LABARI: Jonathan Ya Kafa Kwamitin Binciken Badakalar Ministar - TopicsExpress



          

LABARI: Jonathan Ya Kafa Kwamitin Binciken Badakalar Ministar Harkokin Jiragen Sama. Shugaban Goodluck Jonathan a jiya ya kafa kwamiti don binciken badakalar ministar harkokin jiragen sama ta kasa, Stella Oduah, kan sayen motocin hawa guda biyu kirar BMW kan naira miliyan 225. Kwamitin mai mutane uku Isa Bello Saleh ne zai jagorance shi, yayin da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Sambo Dasuki zai zama sakatarensa. Babban aikin kwamitin shi ne zai bincike shin ma an sayi motocin da ake da kumfar baki a kansu ko kuwa duk shaci fadi ne. Sannan kwamitin ana sa ran zai bada rahotonsa cikin sati biyu. A wani bangaren kuma ministar a jiya ta bi bayan shugaba Jonathan din zuwa kasar Isra’ila inda ya tafi sauke farali da ziyarar aiki. Wata majiya ta bayyana wa Jaridar # RARIYAcewa Oduah ta bi bayan shugaban ne don ta samu damar yi masa jawabi yadda zai fahimta kan badakalar, wanda aka ce tun da abin ya faru ta kasa samun ganinsa anan gida Nijeriya. Daga Shafin Jaridar Rariya.
Posted on: Thu, 24 Oct 2013 08:19:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015