Kamfanin man fetur na Shell na ba da bayanan karya game da - TopicsExpress



          

Kamfanin man fetur na Shell na ba da bayanan karya game da malalar mai a Nigeria in ji kungiyar Amnesty International da cibiyar kare hakkin muhalli ta CEHRD. Wani rahoto da ka wallafa a yau ya bankado lokuta da dama da Shell ya ba da bayanan karya game da sababin malalar mai, adadin man da ya malala da kuma aikin da aka yi na tsaftace muhallin. Rahoton ya ce tsarin da ake bi wurin gano dalili da yawan malalar mai a Nigeria na da matukar rauni. Tasirin hakan kan alumomin da abin yake shafa shi ne karanci ko ma rashin diyya dungurungum. Kungiyoyin Amnesty International da CEHRD sun bukaci wani kwararren mai binciken malalar mai da ke zaman kansa a Amurka ya yi nazarin rahotannin da kamfanonin man fetur a yankin Niger Delta da kuma gwamnatin Nigeria ke fitarwa game da malalar mai a yankin.
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 04:14:38 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015