Kakakin majalisar wakilan najeriya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya - TopicsExpress



          

Kakakin majalisar wakilan najeriya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyan cewa shi fa yana majalisar wakilan najeriya ne domin yiwa kasa aiki ba don yiwa jama’iyyar PDP ba. Tambuwal ya bayyana hakkanne jiya a karamar hukumar ilewa Ekiti, na jahar Ekitin a najeriya. Aminu ya fadi hakanne yayin da aka yi masa nadin sarauta na ban girma a jahar. Kakakin yace abun mamaki ne wadansu yan jama’iyyar PDP na jahar osun suke cewa wai ya yaba wa aikin da gwamna Abdurauf Aregbesola na jahar osun yayi wa jahrsa. Ya kara da cewa gwamnan jahar Ekiti mista Kayode Fayemi yana kokari kan kawo tsari da kuma ayyukan da zasu kawo wa jahr sa ci gaba. Tambuwal ya gode wa sarkin Oba Ajibade Alabi da irin ban girman da aka yi masa ba tare da tunanin cewa shi dan arewa ne ba. Gwamanan ekiti kuwa ya kwatanta shi ne da shugaba na gari wanda yake jagorantar majalisar da zuciya daya. Gwaman dai ya nemi a cigaba da bawa gwamnatinsa hadin kai domin samun dorewar cigaba a jahar ta ekiti.
Posted on: Mon, 24 Jun 2013 07:17:46 +0000

Trending Topics




© 2015