FALALAR ADDUA DA YIN SADAKA: Assalamaalaikum yan-uwa musulmai, - TopicsExpress



          

FALALAR ADDUA DA YIN SADAKA: Assalamaalaikum yan-uwa musulmai, kamar yanda nayi alqawari a wani posting danayi a ranar talatar data wuce 25/03/2014 cewa nanda Jumaa zanyi bayani akan number 14 da 22... Toh Alhamdulillah Allah yakawo mu Jumaa kuma zan cika alqawarina amma zan fara da number 14 wato KA YAWAITA YIN SADAKA SAI ALLAH YA TAIMAKEKA AKAN MAQIYA... Bari inbada abarin wani bawan Allah da wata tsuntsuwa a zamanin Annabi Sulaiman GA LABARINA KAMAR HAKA: A zamanin Annabi Sulaiman anyi wata tsuntsuwa data kai qarar wani bawan Allah wajen Annabi Sulaiman, ita dai wannan tsuntsuwa ga abinda take kokawa akai, tacema Annabi Sulaiman ita dai ta kasance tana yin kwai akan wata bishi a cikin gonar wani mutum, shi kuma mutumin daya fahimci hakan sai yana zuwa yana kwashe mata kwai duk sanda tayi kwan, ita kuma bata son haka shiyasa tazoga Annabi Sulaiman dan ya hana wannan mutum kwashe mata kwai, shiko Annabi Sulaiman dajin haka sai yace aje a kawo wannan mutumi mai gonar, da aka kawoshi sai Annabi Sulaiman ya fada masa abinda tsuntsuwar tace, sai mutumin yace Insha Allahu bazai sakeba, sai Annabi Sulaiman yace su tafi, bayan kwana biyu sai wannan mutumin ya manta yaje ya sake kwashe kwan wannan tsuntsuwa, ai kuwa tsuntsuwa da ganin haka sai kawai ta nufiga Annabi Sulaiman tace ya Annabin Allah wannan mutumfa bai dainaba ya sake kwashe min kwai, sai Annabi Sulaiman yace aje akawoshi, da aka kawoshi sai Annabi Sulaiman yace ya akayi hakan ta sake faruwa sai yace wallahi ya mantane, sai Annabi Sulaiman yace dashi wannan shine na qarshe dazan barka banma komaiba ka tafi karka sake, yace naji kuma nagode, bayan sun wuce sai Annabi Sulaiman yacema wasu Aljanu guda biyu suje suyi gadi akan bishiyar da tsuntsuwar take kwai da sunga mutumin yazo daukar kwan su jefoshi qasa sannan kuma su kawo mai shi, sukace toh suka wuce... Ashe dai shi wannan mutumi yanada wata dabia da Allah ya daura masa wato yawan mantuwa, saide kuma shi wannan mutumi yanada wata dabia daya daurama kanshi wato kullun idan zai fita daga gidanshi sai yayi addua Allah ya kareshi daga daga duk wata sharrin dazata sameshi sannan idan yagama sai yayi SADAKA... Sai rannan aka sake yin rashin saa mutum nan yazo gonarsa sai kuwa ya manta yaje ya sake kwashe kwan tsuntsuwa, itako tsuntsuwa dataga haka bata tsaya ko inaba sai fadan Annabi Sulaiman, da zuwa tace ya Annabin Allah yafa sake kwashe min kwai, shi kuma dajin haka sai ya cika da mamaki yace ina Aljanun danasasu gadin kwanki, sai tace suna wajen, yace aje a kirasu, da sukazo sai yace musu ya akayi kuna wajen har yazo ya kwashe mata kwai kuma tun kafin ya kwashe bakuyi mai abin danace ku aikata akanshiba, sai sukace ya Annabin Allah lallai munga wani babban alamari da wannan mutumi domin kuwa sanda yazo kwashe kwan tare da wasu malaiku yake yawo, sanda mukazo jehoshi qasa kamar yanda ka umarcemu sai waannan malaikun suka hanamu sukace kar mu sake muyi wani abu na cutarwa agareshi, mu kuma da mukaga haka sai muka kyaleshi, sai Annanbi Sulaiman yace aje azo da wannan mutumi, yana zuwa Annabi Sulaiman yace dashi ka fadama mutane da aljanu da duk wata halitta da take nan cikin fadar tawa abinda ka kasance kanayi a kullun ni kuma zan fada muku abinda duk baku saniba... Sai yace na kasance saboda yawan mantuwa da Allah ya daura min bana fita daga gida sai nayi addua neman tsari daga duk wata sharri dake fuskantana sannan kuma inyi sadaka, sai Annabi Sulaiman yace lallai ka rabauta dan kuwa duk wanda ya kasance yana adduar neman tsari kafin yabar gida kuma YA ZAMO MAI YAWAITA YIN SADAKA Allah zai hadashi da malaiku guda biyu su zama masu bashi kariya daga fitarsa har dawowarsa... Sai Annabi Sulaiman yace ya tafi kuma yamai Addua Allah yasa ya daina mantuwa, sai yace ke kuma tsuntsuwa kiyi koyi dashi ki zama maiyin addua kafin kibar mazauninki sai Allah ya tsare miki kwanki daga duk wata sharri... ALHAMDULILLAH! Da fatan zamu kasance masu YAWAITA YIN ADDUOI DA KUMA YIN SADAKA domin samu kariya daga sharrin maqiya... JUMAAT JAMEELA...
Posted on: Fri, 28 Mar 2014 05:48:04 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015