##*** FILM din NAS***## A bisa aladata bana fiya son kallon film - TopicsExpress



          

##*** FILM din NAS***## A bisa aladata bana fiya son kallon film ba cikake ba indai ba series bane, musamman films din Kannywood ko Nollywood Films, dan haka ko a lokacin da film din Tahir I Tahir mai suna NAS ya fito ban nemi shi na saya ba duk da yadda nasha kallon tallansa sau ba iyaka a wasu fina-finan, hauragiya da soki burutsi da maganganu masu maana da marasa tushe da alawadai da Allah ya shirya da garama jiya e yau yasa na soke aladata na nemi films din NAS na saya dan naga kallamai da abubuwan da alumma suke fadi kansa, koda na saya sai da tunanina ya tuna min da lokacin da wasu film irinsu MADUBIN DUBAWA, DAN MARAYA, KISHIN MAZA, QONA GARI d.s.s suka fito amma na qeqashe qasa naqi kalla sai da cikakun su suka fito maana (1,2,3 da 4). Na jima ina kaikawo tunani a zuciyata amma daga bisani sai na tuna da wani post da wani dan uwa yayi a shafin sadarwa na facebook da irin chanje kalaman muhawararru da aka ringa, wanda har wasu suke tsokana kan bance komi ba, a tunaninsu baa taba kawo laifin yan wasa hausa ban kare su ba, amma sun kasa fahimta cewa bana kare mutum ko abu ba tare da ina da hujja a hannun ba, kuma mudin na gano laifi zanyi qoqari na fadi koda bazaa ai amfani ba, amma zan sauke nauyin wannan batun yanzu ba ko a shekarun baya da nake rubutun articles bana shakkah ballantana tsoron fadin gaskia. Na kalli film din NAS 1&2 na dau alkalami da waraqa dan bajewa alumma mai na fahimta dangane da saqon da NAS ke dauke dashi amma sai na lura mudin nace zanyi akan qaya 2 dana kalla banyiwa wanda ya shirya da wanda ya bada umarni da wanda ya tsara labarin adalci ba, dan haka na jira tsumayen fitowar na 3&4, kusan bayan wata 1 zuwa 2 sai naji rade_radin cewa na 3&4 ya hito naje nema amma aka shaida min tukuna dai, hmm saboda qaguwa yasa na bada lambar waya na, aiko a ranar daya fito akai min waya naje amsa. Na kalle shi a nutse na kuma koma baya na kalli na 1 da 2 suma dan haka na tattara abinda iya fahimtata da hangena waje daya, cikin ikon Allah sai a yanzu Allah ya nufa zanyi rubutu akan FILM din, Allah ina roqon yasa kar rudani zuciya ko san rai ya rinjayeni, Allah yasa kuma abinda zan fada ya isa ga waddanda aka rubuta dan su. Sunan Film: NAS 1,2,3&4. Shekara: 2013. Story: Adam A Zango. Screen play: Ibrahim Birnawa. Editor: M-Peg (Sunusi Dan Yaro). Producer: Tahir I Tahir. Director: Sadiq Mafiya baquwar rarara Artist: Kabiru/ Adam A Zango (NAS), Maryam AB (Amatallah), Yakubu Muhd (Mal Hassan) Gambo Sawaba (Habibu), Asmau Ahmad (Zee),Baba Qarami (Baban NAS) Mustapha Nabaraska, Auwal Isah West, d.s.s Film din NAS ya nuna illar baiwa yaro gata daya wuce qima, wanda idon mahaifi kan rufe koda dan nasa yana aikata alfsha da munkarai, haka zalika gatan yana hana mahaifi ya kula da ilimin dansa yadda yake tafiya musamman na boko, na addini kuma bayama laakari dashi kasancewar soyayyar daya dorawa dan nasa, laifinsa ko daya bai qaunar ji ballantan ya yarda! Koda matarsa bata isa ta gayya masa laifin Dansa ba ballantana ta gayamasa ya sanya ya gyara, irin wannan shagwaba ta sanya Kabir Zango yake abinda yaso a makaranta ya taka wanda yaso ya mitsike wanda yaso, in kuma yana son abu labuddah sai abun yaso shi koda abun zai mutu, film din ya nuna NAS naso wata yarinya amma saboda kasancewar gurbatacceb hali gareshi yarinyar taqi shi wanda daga qarshe takai sai dai yai mata fyade ya bi ya kashe saurayin da zata aura da mota akaje har gaban koto amma da yake ubansa BABA QARAMI yana sonsa yai iya qoqarinsa sai da yaron aka wanke shi ta hanyar cewa yana da ciwon hauka. Shagwabashin da akai yasa yana iya aikata komi ya bada kudi dan maganar ta mutu. Shagwaba ya sanya ubansa yakaishi karatu kasashen waje amma maimakon karatun sai ya qara zama tantirin dan duniya, bai dawo ba sai da mahaifinsa ya rasu, ya dawo ya ci gaba da baqar sanaa ta haramun da kuma aikata abinda yaso a lokacin da yaso na fasuqanci da shaye-shaye bisa taimakon Manyan dogaransa MUSTAPHA NABARASKA da AUWAL WEST, duk da haka abokinsa GAMBO SAWABA yan bashi shawara akan yabi duniya a sannu amma ya qiya. ADAM A ZANGO sai da ya zamana kaf garin an tambarashi a matsayin dan iska amma bakin jamaa da roqon da yan uwansa sukai masa kan ya nutsu a banza duk da yayi musu korar kare a gidansa. Kisa, Cuta, fyade, da Zalunci sai qaruwa yake. Ido biyu da yayi da Fuskar MARYAM AB YOLA yasa ya fara tunanin abinda ya aikata lokacin da yana matashi, da kuma irin son da yayi mata, a zatonsa yarinyar daya taba yiwa fyade ne a secondary. School, bayan da yasha mari a qoqarin da yayi na bude mata ido yayen niqabin da yake fuskarta. Maryam AB YOLA (Ammatullah) yarinya ce nutsatsia mai kamala da sanin ya kamata da riqo da addini kamar yadda film din ya nuna, wanda har an sanya mata rana da malamin makarantarsu YAKUBU MUHD (mal hassan). NAS (A Zango) yasa yaransa su kamomai ita don cimma muguwar aqidarsa ta yiwa yan mata fyade amma cikin ikon Allah ya kasa. A taqaice dai bayan ya kulleta yayi yayi yai amfani da ita ya kasa, ya haqura amma soyyayarta ya kasa dannewa, daya fuskanci tana son komawa gida, yai mata alqawari haka amma sai in ta yadda zata so shi, ta yarda ta kuma amince har ta sanya ya sauya halinsa tun daga kan sutura, daraja ran dan adam, da tsabtace sanaarsa da komawa ga hanya madaidaicia, wanda daga qarshe aka daura musu aure dashi duk da AMATALLAH da NAS din basu san cewa MAL HASSAN ya haqura ba sakamakon ROQON da HABIBU yai masa lokacin da NAS ya kwanta rashin lafiya sakamakon korar da AMMATULLAH tai masa da kallamanta na cewa dama ita ba sonsa take ba tayi haka ne dan tserar da budurcin duban yan mata daga lalatarsa da kuma tserar dashi daga muguwar dabiar da ya barta a baya. Abun Lura da Laakari a Film din NAS: A- Sutura: a gaskia anyi amfani da suturu kala , 1- suturar kammala 2- suturar fitsara Ba sai nayi bayani kan suturar kammala ba, zan karkata akallar kan suturar fitsara, anyi amfani da matsatsun kaya, dan kunne, sarka, kona gashi d.s.s, a wannan zamani mutane ake kiwo ba dabba ba, matasa mu suna daukar mode of dress ne yawwanci daga yawanci fina-finai, a kano a duk lokacin da akace ranar sallah ne musamman lokacin hawan Nassarawa zakaga yadda gayu ke shigar hauka da sunan gayu, da ka tambayesu sai kaji sunce mawaqi ko dan film suka kaga yayi shigar suka kwaikwaya, na san anyi wannan shigar ne dan fadakarwa amma in ka nutsu sai kaga kashi 80% na masu kallo koyar shigar zasui ba gudarta ba, kai xai wuya wanda yake yin shigar dan yaga film din ya daina. Saka sarqa, dan kunne da balotelli bata daga cikin shigar shagalallun yayan masu kudi musamman yayan hausawa, duk wanda kaga yana yi zakaga ko dai dan tasha ne ko kuma dan Allah bamu, so a nan na kasa fahimtar inda costume ya gano wannan nauin sutura har aka saka su a cikin film din NAS. Kalamai: anyi amfani da kalmar fitsara da hauka da shirme kai har lafazi mara dadi a ciki, a lokacin da kawun ADAM ZANGO yaje gidansa ya nuna fushinsa sosai kan irin ziyarar bazata da yayi mishi inda har yake fadin ko mutuwa tai mai irin wannan bazatan, bata isa ba komawa zatai Haka akwai inda yake cewa tsakanina da duniya akwai fahimta don haka ba abinda zata nema ya hanata Da kuma inda yake cewa mutuwa bata da farin jini dan haka bazai rungumeta ba Akwai dai irin kalamai da-dama da aka ringa fadi wanda basu da muhalin shair kuma bai kamata a fade su ba, amma bansan inda tunanin mai bada umarni yayi ba da ya hana jarimin chanja kalaman da wasu kalamai wanda ba zasu zamo masu illa ko hatsari ga jarumin ko aluma masu kallo ba. Jinkirta Tuba: bai kamata ace dan adam yana furucin xai jinkirta tuba ba har zuwa wani lokaci, Mallam mai akhdari yana fadin cewa ya haramta ageshi da jinkirta tuba yace har sai Allah ya shiryeshi, ko da yake ya bar wannan kudurin nasa bayan da Ammatullah tai masa waazi. Shaye-Shaye: a zahiri yake matasa ba abinda yake damunsu a wannan zamani irin illar shaye-shaye, gaskiya kam dan film din NAS ya nuna cewa shaye-shaye na daya daga cikin abinda ya qara fandarar da KABIRU/ADAM a zango, to amma abin diba anan shine shi matashi a duk lokacin da yake kallan abu yana qoqarin ganin ya ciri wani abu daga cikinsa ne, lissafo kayan maye da nuna kayen maye a zahiri ana sha kamar su cocaine, barasa shima ya kamata a ringa duba ana kallon bakin gatarin. Fadakarwa: YES film din NAS ya fadakar matuqa ya kuma issa ga inda ake so ya isa musamman masu kallo, dan ya fadakar kan illar baiwa yaya mahaukacin gata da baxaa kula da yadda rayuwarsu take tafia ta hanyar abokanai, ilimi, abincin su da abin shan su, da uwa uba riqo da addinisu, wanda wannan shine duk sillar tambarewar NAS. Ya kamata iyaye suna kulawa da wacca naka, saboda rashin sanin gawar fari, kar ka mutu kabar yaro da dukiyar da zata zaman ma annoba da balaI a kabarinka. A qarshe ina kira da jarimin film din da ya ringa kokarin kare tabargazar kalamai daga harshen sa, dan abun tambayane ranar alqiyama. Allah ya kyauta, Allah yasa mu dace. Ina maraba da duk wani suka ko gyara mai maana. Nagode, Naku: Prince Ahmad Amoeva Aamoeva@gmail 08066038946
Posted on: Mon, 04 Nov 2013 10:06:04 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015