HATTARA YAN MATA DA IYAYE SABUWAR HANYAR YAUDARA TA - TopicsExpress



          

HATTARA YAN MATA DA IYAYE SABUWAR HANYAR YAUDARA TA SAMARI... Daga Aminullah Othman Alhaji 1.. yanzu haka Samari sun bulo da wata Hanyar Yaudarar yan mata wannan Hanyar ba wata Hanya bace Illah suna zuwa Neman yarinya kamar da Gaske ayi maganar Aure da komai har su biya Dukiyar Aure da Kuma SADAKI sai asa ranar Aure to suna yin wannan Abin sai su fara Buloma Mace da wasu Halaye na Nuna ma mace cewa yanzu fa Tunda na biya komai har ansa ranar Aure to kamar kin gama zama Malakina ne sai kaga Wasu Samari suna aiki da wannan Damar suna domin cima wata manufa ko wani Buri wajen Yan mata... Yan mata kuna kuskure wallahi karku mance duk macen data Amince da Namiji a waje ko Aurenta yayi Har abada ba zai sake ganin Kimarta ba ko darajarta ba kuma yanzu wannan Halin ya zama ruwan Dare duk sanda Namiji ya samu biyar bukatarsa wajenki a irin wannan Sigar to zai dinga canza maki yana maki wasu Abubuwa wanda daga Karshe zai nemi kuyi Fada barambaram sai kawai ya fito yace shi yama fasa Auren sai an bashi kudinsa cin mutumci kala-kala. Wanda daga karshe sai an bashi kudinsa ke kuma ya tafi yabarki cikin bakin ciki da bacin rai. Da kuma dana sani marar amfani.. Wallahi yan mata da Iyayaen mata kuyi a hankali wannan halin samarin yanzu ya zama Ruwan dare.. Idan kin tsare kanki da mutumci baki son abin duniya kuma kina tsare kimar kanki zaki tsalake sharrin samarin yanzu.. SHAWARA GA IYAYYE ku daina amsar kudin SADAKI samari har sai Ranar Daurin aure saboda tsare darajar kanku data yayanku. Hafsa AA
Posted on: Tue, 10 Sep 2013 06:10:48 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015