FREEDOM RADIO! Amadadina Ni AIA da daukacin iyalaina dama duk - TopicsExpress



          

FREEDOM RADIO! Amadadina Ni AIA da daukacin iyalaina dama duk wanda yake karkashina kama daga Wayata xuwa yar AKUYATA duk muna taya gwarxuwa kuma jarumar tasha wato Freedom Radio murnar cika shekaru GOMA dafara watsa shirye - shiryensu! Ba wata tasha data kusa ko kama kafarku wajen iya tafiyar da shirye - shirye masu Maana! Freedom Radio sune suka fara wayarwa da DAN AREWA kai domin yasan wanene shi musamman anan KANO da jigawa da wasu sassa na kasar Niger da kuma katsina! Sun bayyana a lokacin da Dan Arewa yake da bukatarsu kuma sunxo da manufa mai kyau ta niyar tallafawa TALAKA badan kawai sutara abin duniya ba! Freedom Radio tayi sanadin tallafawa rayuwar wasu bayin Allahn musamman idan kana sauraron shirinsu na INDA RANKA! Dan hakane ma naxabi NASIR SALIS ZANGO yaxama gwarxon Shekarata duba da yadda yake bibiyar hakkin wadanda aka zalunta walau a wajen yan siyasa ko kuma akasin hakan! Sunsha fama da magauta wadanda sukaso a rufe radion ma gabadaya sbd kawai abin yatsone musu idanu! To dayake abin Allah aka nufa dashi sai Allahn yaxamemusu JAGORA! Tabbas ina Alfahari da Freedom Radio duba da yadda suke bada gudunmawa wajen cigaban malam BAHAUSHE batare da wata KETA ba! Freedom Radio tayiwa malaman Kano gata, tayiwa mawakan Kano gata, tayiwa yan film din kano gata kai tayiwa duk wani jahar kano GATA wlh! Wanda kaji yana kushe freedom to wlh makiyin Gaskiya Ne! Kaxo kafadi raayinka batare da cin xarafin kowa ba, kuma duk wanda yatsinci kansa amatsayin maaikacin freedom to wlh kabashi shekara daya xakaga yaxama Kwararre sbd ba mugunta aran manyan Gidan! Ba hantara, ba cin xarafin maaikatan gidan da sunan wai ana karkashinsune ana neman KUDI! Nakanji dayawa maaikatan gidan suna fadar cewa wlh idan kaga manyan gidan da sauran maaikatan gidan ana xaune ana hira ko cin abinci sai ka kasa tantance shin waye babban ne kuma waye yaron! Xaabaka dama kagwada basirarka batare da wata hantara ba! Kuma sundauki maaikata wadanda ko kusa ko alama basu karanci aikin jarida ba amma ahalin yanxu sunxama kwararru harma sunfi wadanda suka karanta din! To dama haka duniya takeso musamman inda akacigaba, anaso aringa bawa dan adam dama yana gwada baiwar da Allah yayimasa ba lallai sai yaje ya karanci wannan bangarenba! Domin ahalin yanxu muna da wadanda xasu iya gyara kasar nan wlh kuma suna nan batare da sunyi xurfi a karatun xamaninba! Idan kaduba baya kayi karatun ta nutsu xakagane me nake nufi, idan har ka iya tuna tarihin manyan Arewa na gaske to xakaga cewa wani ba gabadaya baitaba shiga Class ba amma dayake yana da kishin Arewan aransa sai da suka fidda Ai a rago! To ahakikanin gaskia Freedom Radio sunxama Uwa maba da Mama, suna da maaikata dayawa wadanda sune suka rainesu kuma ahalin yanxu suna wasu kasashen suna aiki kamar irinsu BBC da Jamus dama sauran tashoshi na nan gida Nigeria! Allah yatayaku riko, kuma yakareku daga sharrin Mahassada! Allah yaqara taimaka muku ya kuma kawar muku da tunanin son xuciyoyinku! AmEEN! ●●●► © Auwalancy4us | AIA ────(♥)████████████(♥) ──────(♥)████████(♥) ────────(♥)████(♥) ─────────(♥)██(♥) ───────────(♥)
Posted on: Mon, 09 Dec 2013 16:14:51 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015