Labarai da dumi-dumi Man city da Arsenal da Man utd sun fara - TopicsExpress



          

Labarai da dumi-dumi Man city da Arsenal da Man utd sun fara zawarcin mai tsaron raga kuma captain na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, bayan situation din da ya tsinci kansa na dumama kujera a club din. To amma har iwar haka goal keeper din dai bai ce komai ba tin daga ranar da madrid din ta sha da kyar daga hannun takwararta Real betis. A hannu guda kuma golan barca wato Valdes ya bayyana takaicinsa na wulakanta Carsillas da wai club din keyi bayan gagaruman nasarorin da golan ya kawo a tsawon lokacin da yake a team din. Ya kuma cewa, golan bai cancanci hakan ba, tinda ba rashin kokari yake ba. A cewar sa babban gola kwararre a duniya kamar cassilas bai cancanci zama a benci ba. Real madrid da Tottenham sun karyata jita jitar wai sun cimma yarjejeniya akan sayan Bale. sun ce har yanzu dai cinikin bai kammalu ba. A gobe alhamis ne Real madrid zata buga wasa mai taken SANTIAGO TROPHY da Al sadd a Santiago inda tsohon captain din Real madrid wato Raul Gonzalez zai zama babban bako a wasan. Raul din dai zai bugawa kowane bangare wasa da madrid din da Al sadd din.
Posted on: Wed, 21 Aug 2013 11:11:28 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015