Ko tafiya kake yakamata ka tsaya domin karanta wannan *BABBAR - TopicsExpress



          

Ko tafiya kake yakamata ka tsaya domin karanta wannan *BABBAR FITINA A RAYUWAR MATASA MAZA DA MATA ITACE SHAAWA. ================= A wannan zamanin wani muhimmin abu daya addabi mutane sosai, musamman matasa maza da mata shine SHAAWA, kusan kullum matasa na fadawa cikin bala’in fasikanci kala-kala a dalilin rashin sanin hanyar kaucewa haka. Idan mutum yayi duba na tsanaki tareda la’akari da yanayinmu da kuma yanayin zamani zaiga cewar dayawa wasu na fadawa cikin aikata fasiqanci ba cikin son ransuba, sai don abin ya fi karfinsu. Sauda yawa zakaga matashi mai hankali mai tarbiyya mai tsoron ALLAH, yasan illar zina, yasan girman zunubin ta, amma saboda fitinar sha’awa yakasa daurewa yaje ya aikata din. Wani haka zaita aikatawa yana tuba, da haka har zina tazame masa jiki ya runka ganin ai yinta ba komai bane. SubhanAllah! Haka zakaga yarinya kamila mai tarbiyya mai hankali, tasan illar zina, tasan girman zunubinta amma sai fitinar sha’awa tasa ta afka cikin wannan balai. Domin kaucewa fadawa makaranatar shaidan dolene duk wani matashi dayake fuskantar barazanar Shaawa ya yi laakari da wasu dokoki da addini ya sharanta masa, sannan kuma yayi amfani da dabaru wanda zasu taimaka masa. Mu sani cewa fitinar sha’awa halittace kuma a zuciya take, daga cikinta take bijirowa, don haka maison ya iya danne fitinar sha’awarsa duk lokacin da ta taso masa, sai yafara da gyara zuciyarsa tukunna. Toya ake gyara zuciyar ??? Ana gyara tane ta hanyar cikata da kyawawan tunani da shau’uka, da yanke duk wata igiyar mummunan tunani daga cikin ta, da goge mazaunin duk wani mummunan shauqi. Daga nan sai kyautata dabi’u halaye da ayyuka, duk wata dabi’a, wani hali ko wani aiki da mutum keyi indai bamai kyau bane, to yin watsi dashi zai kara haskaka masa zuciyarsa. kyawawan dabi’u sun hada da yawan murmushi, taimakawa ‘yan uwa, makwabta da abokai, gaskiya da rikon amana, da sauransu. kyawawan ayyuka suhada da taka tsan- tsan wajen tsaida addini, duk abinda akansa ba dai-dai bane a addinance sai ayi kokari a barshi komai dadinsa ko ribarsa. Yawan sanya ALLAH a zuciya da yin zikiri. ALLAH madaukakin sarki, Yafada cikin Alqur’ani mai girma cewa: “Lallai da ambaton ALLAH ne zukata kan sami natsuwa.” Shedan baya iya zama cikin zuciyar dake ambaton ALLAH balle harya gudana cikin hanyoyin jinin ta, to tayaya kuwa harzai tafarfasar da fitinar sha’awar wannan zuciya ??? Kiyaye ibada yana daga cikin maganin da yakewa mutum kandagarki daga fitinar sha’awa. Lallai ne yan uwa mu kula da kiyaye sallolin farilla da nafila da yawaita karatun al-qurani da sauran azkar dasuka tabbata daga manzon ALLAH sallalahu Alaiihi Wasallam. Sannan dole mu kiyaye maganar Manzon ALLAH (s.a.w) inda yake cewa yaku matasa duk wanda yake da hali ko iko toya gaggauta yin aure, wanda kuma bashida halin yin aure to yayi azumi domin wannan yana dakushe kaifin fitinar sha’awa. Sannan dole su kansu Iyaye su kula da rayuwar ya yansu matasa maza da mata, domin karesu daga wannan balai. Wani matashi ya taba tambayar wani malami cewa shi wallahi yana Azumi yana karatun Al- qurani Amma wallahi Shaawarsa kullum karuwa take yi, malam yabashi amsa da cewa to lallai yadage yayi aure. Kusan babban dalilin da yakan hana matasa aure shine rashin tsayayya ko kwakwkwarar sanaar da mutum zai iya rike kansa da kuma Iyalinsa, wannan kam babban alamari ne, domin babu yadda zaaji dadinaure idan babu wata hanya da mutum zai iya daukar dawainiyar iyalinsa, dan haka dole a dage a koyi sanaa domin a dogara dakai. Ya ALLAH ka baiwa dumbin matasanmu dama da ikon yin aure albarkacin Muhammadu Rasulullah (s.a.w). Admin Sudais Adm Zango
Posted on: Mon, 25 Nov 2013 12:57:39 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015