#LABARI MAi #TSUMA JIKI.. Ku daure ku karanta domin fadakarwar - TopicsExpress



          

#LABARI MAi #TSUMA JIKI.. Ku daure ku karanta domin fadakarwar dake cikinsa mamusamman ma ga mata. Akwai wata yarinya sunanta Aysha, tunda ta taso agidansu ake ji da ita duk abunda ta nema ana bata matukar baifi karfin iyayenta ba. A lokacin da ta gama makarantar "Secondary" sai ta fara jin ai ita yanzu wayewa take yi ta kuma fara yiwa samari wani gani-gani. Ana haka mahaifinta ya sama mata "addmission" a poly, ta fara karatu nanfa ta dauki girman kai ta kara sama kanta har takai matakin da tayi diploma, sannan mahaifinta yace aure zai mata kuma yana da wanda yake so ta aura, nanfa ita tace ina tana da wanda take so anyi-anyi da ita tace wai Najib take so. Wanda aka fi saninshi da najiba guy, abokin karatunta shi kuma yaro ne. Da mahaifinta yaga baza ta gane ba sai yayi fushi da ita yace: bashi ba ita kuma tace taji ta gani idan har zata auri Najib, da mahaifinta yaga haka sai yaje wajen mahaifin Najib domin sanin inda magana ta kwana, su kuma iyayen Najib suka ce basusan wannan maganar ba, su dansu karatu zaiyi. Tun daga nan hankalinta ya tashi sannan kuma kowa ya zuba mata ido, yanzu gashi lokaci sai kara kurewa yake yi, shekarunta na karuwa har takai shekaru 30 >35 amma ba wanda yazo yace yana sonta ga kuma nadama da takeyi..... Darasi: Wannan ya nuna cewa idan lokacin abu yayi ayishi kafin lokacinsa ya kure masamman ma idan iyayen mutun ne suka mai zabi nagari.. Allah yasa mudace!
Posted on: Tue, 17 Sep 2013 12:41:25 +0000

Trending Topics



sroom Training Center
Onion Grass in Oblong Ceramic Planter CHECK PRICES >>

Recently Viewed Topics




© 2015