KAFIN MU FARA JERO SHUBUHOHIN RAFIDHA YAN SHIA A KAN - TopicsExpress



          

KAFIN MU FARA JERO SHUBUHOHIN RAFIDHA YAN SHIA A KAN WANNAR MASALA ZA MU YI SHIMFIDA DA WASU KAIDOJI DA ZA SU SA MUTUM MAI HANKALI DA ADALCI YA FAHIMCI DUK WATA MATSALA DA TA FARU A TSAKANIN SAHABBAI, KO DUK WANI LAIFI DA AKA RUWAITO AKA JINGINA SHI GA SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW). GA QAIDOJIN NAN KAMAR HAKA: 1. SAHABBAI DUKKANSU ADILAI NE, DUK DA CEWA; AKWAI FIFIKO A TSAKANINSU WAJEN FALALA. 2. KASANCEWAR SAHABBAI ADILAI NE, BA YA KORE FARUWAN KUSKURE KO LAIFI DAGA WAJENSU. 3. YIN MAGANA GAME DA WANI SAHABI KAMAR YIN MAGANA NE GAME DA WANINSA A CIKIN SAHABBAI. MISALI; YABON ALIYU (RA) YANA LAZIMTA YABON UMAR (RA), KAMAR YADDA SUKAN UMAR (RA) DA AIBANTA SHI YANA LAZIMTA SUKAN ALIYU (RA) DA AIBANTA SHI DA CI MASA MUTUNCI. SABODA ALIYU (RA) YA WAYI GARI A MATSAYIN WAZIRI MAI BA DA SHAWARA WA UMAR (RA) A LOKACIN KHALIFANCINSA, DON HAKA IN UMAR (RA) KAFIRCI YA AIKATA, TO TA YAYA ALIYU (RA) ZAI ZAMA MAI TAIMAKON KAFIRI, ALHALI SHI YANA MATSAYIN MAASUMI (A ZATON YAN SHIA)??! DON HAKA SUKAN UMAR (RA) AIBANTA ALIYU (RA) NE!! AL- ALAIY (R) YA CE: ﻥﺇ ﺡﺪﻗ ﺎﻤﻠﻛ ﺔﻋﺪﺘﺒﻤﻟﺍ ﻪﺑ ﻲﻓ ﻦﻳﺬﻟﺍ ﺔﺑﺎﺤﺼﻟﺍ ﺍﻮﻄﻘﺳﺃ ﻢﻬﺘﻟﺍﺪﻋ ﻢﻬﻴﻠﻋ ﺭﻮﺼﺘﻳ ﻪﻠﺜﻣ ﻲﻓ ﻦﻳﺬﻟﺍ ﺔﺑﺎﺤﺼﻟﺍ ﻢﻟ ﺍﻮﺣﺪﻘﻳ ﻲﻓ .ﻢﻬﺘﻟﺍﺪﻋ ﻥﺈﻓ ﺍﻮﻟﻭﺄﺗ ﻦﻣ ﻝﺎﻌﻓﺃ ﻰﻠﻋ ﺍﻮﻘﻓﺍﻭ ﻪﺘﻟﺍﺪﻋ ﺍﻮﻨﺴﺣﻭ ﻢﻬﻟ ﺝﺭﺎﺨﻤﻟﺍ ﻲﻓ ﺍﻮﻧﺎﻛ ﻢﻫﺭﻮﻣﺃ ﻦﻴﻠﺑﺎﻘﻣ ﺎﻧﻮﻔﻟﺎﺧ ﻦﻤﻴﻓ ﻪﻠﺜﻤﺑ ﻲﻓ ﻪﺘﻟﺍﺪﻋ DUBA: ﻖﻴﻘﺤﺗ ﻦﻤﻟ ﺔﺒﺗﺮﻟﺍ ﻒﻴﻨﻣ ﻪﻟ ﺖﺒﺛ ﻒﻳﺮﺷ ﺔﺒﺤﺼﻟﺍ ) 85 :ﺹ ) LALLAI DUKKAN ABIN DA YAN BIDIA SUKA SOKI SAHABBAN DA SUKA CIRE MUSU ADALCINSU DA SHI, ZA A IYA TUNANIN IRINSA A GAME DA SAHABBAN DA BA SU YI SUKA A CIKIN ADALCINSU BA. DON HAKA IN SUN YI TAWILIN AIYUKA NA LAIFUKA DA KURAKURAN WADANDA SUKA YARDA DA ADALCIN NASU, SUKA NEMA MUSU KYAKKYAWAN MAFITA A LAMURANSU, TO SAI A FISKANCESU DA IRIN (WANNAN TAWILI DA SUKA YI MA WADANDA SUKE SO A CIKIN SAHABBAN) GA WADANDA SUKA SABA MANA A KAN ADALCINSU (WATO SAI ACE; TO SU MA SAHABBAN DA BA SU YARDA DA ADALCINSU BA, SU MA LAIFUKANSU ABIN TAWILI NE BA ABIN SUKA BA). • WANNAR QAIDA CE SHAIKHUL ISLAMI IBNU TAIMIYYA (R) YA YI AMFANI DA ITA A CIKIN LITTAFINSA MINHAJUS SUNNA, IN DA YA YI RADDI MA SHUBUHOHIN BABBAN MALAMIN SHIA IBNUL MUDAHHAR AL- HILLIY, AMMA SAI SU YAN SHIAN, DA KUMA WASU WADANDA BA SU BA, MASU KARANCIN ILMI A WANNAN FANNI, SUKE ZARGIN SHAIKHUL ISLAMI DA AIBANTA ALIYU (RA), SAM, ALLAH YA TSARI IBNU TAIMIYYA (R) DAGA WANNAN AIKI, IBNU TAIMIYYA (R) YA SAN GIRMAN ALIYU (RA) KUMA YA YI IMANI DA FALALOLINSA, GANIN GIRMAN ALIYU (RA) YANA DAGA CIKIN ABIN DA IBNU TAIMIYYA (R) YAKE YIN ADDINI MA ALLAH DA SHI. 4. TARIHIN SAHABBAI YA KASU KASHI UKU (3): (a) MUHKAMI (BAYYANANNE WANDA YA DACE DA ABIN DA YAKE CIKIN AL- QURANI DA SUNNA NA BAYANIN MATSAYINSU), WANNAN SHI NE ASALI, SHI NE TARIHIN DA YAKE HUKUNTA FALALARSU DA ADALCINSU. SABODA AYOYIN AL- QURANI DA HADISAI MUTAWATIRAI SUN ZO SUNA YABONSU DA BAYANIN FALALARSU, DA YI MUSU ALKAWARIN GAFARA DA GIDAN ALJANNA. (b) TARIHI NA KARYA, WANNAN WAJIBI NE A ZUBA SHI A KWANDON SHARA. (c) MUTASHABIHI, WATO MAI RIKITARWA, WANNAN SHI KUMA WAJIBI NE A MAYAR DA SHI ZUWA GA MUHKAMI (BAYYANANNE DA YAKE BAYYANA FALALARSU DA ADALCINSU), WATO KASHI NA FARKO KENAN. DON HAKA SAI A DAUKE SHI A BISA MAANA MAI KYAU, WANDA BA ZAI KAI GA SUKANSU KO AIBANTASU BA. 5. ANA AUNA TARIHI NE DA SHARIA, BA ITA SHARIAR AKE AUNAWA DA TARIHI BA, DON BA A GINA HUKUNCE – HUKUNCEN SHARIA A KAN LABARUN LITTATAFAN TARIHI, AA, ANA ZARTAR DA HUKUNCE – HUKUNCEN SHARIA NE A KAN ABIN DA YAKE CIKIN LITTATAFAN TARIHI, DON HAKA DUK ABIN DA MUKA SAMU A TARIHI, WANDA YA YI KARO DA ABIN DA YA ZO A CIKIN AL- QURANI DA SUNNA DA HUKUNCE – HUKUNCEN SHARIA, WAJIBI NE MU YI WATSI DA NA TARIHI. SHI YA SA YA ZAMA BA KARAMIN KUSKURE BA NE, DOGARO A KAN RIWAYOYI DA LABARUN TARIHI WAJEN YIN HUKUNCI A KAN MATSALOLIN SAHABBAI. 6. DAUKAKAR MATSAYIN SAHABBAI BA YA NUNA CEWA SU MAASUMAI NE (WADANDA BA SA LAIFI), AA, SU MASU LAIFI NE, AMMA KO SHAKKA BABU LAIFINSU BAI KAI NA SAURAN MUTANE BA, SABODA MASAYIN DA ALLAH YA YI MUSU NA HADUWA DA MANZON ALLAH (SAW), DA KUMA ALKAWARIN GAFARA DA ALJANNA DA ALLAH YA YI MUSU A DALILIN TARAYYARSU DA ANNABI (SAW). 7. ABIN DA AKA RUWAITO NA LAIFUKAN SAHABBAI YA KASU KASHI UKU (3): (a) WANDA BAI INGANTA BA TA HANYAR RUWAYA DA ISNADI. (b) WANDA YA INGANTA, AMMA YANA DA YADDA ZA A DAUKE SHI A BISA KYAKKYAWAN MAANA, TO WANNAN WAJIBI NE A DAUKE SHI A BISA KYAKKYAWAN MAANAR. (c) WANDA YA INGANTA, AMMA BA SHI DA YADDA ZA A DAUKE SHI A BISA KYAKKYAWAN MAANA, TO IRIN WANNAN YA KAMATA A DAUKE SHI A MATSAYIN DA IJTIHADI SUKA AIKATA SHI, KO DA TAWILI. ALHALI DUK WANDA YA YI IJTIHADI SAI YA YI KUSKURE, YANA DA LADA GUDA DAYA, MAI KARBABBEN TAWILI KUWA, ABIN AYI MASA UZURI NE A KAN KUSKURENSA. 8. KURAKURAI DA LAIFUKAN SAHABBAI SUNA KEWAYE DA WASU ABUBUWA GUDA BAKWAI (7), WANDA KOWANNE DAYA DAGA CIKINSU SABABI NE DA ZAI SA ALLAH YA GAFARTA MUSU, YA YAFE MUSU LAIFUKANSU, YA BA SU GIDAN ALJANNA KAI TSAYE BA TARE DA AZABA KO WATA UQUBA BA: (a) TUBA, KOWA YA SAN SAHABBAI SUN FI KOWA SAURIN TUBA, KUMA DUK WANDA YA TUBA, TO KAMAR WANDA TUN ASALI BA SHI DA ZUNUBI NE. (b) ISTIGFARI, WATO NEMAN GAFARA, SAHABBAI MUTANE NE MASU YAWAN ISTIGFARI. (c) MANYAN AIYUKAN ALHERI DA SUKE DA SHI, WADANDA SUKE WANKE MUNANAN AIYUKANSU, MISALI; SUN RIGA SAURAN ALUMMA SHIGA MUSLUNCI, DA HADUWA DA MANZON ALLAH (SAW), DA YIN IMANI DA ALLAH DA MANZONSA (SAW), DA YIN JIHADI, DA BA DA JINANENSU DA DUKIYOYINSU SABODA DA ALLAH DA MANZONSA (SAW) DON ADDININ ALLAH YA DAUKAKA, DA FIFITA ALLAH DA MANZONSA (SAW) DA ADDININSA DA RANAR LAHIRA A KAN IYAYENSU DA YAYANSU DA DANGINSU DA GARURUWANSU DA DUKIYOYINSU DA RAYUWAR DUNIYA, DA TAIMAKON MANZON ALLAH (SAW) DA KAWUKANSU DA DUKIYOYINSU. (d) ADDUAN DA MUSULMAI SUKE YI MUSU A KULLUM, NA NEMAN ALLAH YA YARDA DA SU, WACCE TA KUNSHI ROKON ALLAH YA GAFARTA MUSU YA YI MUSU RAHAMA, YA BA SU GIDAN ALJANNA, YA TSARESU DAGA WUTA. (e) CETON ANNABI (SAW) GARESU A RANAR LAHIRA. (f) ALLAH ZAI GAFARTA MUSU A DALILIN MUSIBA DA BALAI DA YA SAMESU A HALIN RAYUWARSU TA DUNIYA, SABODA BALAIN DA YAKE SAMUN MUMINI KAFFARA CE GARE SHI. (g) ALLAH ZAI GAFARTA MUSU A DALILIN TSANTSAR RAHAMARSA DA TAUSAYINSA DA IHSANINSA DA FALALARSA DA AFUWANSA DA GAFARARSA GA BAYINSA, BA TARE DA SA HANUN WANIN MAHLUKI BA. • DON HAKA, DUKKAN KURAKURE DA LAIFUKAN SAHABBAI, IMMA DUKA WADANNAN ABUBUWA DA MUKA AMBATA YA LULLUBESU, KO KUMA WASU DAGA CIKINSU SUN SAMESU. • DAGA KARSHE ALLAH YA CE: ﻻ ﻱﻮﺘﺴﻳ ﻦﻣ ﻥﻭﺪﻋﺎﻘﻟﺍ ﻲﻟﻭﺃ ﺮﻴﻏ ﻦﻴﻨﻣﺆﻤﻟﺍ ﺭﺮﻀﻟﺍ ﻥﻭﺪﻫﺎﺠﻤﻟﺍﻭ ﻲﻓ ﻪﻠﻟﺍ ﻞﻴﺒﺳ ﻢﻬﻟﺍﻮﻣﺄﺑ ﻞﻀﻓ ﻢﻬﺴﻔﻧﺃﻭ ﻦﻳﺪﻫﺎﺠﻤﻟﺍ ﻪﻠﻟﺍ ﻢﻬﻟﺍﻮﻣﺄﺑ ﻢﻬﺴﻔﻧﺃﻭ ﻰﻠﻋ ﻦﻳﺪﻋﺎﻘﻟﺍ ﺔﺟﺭﺩ ﻼﻛﻭ ﺪﻋﻭ ﻪﻠﻟﺍ ﻰﻨﺴﺤﻟﺍ KUMA DU YA CE: ﻻ ﻱﻮﺘﺴﻳ ﻢﻜﻨﻣ ﻦﻣ ﻖﻔﻧﺃ ﺢﺘﻔﻟﺍ ﻞﺒﻗ ﻦﻣ ﻞﺗﺎﻗﻭ ﻢﻈﻋﺃ ﻚﺌﻟﻭﺃ ﺔﺟﺭﺩ ﻦﻳﺬﻟﺍ ﻦﻣ ﺍﻮﻘﻔﻧﺃ ﻦﻣ ﺪﻌﺑ ﺍﻮﻠﺗﺎﻗﻭ ﻼﻛﻭ ﻪﻠﻟﺍ ﺪﻋﻭ ﻰﻨﺴﺤﻟﺍ WADANNAN AYOYI GUDA BIYU (2) SUNA NUNA CEWA; DUKKAN SAHABBAI YAN ALJANNA NE, SABODA ALLAH YA CE: ﻼﻛﻭ ﻪﻠﻟﺍ ﺪﻋﻭ ﻰﻨﺴﺤﻟﺍ WATO DUKA BANGARORI GUDA BIYU (2); NA WADANDA SUKA FITA JIHADI, DA WADANDA SUKA ZAUNA A GIDA, (A CIKIN AYAR FARKO), DA KUMA WADANDA SUKA CIYAR DA DUKIYOYINSU KUMA SUKA YI YAKI KAFIN FATHU MAKKA, DA KUMA WADANDA SUKA YI BAYAN FATHU MAKKA, (A AYA TA BIYU) DUKA ALLAH YA YI MUSU ALKAWARIN ALJANNA. ALHUSNA MAANARTA ALJANNA. TO, ME KUMA YA SAURA?! YA ALLAH MUNA ROKONKA, DON SONMU GA IYALAN GIDAN MANZONKA (SAW), KADA KA SANYA HASADA DA JIN HAUSHIN SAHABBAN MANZONKA (SAW) A CIKIN ZUKATANMU. MU HADU A KASHI NA GABA.
Posted on: Wed, 12 Feb 2014 05:41:30 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015