LABARI MAI TSUMA ZUCIYA Wata rana wani mutum mai - TopicsExpress



          

LABARI MAI TSUMA ZUCIYA Wata rana wani mutum mai shekara tamanin yana zaune a gidanshi shi da yaronsa mai kimamin shekara arbain da biyar. Suna zaune sai suka ga wani bakin tsuntsu ya sauka a windon su, to kasan wani lokaci tsoho kamar yaro yake.... Sai ya bude baki ya tambayi dan yace menene wannan sai yaron yacetsuntsu ne, jim kadan sai tsohon ya sake tambayarsa a karo na biyu, menene wannan?, sai yaron yace, ba yanzu na fada maka ba? Tsuntsu ne! Sai tsohon ya sake tambayarsa a karo na uku, menene wannan? Sai haushi ya kama yaron sai yace ka tambaye ni na fada maka tsuntsu ne! Haba!.... Jim kadan kuma sai tsohon ya sake tambayarsa a karo na hudu, menenewannan? Sai yaron ya daka masa tsawa yace haba baba wai kai wanne iri ne? Kwakwalwarka bata rike abubuwa ne? Ka kama tambayata abu daya har sau hudu!!! Tunda tsohon yaga haka sai ya tashi ya dauko wani littafi ya mikawa yaron yace karanta wannan tsohon yaci gaba da cewa lokacin da kake yaro karami muna zaune ni dakai irin wannan tsuntsun ya sauka a window, kana ta tambayata menene wannan har sau 23 kuma duk sanda ka tambayeni ina baka amsa. Tun lokacin na dauko littafi na rubuta nace nima sai na gwadaka idan kayi girma... Bayan yaron ya gama karantawa nan take sai yaron ya fashe da kuka ya rungume mahaifinsa yana nemangafara. To ku duba ku gani fa shi har sau 23 ya tambayeshi kuma ya bashi amsa bai gajiya ba, amma shi kuwa yanzu sau hudu kawai tsohon ya tambayeshi amma har yayi fushi. MU SANI CEWA......... * Ya zama wajibi muji kan iyayenmukamar yadda suke jin kanmu. * Muyi biyayya agaresu gami da tausayawa, domin suma sun tausayamana lokacin da muke da rauni. * Kada muyi fushi da iyayenmu ko yimusu tsawa, hakan ba dai dai bane. * Nuna so da kauna ga iyayenka domin sune gatanka duniya da lahira.
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 11:11:01 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015