Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. muna godiya gareshi, muna neman - TopicsExpress



          

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. muna godiya gareshi, muna neman taimakonsa, muna neman tsarinsa daga sharrace~sharracen rayuwukanmu da miyagun aiyukanmu. wanda Allah ya shirye shi babu mai batar da shi, wanda kuma ya batar babu mai shiryar dashi. ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , shi kadai, babu abokin tarayya agareshi, kuma ina shaidawa cewa annabi muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne. Allah ya yi tsira agareshi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyakkyawan kwaikwayo har zuwa ranar kiyama, kuma yayi musu aminci, aminci mai yawa. Bayan haka ya yan uwa musulmai nakeso najanyo hankalin dan/yar uwa akan muke dagewa da nacewa wajen ambaton Allah (swt). domin da masu ambaton Allah dayawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanarda musu da gafara da lada maigirma. kuma bai dace ga musulmi ba harshensa ya gushe yana danye daga ambaton Allah ba. saboda haka akeson musulmi yake dagewa a rana irin ta yau Jumma"a da yawaita istigfari, salatin annabi, harma da suratul kahfi. Allah yasa mudace ameen Allah yasa muna daga cikin wadanda zai yanta a wannan watan mai albarka ameen. hppy jumm"at mubaraq@ 2 all ummah.
Posted on: Fri, 26 Jul 2013 11:22:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015