Google zai soma fassara zuwa Hausa Shafin matambayi baya bata - TopicsExpress



          

Google zai soma fassara zuwa Hausa Shafin matambayi baya bata wato Google na shirin kara wasu harsunan Afrika ciki hadda Hausa, Igbo, Zulu da Swahili cikin jerin harsunan da yake fassarawa a ‘Google Translate’. Wata sanarwa da aka buga a shafin Google na ‘Africa Google+’ ya nuna cewar ana bukatar masu fassara ‘yan sa- kai wadanda za su taimaka wajen fassara zuwa harsunan Afrika. Hakan na nufin cewar wadannan harsunan Afrikan za su shiga cikin jerin harsuna 71 da Google ke fassarawa. Duk wanda ke sha’awar shiga cikin masu yin fassarar ana tura shi zuwa wani shafin inda zai tantance wata fassara a bisa ma’auni don tabbatar da fassarar ta yi ko kuma a’a. Wannan zai kasance labari mai dadi ga ‘yan Afrika musamman mazauna kasashen Turai dake fuskantar matsala wajen fassara zuwa harsunan Afrikar. Daga BBC HAUSA
Posted on: Tue, 17 Sep 2013 23:25:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015