HANNUNKA MAI SANDA !!! Masu iya magana suna cewa Baki shi ke - TopicsExpress



          

HANNUNKA MAI SANDA !!! Masu iya magana suna cewa Baki shi ke yanka wuya. Wannan batu haka yake,saboda kwatankwacin hakan ya faru akan idanuna kwanan baya,akan hanyata ta zuwa Birnin Damaturu,daga Bayamari. Muna ciki mota tare da wasu bayin Allah muna tafiya,kwatsam sai muka doso wurin binciken ababen hawa na garin Dapchi. Kafin mu karaso,sai daya daga cikin fasinjojin mu yayi subul-da-baka yace Direba,don Allah karka baiwa wayancan yayan shegun ko sisin kwabo. Tsinannu,kullum cikin haramun,amma da zarar sun mutu,watsi zaka ga anayi da kayayyakinsu daga bariki ko gidan haya. Ni ko dan uwana ne ya shiga aikin damara,to, ba ni ba shi. Tsakaninmu dasu sai dai fatar Allah-tsine. Dubi wancan sai kace wani tinkiya. Mhn! Ashe yana tsintuwa ne a gindin kaba. Acikin motarmu akwai Birgimar Hankaka. Bai ce da shi komai ba,hakazalika daga cikin sauran fasinjoji babu wanda yace uffan. Mukaci gaba da tafiya,har Allah ya kaimu Damaturu. Isarmu wurin binciken ababen hawa na Sojoji keda wuya,sai Sojannan yace asauke wannan mutumin. Abinda naga anyiwa wannan mutumin,kada Allah ya sake nuna min irinsa. Naga yadda ake hora dan Adam cikin kaskanci ci tozartawa,tsirara. A takaice dai,mun samu labarin rasuwarsa yau,a sanadiyyar raunukan da ya samu. Ina mai hada yan Uwa da Allah da Manzonsa,da mu kiyaye bakunanmu musamman idan muna halin tafiye tafiye,saboda bakasan da wanda kake tare ba. Bayan haka,Allah ya kawomu zamani na rashin tabbas. Nidai,wannan ya yame min babban darasi a rayuwa. Fatana, yazama darasi ga duk wanda ya karanta shi. Wannan yasa ni yin tambihi ga yan Uwa Maza da Mata. Allah ya kiyashemu aikin Da-na-sani !
Posted on: Mon, 21 Oct 2013 10:16:57 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015