INGANTATTUN HANYOYI 7 NA TARBIYYAR YARA (1) KADDARAWA / - TopicsExpress



          

INGANTATTUN HANYOYI 7 NA TARBIYYAR YARA (1) KADDARAWA / KIMANTAWA - Nuna masa kana alfahari da shi -Yabe shi idan ya yi abin kirki, - Nuna masa kana kaunarsa koda ya yi kuskure (2) TARAIRAYA -Ba shi hankalinka yayin da yake maka magana -Kasance tare da shi yayin da ya firgita -Yi murna da wani mataki da ya taka (3) KOYARWA - A aikace (ta hanyar kalmominka da ayyukanka) - Yi masa mu’amala irin wanda yake so a yi masa - Karfafa masa gwiwa ya ringa gaya maka matsalolinsa (4) FADIN GASKIYA - Idan ba ka san amsa ba, gaya masa ba ka sani ba, - Kasance mutum na farko da zai tunkara yayin da ya rasa wata amsa - Kada ka bazama shi yayin da ya gaya masa wani abu nasa mai tada hankali (5) KARFAFA GWIWA - Yi tarayya da shi a wajen aikata wani abu da yake so (fita unguwa/ dafa wani abu dss) - Yayin da ka ga ya karkata zuwa wani abu karfafe shi - Ka yi tarayya da shi a wajen karanta wani littafi (6) HORO - Gaya masa ka’idojinka masu sauki da kake da su - Idan an karya maka doka, yi masa hukunci ba don daukar fansa ba - Nuna masa ranka ya baci idan ya yi ba daidai ba (7) KADA KA TABA SAREWA - Ka sani cewa babu wata hanya guda daya jal wadda tafi kowacce a tarbiyya - Sanya wa kanka kalubalen nemo hanyoyin da za su taimaka maka - Yi hira da abokai da masana da kwararru a kan tarbiyya
Posted on: Sun, 25 Aug 2013 09:37:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015