aka binciki kudin da ya boye a bankunan duniya sai aka iske ya boye dalar Amerika milyan goma sha biyar! Na biyu kuma an yi wata mace a kasar Uganda mai suna Credonia Mwerinde wadda ita ma limamiyace ta cocin Movement for Restoration of Ten Commandment of God. Wannan mace da farko cikin birnin Kampala ta ke tana sayar da giya, amma daga baya ta yi da’awar wai tana haduwa da mahaifiyar Annabi Isah AS a wani kogo. Daganan ko ta samu mabiya suka bar birnin Kampala suka koma wani kauye mai suna Kanungu. Daganan ta fada masu cewar za a yi tashin duniya a shekara ta 2000. Saboda haka duk mabiyan suka koma gida suka saida duk kaddarorinsu suka kawo ma ta kudin. Daganan kuma duk wanda zai shigo cikinta sai ya sayar da kaddararsa ya ba ta kudin. Haka ta tsare su suka yi ta yi ma ta noma har cikin watan Afrilu 2000sauran wata takwas duniya ta tashi a cewarta. A cikin wannan watan ne ta sanya su cikin cocin ta ce su yi ta addu’a ita ko da mataimakantaguda uku suka kewaye cocin da fetur suka banka masa wuta duk mabiyan suka kone kurmus. Har yau ana nemanta shekara tara babu wanda ya san inda ta nufa! Saboda haka kai mabiyi ka bi sannu in ba haka ba kana iya zama saniyar tatsa. KIRA GA IYAYE A wuri na babu masu laifi a cikin al’ummakamar iyaye. Wasu daga cikinmu hakika sunan iyaye ne kawai don sun haifa. Da sun haifa za su bar wa iska ta yi ta kwasa, daganan kuma sai abin da Allah yayi. Iyaye su kula da irin abokan da yayansu su ka yi, ka rika karfafa wa yaranka gwiwa da su rika kawo abokinsu gidanka don ka gani in yayi zabe mai kyau ka kara masa kwarin gwiwa in kuma ya zabi tumun dare ka raba su ko ta halin kaka. Na biyu ka lura da irin makarantar da ka kai yaronka tun daga ta boko har ta Muhammadiyya, ka kuma rika binciken abin da ake koyawa yaranka, in ko ba haka ba za ka yi da-na-sani. Da yawa mu ke yin gaddama da abokaina don irin wannan hali. Ni yarana ba su zuwa ko ina don karatun musulunci da ni mu ke yi, ni kuma in je in samo mana. Kuma ko ba ni nan mahaifiyarsu na iya yi. Haka ya kamata ga duk almajiri ya yi, don a ra’ayina in har zaka samu dammar karantar da mutanen waje ban ga dalilin da zai sa ka rasa samun lokacin da zaka karantar da iyalinka ba. Don su Allah ya fara cewa, do ya ce, ‘Ya ayyuhal lazina amanuu quu amfisikun wa ahliikum naaran waquudu han naasu wal hijaara. Akwai wani baiti a bakandamiya da ya ce, ‘Dansu bai yi karatu gun su ba, sun kasa zaune don kwadayin miya.’ KIRA GA GWAMNATI Ya kamata gare ta da ta zage damtse don kare dukiyoyin da rayukan al’umma don hakki ne Allah ya dora mata, in kuma ba ta yi ba, to su sani Allah zai tambaye su. Irin ko-in-kula da aka nuna a cikin rikicin nan da kuma rashin imanin da ma’aikatan tsaro suka nuna musammam ga wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba ya baci. A sa tsoron Allah a kan komai, kada kuma a raba mutane su zama ‘ya’yan mowa da na Bora a rika yin adalci don Shehu Dan Hodiyo ya ce gwamantin kafirci na iya dorewa amma gwamnatin zalunci bata zuwa ko ina. Allah ya nuna mana gasiya, gaskiya ce ya ba mu ikon binta, ya kuma nuna mana karya, karya ce ya bamu ikon kinta. Allah ya raba mu duk abin da ba shi da fa’ida. Wassalamu alykum,
Posted on: Mon, 05 Aug 2013 16:03:05 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015