Duk wacce ta dauki namiji uba, tabbas zata mutu marainiya. Namiji - TopicsExpress



          

Duk wacce ta dauki namiji uba, tabbas zata mutu marainiya. Namiji ba dan goyo bane 70% daga cikin samari, mayaudara ne aslm bayan tarin gaisuwa gareka prince ina fatan katashi lafiya, inaso kaboye suna na, da kuma sunan garin da nake, sannan kayimin posting din wannan labari. Nidai na kasance yarinya ce budurwa, kyakykyawa, doguwa fara, agaskiya ni kaina idan na kalli mudubi ina kara godewa Allah bisa wannan ni,ima da yayimin ta kyau, agaskiya to bana kula samari, duk saurayin da yazomin da maganar soyayya ni kuma sai nace dashi, yayi hakuri ba yanzuba, wata rana naje ziyara gidan sister dina. A hanyata ta dawowa na hadu da wani saurayi, yayimin magana naki kulashi, kawai nayi tafiyata, ashe ya biyoni a baya, ni kuma bansaniba, yazo yaga gidan da nashiga sannan yakoma, dare yayi da misalin karfe 8:30pm sai aka turo ana kirana, ni kuma abin ya bani mamaki, ni da bani da saurayi, to waye yake kirana, da dai nace bazanjeba, amma akace naje naga waye, da fita ta sai naga wannan saurayin na dazu, muka gaisa, nan dai yafara fadomin abinda ke azuciyar sa, nace to zanyi tunani, abu kamar wasa soyayya ta kullu a tsakaninmu, kuma mai karfi sosai, wadda har bama iya yin awa 3 bamuji muryar junan mu ba, son da nake masa yawuce tunani, saboda duk sanda nazama ni kadai azaune to babu abinda nake inbanda tunani, wata rana yacemin zaije karo karatu india, amma bazaiwuce shekara 2 ba, yana dawowa kawai sai ayi auren mu, lokacin da yazo yimin sallama da kuka muka rabu, bayan shekarun kuwa yadawo, satin sa 2 da dawowa amma baizo gurina ba, idan na kira wayar sa baya dagawa, nidai na shiga tashin hankali, wata rana kwatsam sai naji ance yau ake daurin aurensa dashi da wata kawata, ranar nan har asibiti saida aka kaini, saboda kasa barci nayi ga ciwo iri iri, da nakeji, dan haka ni yanzu bazan sake yarda da wani da namiji ba. Nagode prince. Barkanmu da asuba da fatan kun tashi lafiya. #via admin prince abubakar sadeeq.
Posted on: Tue, 10 Sep 2013 05:37:13 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015