Fateema S. Ahmad AlShugairi - أحمد الشقيريAN UWA KUBANI - TopicsExpress



          

Fateema S. Ahmad AlShugairi - أحمد الشقيريAN UWA KUBANI SHAWARA... Kamar yadda fiyayyen halitta ya sanar damu,cikakken mutum shine wanda ke neman shawara a cikin alamuransa kuma yayi aiki da shawarar...nidai na kasance yar kimanin shekaru 19, shekara daya data wuce kwatsam idanuna sukayi arba da wani bawan Allah a makarantar mu,a lokacin yana bautar qasa... Tashin farko ya tsayamin arai alamar ina son shi,amma ban sake ganinshi ba sai bana,ina zaune a asibitin da nake practical sai akace nazo xamu gaisar da sabon likita...ina shiga idanuna shi suka hanga a xaune cikin office din,nan take tsohon mikin xuciyata ya tashi. Daga ranar kullum sai mun hadu,abokan aikina dalibai duk xasuje su gaishe shi amma ni bana iya xuwa,domin kullum nashiga asibitin xuciyata na duka,a tunanina idan na tunkari inda yake zai gane ina sonsa... Banyi kasa a gwuiwa ba nacigaba da kai kukana wajen ubangijina,nayi istikharar neman xabin Allah amma abin sai qaruwa yake. Kwatsam rannan nayi rashin lafia,sai ga kira ya shigo wayana da baquwar number,ina dauka na shaida muryarsa,nayi mamakin hakan amma saina tabbar da lallai shine... A taqaice dai daga ranar muka saba har ya tona sirrin zuciyarsa. Yana sona,yanason halayena,yana son yanayina amma kash!!! Akwai yarinyar da ya tura iyayensa akace su jira,saidai har yanzu ba bayani. Ya furta kalmar so a gareni domin nasani inada muhimmanci,idan ya samu waccan shikenan idan bai samu ba zai dawo gareni. Don Allah menene mafita agareni? Kubani shawara!
Posted on: Thu, 21 Nov 2013 11:15:36 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015