KU YAWAITA TUNAWA DA MAI YANKE JIN DADI Manzon Allah (SAW) - TopicsExpress



          

KU YAWAITA TUNAWA DA MAI YANKE JIN DADI Manzon Allah (SAW) yana cewa KU YAWAITA AMBATON Mai yanke Jin dadi, wato MUTUWA. Yana cewa: Dan Adam ba zai tuna ta ba yana halin Kunci face ta saukaka masa, haka kuma ba zai tuna ta yana cikin Halin yalwa ba face ta taakura masa (Nasai ya ruwaito. Kuma an inganta shi a Saahihah). Sannan, Annabi (SAW) yana cewa: Ka tuna mutuwa a cikin Sallarka (Saahihah). Da wannan Magabata suka ce wajibi ne mu tuna mutuwa kullun akalla sau biyar a Sallar farilla da kuma nafila ma Idan daman haka ya samu. Mutuwa tilas ne, wasu sun tafi, ni da Kai da ke muna hanya. Wane GUZURI muka yi don tafiya? Yaa Allah ka sa mu cika da Imani in AJALINMU ya zo, kuma muyi mutuwar SHAHADAA,... admin: ↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓ ↓↓↓ Bashir Idrees
Posted on: Mon, 02 Dec 2013 06:34:40 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015