HAKA MATA KEDA DABARA ASHE??? Kirana tayi a waya wai dan - TopicsExpress



          

HAKA MATA KEDA DABARA ASHE??? Kirana tayi a waya wai dan Allah nai sauri nazo na raka gidan antin ta. Jikinah yana tsuma na buga babur dina kirar SUZUKI na murza masa wuta cikin kananan mintuna sai gani a kofar gidansu, na aika yaro nace yaje ya cewa ZAINAB DAN HADEJIA ya iso yana jiranta a waje. Wanka tayi mai kyau tace sai gareni mutafi, Amma dan Allah mubi ta hanyar shagon Alhaji sira Gamawa inda ananne wanda suke baje koli na shekara shekara suke baza kayayyakin sayarwansu. Hakan kuwa akayi, Ashe ita dama so take ta jikamun aiki saida mukaje daidai wajen sai ta kyallaro wani takallmi mai tsada tacemun, Hony pliz kadan tsaya dan Allah naga wani takalmi da nake matukar sonsa amma wallahi na manta jakata a gida ko zaka bani naira dubu biyar na saya??? Salati nayi cikin zuciyata kasancewar wata yayi nisa banda kudi, a takaice naira dari kadai ke aljihuna, Kawai sainayi dabara nace mata, Oh!! Sweetynah yanzu kinga babu banki a kusa, amma ga wannan naira dari en kiyi sauri tunda kachar mashin nawa ta yanke, kitari mashin kije gida ki dauko jakarki da kika manta en sekizo kisayi takalmin. Hmm....Gaskia ba yadda aka so ba domin naji kunya dayawa. Amma yanuwa yaya kuka gani nakyauta danayi haka ko kuwa da na kar6o koda bashine na saya mata?? Domin yanzu kunyar komawa wajenta nake.
Posted on: Tue, 26 Nov 2013 03:39:02 +0000

© 2015