KECE BURINA Tun tana karama alokacin bata wuce shekara 11 bah, - TopicsExpress



          

KECE BURINA Tun tana karama alokacin bata wuce shekara 11 bah, nake kula da ita ina faman tarayrayarta. alokacin ni kuma inada Shekara 23 a duniya. ina SS3 ita kuma Kausar tana Jss 2 akullin idan xani skull saina biya ta gidansu na dauketa saman Mashin dina kirar Roba-Roba Zancen. wani lokaci idan naje baa gama shirya mataba amma ahaka xan tsaya har wani lokaci inyi latti a skull,kuma saina kaita har primary dinsu sannan inbata #100 dan ganin yarinyace kada insaba mata da kashin kudi da kuma son kudi tun tana karama. idan kuma aka tashesu hakan xan dawo daga skull koda kuwa inada Lesson lokacin domin in maidota Gida. ahaka harna karasa Secondary skull dita. amma akullin saina kaita makaranta kuma insun tashi naje na daukota. sannan kuma duk ranar jumaa sai inje gidansu insa ay mata wanka in dauketa saman mashin dina muyita xuwa xumunci gidajen yanuwa da kuma wajajen shakatawa. Muje tasha Ice-Cream, insai mata Boga,Shuwarma,Popcorn,Chacolate iri-iri sannan inmaidota gida.Sannu sannu har itama ta saba dani sosai. Har wasu lokutta sai taxo gidanmu ta kwana da sunan taxoman Week-end. hakan yasa abokaina suka rika kirana da Angon Kausar har sunana na asali y bace watau Faruk. ana haka sakamakon Jarabawata ya fito, kuma nayi nasara sosai dan harna samin Admission a egyft vamma kewar barin Kausar ya hana xuciyata ta samu isarshiyar walwalar daxanyi murna sosai. Gashidai Kausar bata mallaki hankalin daxamuyi bankwana irin na masoyaba amma gsky ina matukar jin haushin intai inbarta dan wlhy nakamu da Kauna. washe gari tunda safe wajen misalin karfe 11am natai gidansu kausar kai tsaye nayi sallama nashiga domin daman da hakan nasaba. Mungaisa da iyayenta cikin mutumtawa, sai gata ta fito daga cikin daki tace Yaya Faruk inakwana na kalleta cikin Shaukin so nace lfylau my sister. Amma sainaga kamar yau tafi ko wacce rana yin kyaul, nace dama Hajiya naxo na fada maku nasamu Admission a egyft kuma inajin nanda sati biyu(2) xan tafi, shine naxo na shaida maku. Cikin sauri kausar ta rugo ta hayeman baya cikin siririyar Muryarta tace laaaah !!!! yaya Faruk kasamu damar xuwa jamia kamar yadda ka taba gayaman kana neman intayaka addua, daga kaina kawai nayi tare da cewar kuma kinga Allah y karbi adduarmu ko? tace eh sai tace to yaya Faruk waxai rika kaini makaranta kuma dawa xamu rika xuwa yawo ranar Jumaa munashan Ice-cream....... shiru dataji nayi yasa tasa hannunta ta dagoman kaina, sai kawai taga ina hawaye. cikin sanyin murya tace yaya Faruk miyasaka kuka, nace Kausar banson intai inbarki kuma gashi kema kinsaba dani ko? tace Yaya Faruk ay tare xamutai ko? nace kausar ay hakan baya yuwuwa. amma kiyi hakuri kamar gobene xakiga na dawo kinjiko cikin shagwaba ta kwanta saman jikina itama tana kuka....... ........ wasa- wasa harna kammala karatuna na shekara 5 sanadiyyar ina karantar Civil Engineering. saboda tunda natai bandawo gida Nigeria bah, radda xandawo kau aranar banyi bacci bah,dan murna da kuma dokin dawowa cikin kasata da kuma masoyana da kuma babban gurin ganin Kausar dita. wadda yanxu nasan takai kimanin shekara 17 nasan taxama Budurwa sosai.wadda ni kuma yanxu inada shekara 27 nasan xamu samu damar fahimtar juma sosai da ita. Zaune nake a falon mamarsu Kausar acikin gidansu.bayan dukmun gaisa da kowa da alokacin dagani sai ita babu abinda ke raina illa inmata tuni akan soyayyarmu domin inji ina aka kwana. Lallai Allah y halicci Kyau a jikin Kausar dan yanxu na kara yadda Kausar kyakkyawace ta ajin farko,gsky rayuwar Aurenmu da Kausar xatai matukar dadi.... ........ ......... sai naji ta ta6a Cup din dake hannuna, tace Yaya Faruk mikake tunani haka inata magana amma kayi shiru. murmushi kawai nayi sai wayarta tayi Ringing alamu ana kiranta cikin sauri ta dauka tayi magana kamar ta tsawon minti 1 saita kashe. tace yaya Faruk dan Allah ka tsaya yanxu Abdul xaixo saiku gaisa, cikin sauri na dago kaina nace waye kuma Abdull. Cikin shagwaba tace aikau shine wanda xan Aura !!! Cikim sauri na mike tsaye Cup din dake hannuna ya kubce ya fadi kasa.Hm macce.. Via ecoinss
Posted on: Sat, 27 Dec 2014 09:45:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015