Hmmmm Idan suka saci kudin Talakkawa, sai su kai su SWITZERLAND. - TopicsExpress



          

Hmmmm Idan suka saci kudin Talakkawa, sai su kai su SWITZERLAND. Idan za su yi harkokin kasuwancinsu, sai su tafi AMERICA. Idan suna son ginawa da mallakar manyan gidajen alfarma, sai su je LONDON. Idan za su yi sayayyar su ta kayan alatu da alfarma sai su tafi DUBAI. Idan suna son zuwa yawon shakatawa da hutawa, sai su tafi BAHAMAS. Domin kuma karatun yaran su, sai su kai su kasashen TURAI. Idan kuma zasu yi ibada da rokon Ubangijinsu, sai su tafi SAUDIA ko JERUSSALAM. Idan ba su lafiya, GERMANYsuke zuwa. Amma idan sun Mutu, sai a kawo Gawarsu nan NIGERIA a rufe, mu kasar mu dama an yi ta ne don gawarwaki. Su waye wadannan????
Posted on: Sun, 10 Nov 2013 06:32:17 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015