JIBWIS MANARA: Tsarin taimakon kai da kai na Jibwis Manara ta bada - TopicsExpress



          

JIBWIS MANARA: Tsarin taimakon kai da kai na Jibwis Manara ta bada Tallafin Kayan Abincin da yakai Mota (Trailer) Goma sha biyu, irin su Shinkafa, Sugar, da Mangyada kamar yadda kuke ganin Hoton Motoci dauke da su Zuwa Jihohin Adamawa, Borno, Gombe, Taraba da Yobe. Tallafin ya game dukkan Jamaar da Musibar ta shafa ba tare da nuna banbancin Aqidah ko fahimtah ba. Kungiyar #Izala karkashin Jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ta shirya wannan tsari na Manara domin taimakawa kai da kai da zarar Bukatar Hakan Ta Taso, Mun san irin yadda Yan uwan mu na jihohin Arewa maso gabas suka fada cikin jarrabawa na tashin hankali, wanda Gwamnati tana iya bakin kokarin ta na Tallafawa yan gudun Hijira, Amma akwai wadanda Wannan tallafi bai kai gare su ba, musamman wadanda baa sansanin gudun hijirar suke ba, Ganin Haka ne Shugaba Bala Lau ya Umurci Shugabannin Jibwis na wadannan yanki da su zakulo irin wadannan mutane domin kungiya ta tallafa musu karkshin tsari na Manara, wanda a halin yanzu Kungiya ta tura da nata gudunmawar zuwa gare su. Wannan Tsari na Manara yana tafiya ne karkashin irin Tallafin da Kuke badawa lokaci zuwa lokaci, tare da karfafawar Bankin Jaiz Bank da kuma Shugabannin Jibwis na Jihohi da kwamitin Manara a dukkan Matakai. Godiya ta musamman ga Bankin jaiz Bank Allah ya karfafa su, sannan muna godiya ga sauran talakawa masu bada gudumawa na sati sati ta hanyan scratch card na manara. Nan gaba kadan zamu kawo muku yadda aka raba wannan tallafi don kara karfafaku wajen chigaba da tallafawa addini. Muna Adduar Allah ya sakawa duk mai taimakon addininsa da Bayin sa da alkhairi, ya taimaki Shugaba Sheikh Bala Lau akan Manufar sa ta alkhairi, ya kare shi da kariyarsa tare da yan majalisar sa. Amin Summa Amin. jibwisnigerian@yahoo jibwisnigerian.org manaraproject
Posted on: Sun, 19 Oct 2014 14:48:25 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015